*RA'AYI*
'''Na Safiyya'''*02*
Ajiyar zuciya take ta saukewa tare da shashsheka mai nuni da taci kuka ko tana kanyin kukan.
"Ya Salam! Wai Zarah meke faruwa ne kike ta wannan irin kukan tun daren jiya gashi yanzuma kin kuma wayar gari dashi?"
Sake ballewa da kukan tayi, ta k'amk'ame Zainab, wannan karan kukan sosai ya tab'a zuciyar Zainab, dan haka itama kukan tasaki mara sauti, cikin kukan take cewa "Kaicona ni Zainab, na kasa rik'e amanar da Ammi tabarmin, nabari Autanta tana kukan maraici, yau ina zansa kaina?, nabar marainiyar Allah tana ta zubda jurwaye na kasa tsaida mata dasu?, wayyo Ammi ki gafarceni wallahi bansan zuwanta ba shi yasa, ya Allah kakawoma 'yar uwata mafita ba dan halina ba".
"Aunty dan Allah ki daina kukan nan haka, kinga nima na daina, yanzu komi yawuce, haka dama rayuwa take kuma na d'auketa ayarda ta zomin amma dai bazan yafewa duk wanda yake zargina ba, ko kuwa waye shi".
"Zarah sanar dani damuwanki in ba so kike naga kamar amanar da Ammi tabani naki nakasa rik'esa yarda yakama ta bane".
"Aunty ni da yaya hero ne, kuma ya wuce".
"Uhmm ina jinki meya hadaku?"
Zero legs dinta tayi kasa tare da mik'ewa ta nufi hanyar toilet, sai da ta kama handle din shiga toilet din sannan ta juyo "Aunty please don't bother yourself, i said am ok".
Gyad'a mata kai tayi tare da komawa ta zauna da zuba tagumi tana k'ok'arin lalibo abinda ya hada k'anwarta da Ahmad.
Ko da tafito daga toilet shirinta tasomayi cikin sanyin jiki, tashirya tsaf cikin riga da wanda na English wear ta d'ora k'aramin hijab, tayi kyau duk da bata cikin walwala, tazo ta sunkuya gaban Zainab tare da dafa gwaiwoyin ta "Aunty nace komi ya wuce fa, bakomi yayi min ba illah fad'a da yayi mana duk kanmu amma dai tawa yafi yawa ne da k'ona rai, shine abinda yasakani kuka, sannan na yarda na aminta cewa sai wanda ya damu da kai shine zai yima fad'a na kabar abinda bai dace ba da ka dawo d'abi'a na gari, to nagode masa kuma in Allah yaso zan gyara".
" Meye kike aika tawa haka batare da nasani ba Zarah?"
"Forget about it pls Aunty, bawani abin aibu ba ne".
" Tam naji amma ba dan na gamsu da bayanan kiba, dan haka zan bincika naji ko meye".
"Uhmm Aunty ki bari kawai zan sanar dake komi da kaina".
"Tam, Allah yayi miki albarka, ya kuma tsaremin ke tare da 'yan uwanki".
Rungumeta tayi tana murmushin yak'e, "Amin my second
Ammi"."Bari naje na gaidasu Hajja da Tsoho mai ran k'arfe".
Tafice da hanzari, da kallo Zainab tabita dashi tana mamakin wai yau Zarah ce ta ke boye mata damuwarta abinda bata taba hashashensa ba.
Hey Guy's ina buk'atan shawaranku akan yarinyar nan da ta wulak'antani abainar jama'a amma in har mutum yasan bazai fad'i abin arzkiba to kada ya sake naji sautin muryansa, dafatan anji ni da kyau?"
"Yeah Oga".
suka amsa masa." Oga ka aikamu kawai mu d'auko maka ita zuwa gidan nan daganan sai kayi mata kaca - kaca inyaso kayi kalacin safe har da marece da ita, kaga daganan zata gane ban bancinku da ita mai tazara ne".
"Eh wannan hakan shine hak'ik'anin shawaranmu akai Oga!!". Suka fad'a cikin ihu.
" Ban dani ciki, dan ni kam bazan taba jagorancin cin zalin ba akan abinda da shine yasoma janta da fad'a, kuma kota ina in an duba babu adalci acikin lamarin da kuke son ya aikata".

VOUS LISEZ
RA'AYI
Roman d'amour"Mitchew!!" taja tsaki "Meke damuna ne ni ZARAH?' Ya Allah ka kawomin dauki alfarmar Annabin farko da k'arshe Amin.