Ra'ayi.
Mrsjmoon*33*
"Uhmm Yaya kenan kaidai baka tab'a gajiya da neman lada."
"In banda abinki Sweetheart taya za'a gajiya da neman lada."
Yana maganar tare da taimaka mata ta mik'e ya cire mata hijab.
Tsirawa cikinta idanu yayi "Anya cikinnan kuwa ba twins suke ciki ba?"
"Ga dai shinan sai nauyi yake ta k'arawa."
"Sannu Allah ya biyaki da mafificin alkhairi."
"Amin dear."
"Gobe tare zamufita, dan da kaina zanyi miki scanning."
"A'a yaya dan Allah abarshi kawai in na haihu aga ko ma meye ."
"Ohk an barshi tunda ba kyaso.
"Now kwanta in miyi miki awo."
Kwanciya tayi tana cewa "Barci nakeji abari in natashi ayi."
"Angama mmn twins."
Murmushi ta sakar mishi tare da lumshe idanu, kwanciya yayi a bayarta ya rungumeta, yayi k'asa da voice "Barci irin wannan lokacin shine Ma'aiki S.A.W yake kiransa da barcin sunna, wato barci bayan fitowar alfijir, tana d'auke da ni'imomi tare da falala, ki daure kinayinsa Sweetheart bawai daga idar da laziminki ba ki wuce kitchen."
"Tam zan rik'ayi in sha Allah."
"Allahumma ya baki iko."
"Amin."
Daga haka barci mai nauyi ya d'aukesu, wanda basu suka farka ba sai misalin 10am.
A gaggauce suka kammala had'a breakfast sannan sukayo wanka, suka zauna dan gabatar da break.
Rayuwa mai cike da kulawa Zarah tacigaba da gudanarwa tare da heron ta.
Lallab'ata yakeyi kamar egg, duk wani damunta da yawan sex ya daina dan yafahinci tana takura da hakan, sai ya maida hankali wurin azimin nafila dan samun raguwar dire, sosai yasami sauk'i sai yadawo mai hak'uri da juriya wanda wata rana ita da kanta take tsokanoshi suraya sunnar sabida da tausayi dayake bata.
"Autan Ammie kece da kanki bakya ko jin nauyin jikinki."
"Aunty exercise nakeyi kinsan month ya shiga jibi edd na zai cika."
"Oh haka ne fa ,to Allah raba lafiya.
Wuri tasamu ta zauna da k'yar tana cije lips.
" Abdul bani ruwa mai sanyi."
"Tam mommy Zarah." Yaron ya amsa.
Koda yakawo mata ruwan sai tace ya zauna ya matsa mata k'afafu.
Kallon legs nata Zainab tayi tace "Sun kunbura sosai k'anwata."
"Eh wallahi Aunty, kuma bp na normal yake."
"Mata ko wacce da kalan laulayinta, Allah dai ya sauke ki lafiya."
"Amin."
Bayan sallar la'asar ta mik'e dan komawa side nata.
Abu kamar wasa taji ta kasa d'aga k'afafun sai kawai tasaki kuka.
"Subbahanallah!, lafiya kike kuka Zarah?"
Dariya Zainab tasa sanda taji abinda yasanyata kukan.
"Zarah hoo yanzu rik'ewar k'afafu kikewa kuka haka to inaga anzo haaihur, yarinya k'arami ciwo akewa kuka dan ki sani."
Ita dai hawayenta tacigaba dayi tare da komawa ta zauna sai kuma ta mik'e a zabure.
"Lafiyarki kuwa?"
"Ciwo Aunty bayana, cikina, cinyoyin kamar zasu rabi da jikina ga wani ruwa mai d'umi sai zubomin yaketayi washh!! Aunty kitaimake ni!!." Ta furta cikin k'araji.
"Zo muje in dubaki."
Tallabeta tayi zuwa wani madai-daicin room.
Tashin farko tagano labour ce yazo mata mai zafi da hanzari ta had'a allura tana shirin yi mata taga kan d'a na turowa tayi jifa da sirinjin ta taimaka mata babyn ya k'arasa fitowa.
Tana yanke masa cibi ta hango kan wani ya turo, shima cikin gaggawa ta tareshi, sai lokacin muryan Zarah ya fito "Alhamdulillah!!." Ta furta da k'arfi.
"Sannu adon mata, lallai kinyi jarumta, Allah ubangiji ya raya miki su cikin sunnah."
A hankali ta amsa "Amin."
Cikin 30 minutes Zainab tagama gyaresu tsaf ita da babies sai lokaci tasoma sanarwa da al'umma, aikam nan da nan side nata yacika da mutane, sai albarka suke ta saka mata ita da maijegon.
Angon k'arni kuwa yanacan office aiki ya kacame masa amma duk hankalin na wurin sweetheart nasa, haka nan ya rufe office d'in ya nufo gida batare da ya kammala aikin ba, addu'a yake tayi Allah yasa dai lafiya take ganin yayi ta kiran wayarta yafi a irga bata d'auka ba.
Yana sawo kai cikin estate d'in gate men suka soma yi masa barka amsawa kawai yakeyi batare da ya fahimci inda lamarin ya dosa ba.
Da Modibbo yaci karo sadda ya fito cikin motan.
" Ahmadu ashe kana tafe." Yace dashi cike da walwala.
Ya russuna "Eh Modibbo, anyini lafiya?
"Lafiya lau, ya wurin aikin naka?"
"Alhamdulillah."
"Masha Allah, sai ka k'arasa shashin Zainabu kaga kyautar da Allah yayi maku."
Jim yayi "Ah dama Aunty Zainab nada ciki ne?"
Murmushi Modibbo yayi "A'a Uwata ce ta sauka bada jimawa ba, ta sami kyautar 'yan biyu duka maza."
Baki bud'e yake kallon dattijon sai kuma ya kwasa da gudu ya nufa side d'in Zainab.
Jijjiga kai Modibbo yayi fuskansa d'auke da murmushi ya dogara sandarsa zuwa parlonsa yana mai furta "Ahmadu hoo har yanzu dai yana nan da gudun nan nasa kamar d'iyan barewa."
VOUS LISEZ
RA'AYI
Roman d'amour"Mitchew!!" taja tsaki "Meke damuna ne ni ZARAH?' Ya Allah ka kawomin dauki alfarmar Annabin farko da k'arshe Amin.