page 25

604 40 2
                                        

*25*

Wanka ya gabatar ko lotion bai samu shafawa ba ya sanya vest da boxer ya fito parlor yayi powering disc d'in k'ira'ar AL-QUR'ANI cikin suratul ANKABUT.

Lumshe idanunsa yayi yasoma bin karatun, sannu bisa hankali nauyin da zuciyar tayi masa yasoma raguwa, ni'ima yana ta wadatuwa agaresa, ahaka wani barci mai dad'i ya sureshi batare da ya shirya ba.

Arazane ya farka lokacin duhu ya kawo jiki dan anata kiraye - kirayen sallar magrib a masjid wasuma har sun tada sallah.

A gaggauce ya d'auro alwala tare da zira jallabiya ya fice da hanzari dan kwad'ayin samun jam'i.

Zarah ciwon ciki ya dawo ya hanata sukuni tun misalin 4:30pm take fama dashi har zuwa magrib sai kuka takewa Zainab, bayan Zainab ta idar da sallah ta d'auko allura tayi mata wanda saida takusa marinta sannan ta bari akayi mata.

Tana kwance a parlor tasoma jin sauk'i amma hayaniyar su Najiba duk ya isheta.

Mamun ne ya dawo daga masallaci, tayi  masa sannu da zuwa cikin dauriya.

Amsawa yayi cike da zolaya yace "A'a A don mata ce anan kwance ga mijinta can yana ta bilayin nemanki"

Kauda fuskanta tayi cikin jin kunya sai kuma ta mik'ewa hankali zata fice.

"Dawo ki jirasa yazo yatafi dake, kinsan ba lafiya ce ta wadaceki ba, wasa nake miki yana nan shigowa ya tafi da kayarsa."

Kunya maganar ta bata dan haka ta cusa kanta tsakanin cinyiyinta.

Dariya suka saka mata har da yaran wanda basu fahimci komi akai ba.

Tana ganin sun shige bedroom tamik'e cikin cije lips tayi tafiyarta zuwa side d'inta.

Tana zama samar Cushing yana shigowa, da sarsarfa ya iso inda take ya kamo fuskanta ya had'a da nashi, hancinsa yasoma koga mata ta lumshe idanu.

"Wash Allah Sweetheart affuwan bancika alk'awari ba, wallahi wani uziri ne yashamin kai."

"Bakomi yaya komi kagani sai Allah yanufa ai."

"Thank you my heartbeat, da kika fahinceni"

Murmushi ta sakar mishi.

"Aunty Zainab ta sanar dani bakya da lafiya ciwon cikin ya dawo sosai har saida tayi miki allura."

"Eh." Ta amsa tana mai zamewa ta kwanta daga rik'on da yayi mata.

"Kinsha zak'i ne ko?"

"Na manta ko nasha ko ban shaba I can't recall."

Cheek nata ya d'an mara kad'an "Kinsha kenan dai.

"Uhmm nifa barci nakeji, gashi da alama surutunka bazai barni nayi ba."

Mik'ewa yayi yaje ya kulle parlor ya dawo ya d'auketa cak zuwa bedroom.

Bai direta ko inaba sai cikin bathroom, ruwa mai zafi ya had'a mata ya umurceta da tayi wanka,  ya fice bayan ya kulle mata k'ofar.

D'akinsa ya nufa, kayan barci ya sanya ya dawo lokacin daidai tafito shi ya taimaka mata ta shriya ya kuma suranta zuwa room nasa.

"Yaya Hero meke damunka naganka wani iri?"
Maganarta ya katse masa tunanin da yakeyi.

"Dama ba ki barci ba ?"

"Eh."
"Ohk to maza kiyi barci dan nima shi zanyi yanzu."

Tana shirin sake magana ya d'ora bakinsa anata ya hanata magana.

***** Rahila kuwa bata dawo hayyacinta ba sai cikin dare tana fahimtan a inda take ta fasa ihu cike da takaicin wulak'ancin da Ahmad ya shuka mata.

"Inban koya ma doctor hankali ba, ba sunana Rahila ba lallai." Ta furta cikin kuka.

K'ofar tasoma jijjigawa amma ba alamun zai bud'e, komawa tayi ta cure jikinta tana rawar sanyi, ranar Ahmad kam yasha tsinuwarta ba adadi.

Washe gari sai misalin 11:00am yasami fitowa dan saida ya tabbar da Zarah ta warware har tasoma gabatar da ayyukanta sannan ya shirya yafito.

Koda ya iso office aikinsa yasomayi danshi ya manta da yayi ajiya a toilet nasa.

Sai da lokacin sallar azuhur yayi ya dakata da komi ya nufi toilet dan d'auro alwalan sa.

Bak'aramin razana yayi ba sanda yaganta kwance dafe da ciki sai juyi takeyi.

Wani uban tsaki yaja ya daka mata tsawa "Zo ki ficemin kafin in karkaryaki."

Jiri na d'ibanta ta mik'e ta zo ta rab'a gefensa tafice.

Fasa shiga toilet d'in yayi ya biyo bayarta "Ke."

Ja tayi ta tsaya, kusa da ita ya matsa ya sakar mata mari mai kyau, ta tafi luuuu, bai tareta ba har ta kai k'asa ta kuma bige hannun dataji targad'e jiya ta ko kwalla ihu.

"Yimin shiru ko inbaki mamaki yanzu."

Rahila dan Allah ki fita rayuwa ta Inbaso kike na illataki ba." Ya furta a hankali.

Shiru tayi tana kallonsa wanda hakan ya hassala shi.

"Kinjini ko bakiji ba!!?" Ya fad'a ciki tsawa.

"Naji." Ta amsa tana mai jifarshi da mugun kallo.

"Good, you can go." Ya nuna mata hanyar fita idanunsa kulle dan baison ganinta gabansa.

Ficewa tayi cike da alk'awarin d'aukan fansa akanshi ko akan 'yar gold d'in matarsa.

RA'AYIOnde histórias criam vida. Descubra agora