08

970 78 0
                                    

*RA'AYI.*

*08*
Motar Zainul suka nufa wacce take ajiye gefen a k'asar bishiyar dalbejiya dake kusa da gate.

Bud'e mata gefen kusa da driver yayi ta zauna shi kuma ya zagaya driver seat ya zauna.

Hira mai cike na nishad'i sukeyi, zuwa can Zainul yayi shiru alamar ya fad'a kogin tunani, had'a yatsunta 2 tayi ta murzasu daf da face d'insa suka bada sauki mai k'ara, ajiyar zuciya yaja mai k'arfi tare da dubanta ya saki murmushin yak'e, bata rai tayi "me ke damunka friend?" Tace dashi.

Kallonta ya yi cikin kalan tausayi yayi k'asa da voice ya amsa "I'm thinking about my Mum".

"Bata da lafiya ne?"

"No, lafiyarta lau, ina dai jin kewarta ne, she's in Spain together with my sister".

"Ayya sorry, tafiya sukayi halan?"

"Eh, a'a".

"Tofa, like how?, ban fahimce ka  ba".

Jim ya yi kamar bazaice komi ba.

"No kabarshi in da damuwa". Tace.

"Kinfi k'arfin komai a wurina Zarah, kawai dai na rasa yarda zan sanar dake cewa Mum d'ina bata tare da Dad d'ina ne, sun rabu da juna, shine ta wuce k'asarsu tare da sister dina, ta barni tare da Dad, so kewarsu ya dameni shi yasa na fad'a tunaninsu".

"Ya Salam, sorry rabuwar iyaye ba dad'i, dole kam kayi tunaninsu, Allah ya dai dai tasu cikin sauki".

"Uhm to Amin dai amma dai it's hardly dai dai tuwan nan tasu".

"Kada kayanke k'auna da hakan, dan shi lamarin ubangiji a hijabi yake, bawanda yasan yaya yake sai shi kad'ai, in yanufa sai kaga komi ya dawo normal kamar wani abu baitab'a faruwa ba".

"Tam shikenan Allah ya tabbatar mana da Alkhairinsa".

"Amin".

Cikin tsokana tace "Gaskiya gana kayi kama da turawa ashe Mum d'inmu baturiya ce".

Dariya yasa mai sauti, "Kinjiki da wani zance, to Dad yafi Mum haske da kyau dan shi ma bafutanin gombe ne aiki ya kawoshi garin Abuja".

"Oh ashe duk 1 muke,  koda yake ma ai duk mazauna garin Abuja kazo na zo ne".

"Haka zancenki yake Mai kyau".

Hararansa tayi "Banson tsokana fa tam".

"Wallahi ba zancen tsokana Zarah, ke mai kyau ce mai kuma matuk'ar d'aukan hankali ga kwarjini mai sa aji shakkarki ko da ba'a shirya ba".

Dariya ta soma ganin yarda yake maganar yana kwatantawa da hands d'insa.

" Wallahi kome zakace akaina nasan ban kaika kyau ba, kaifa half cast ne".

"Uhmm Baby kinko san yanda kike?"

"Zarah!! Uban me kikeyi a wurin nan? Oya come out ki shige ciki kafin inci miki k'aniya".

Abbanta kenan yake magana cikin fushi.

Jikinta na rawa tafito ta shige ciki da hanzari, tana wai wayen Zainul.

Jingina yayi a seat d'in ya d'aga kansa sama wani abu na mintsilinshi a zuci.

"Kafita hanyar 'yata yaro ko insa a d'aureka har igiya tayi ra ra".  Maganar Abba ya dawo dashi cikin natsuwarsa.

Cike da ladabi ya fito ya durk'usa "Abba kayi hak'uri dan Allah".

Mitchew!!! Abban yaja tsaki tare da barin wurin afusa ce bayan ya watsa masa kallon kanka akeji.

RA'AYIOù les histoires vivent. Découvrez maintenant