*RA'AYI*
'''Na Safiyya''
*07*Sunyi jugun-jugun suna kallon yarda numfashinta ke sauka. Sallamar Ummie shi ya katse zaman shurun nasu, amsa mata sukayi atare, direct bed d'in da Zarahn take kwance ta nufa, ta mik'a hannu ta dafa goshinta sannan ta juyo tace "Ahmad d'in kuwa yazo ya yi mata alluran?"
"A'a baizo ba' amma dai Aunty Zainab tayi mata shinema har ta sami barci".
Zeenat ce ta amsa mata.
" OK hakanma ya yi Allah yabata lafiya".
"Amin" suka amsa atare.
Bayan fitarta Ahmad ya shigo, ya d'an duddubata ya juyo yana auna masu kallon banza, saki yaja fuska ahad'e yake cewa "Kun san Allah inbaku rage shan zak'i ba bawanda zai kuma bata lokacinsa akanku, in banda iskanci kuna sane period d'inku ya kusa, maimakon ku guji cin zak'i ko shansa dan samin sauk'i, a'a ku time d'in kuke shige masa, duk kuzo ku ishi mutane da kwakwazon banza, to kuyi tayi kada kufasa kunji, musanman ke ya nuna Zeenat da aminiyartaki uwar 'yan raki" yana mai hararan inda Zarah take kwance.
Haka ya k'araci fad'ansa ya fice, bawanda tayi motsin kirki.
Baya sallar isha'i dukkansu suna zaune har da Zarah a cikin parlon Hajja, supper suke ci amma ita Zarah kwance take dan har lokacin tanajin ciwon maran, kad'an _ kad'an bai gama sakinta ba.
Hayaniyarsu duk ya isheta, ta mik'e a hankali ta fice, side d'in Zainab ta nufa tana daf da shiga ta tsinkayi maganar sa
"Gyara tafiyarnan ko in sab'amiki, in banda iskanci kina wani tafiya kamar agwagwa ko ince d'an kaciya".
Ja tayi ta tsaya tana cije lip, tana kuma auna masa harara a fakai ce.
Jan hannunta yayi da k'arfi, ta saki siririyar k'ara bai kulata ba, side d'in umma Amarya ya nufa sai da ya sadata da room d'inta sannan ya saketa ya ja da baya ya hard'e hannayensa a k'irji he gazing at her.
Bazata jure wannan kallon nasa ba dan haka sai ta sauke kanta k'asa tana jan hanci alamar harda mura ke damunta.
"A don 'yan mata".
Da hanzari ta dubeshi, jin sunar da yakirata da shi, bazata iya tuna sanda ya kirata da hakan ba na k'arshe.
"Yeah my Star, kina mamaki ne?" Yace hakan tare da d'aga mata gira.
Zamewa tayi ta kwanta, ahanakali ta furta "Mukwana lafiya, barci zanyi". Dan bak'aramin haushi d'aga giran nasa yabata ba, wai shi nan adole sai na so shi kenan.
Zama ya yi gefenta ya kamo hannunta ya rik'e gam, abinda ya dawo da ita duniyar tunanin da ta fad'a na wucin gadi.
Kiran sunarta ya yi cikin laushi, tana jinsa amma tak'i amsawa haka tak'i bud'e idanunta dake kulle.
Kallonta yakeyi murmushi d'auke a kyakykyawan fuskanshi, magana yake mata k'asa - k'asa tare da murza mata fingers, cikin kasalalliyar murya tace "Wannan ba tarbiyyan gidanmu bane kuma ba d'abi'ar kirki bace, in kuma kaga hakan dai dai ne da kai sai kacigaba amma ka sani zunubin akanka zai k'are."
Sakinta yayi ya fice batare da kuma cewa da ita komi ba.
Tsaki taja mai sauti "Iskancin banza yagama cemin agwagwa kuma ya wani zo yana mak'emin voice, wai my star a'a moon ne ba star ba". Ta k'arasa zancen cike da tsiwa.
_3 days later_
Da gudu ta shigo garden tana k'yalk'yala dariya, ta sami gefen swim-pool ta zauna tana cigaba da dariyanta ba jimawa Zubaida ta shigo ita kuma sai haki takeyi ta zauna gefen Zarah sai aikin maida numfashi takeyi.
"Wallahi sis Zarah ke d'in ba k'aramar muguwa ba ce, dan mugunta kije ki tsokano dog d'in yaya Imam, kibar mutane da bala'i, ko kinsan duk ya ya k'ushe Aunty Suby".
"Wayyo Allah nagode maka, duk da ban zaci ita zai bi ba wallahi ca nike 'yar buhuncan zai bi, ya salam! Muje inga yarda ya yi mata, Allah yasa bai cije mata wannan mazaunar ba masu kama da an tab'e daddawa".
Dariya Zeenat tasa har da kwallah.
"Muguwa to ba inda zani, kuma ko me yayi mata Ai ke kikaja, wallahi rabona da inyi gudu irin haka tun ina secondary, sanda mahaukacin nan ya biyomu wanda Zulfa'a ta gefe da dutse, sai kuma yau da kika tsokano mana kare da nonuwanmu da komi amma kika samu gudun fanfalak'i, kai wallahi sis wata rana kina da sa damuwa kam".
Dariya Zarah ta kuma sawa tana fad'in, "Bartunomin da abin takaici, kokinsan lokacin sai da nayi fitsari wurin gudu ban sani ba?"
Dariya mai had'e da ihu Zeenat ta kwashe dashi, har abin yaso bawa Zarah haushi ganin yarda take dariyan har da rik'e ciki.
"Ina 'yan banzan yaran suke?"
"Suna ciki yaya".
Kallon kallo suka somayi, dariyan ta d'auke sai zare eyes sukeyi, jin muryan Imam da sukayi yana tambayar inda suke Zulfa'a na amsa mishi.
A guje suka kwasa sukayi ciki suka fice ta d'ayar k'ofar da zai sadasu da side d'in Hajja.
"Lafiyanku kuwa?, rid'i_rid'in 'yan mata da ku amma kuna irin wannan gudun kamar 'yan matan k'auye".
"Hajja Azara'ilu ne zai dokemu".(Imam suke kira da haka dan sanin bak'in halinsa da iya muguntarsa tun suna yara)
"Laifi kukayi masa, dan nasan takwaran Malam bazai dake ku haka kawai ba sai da dalili".
"Munshiga uku!!, ni Zeenat".
"Wallahi sam na manta Hajja bata ganin laifin mai sunar Mijinta, ba muyo nan ba".
"Sis komi akayi mana ke kika janyo inda baki shiga kin had'a matarsa da kare ba da duk haka bata faruba".
"Innalillahi Hajjaju!!!, kina cikin nutsuwarki kuwa?"
Cikin d'aurewa ta amsa "Ras nake, ramawa nayi dan kwanaki ita da Zulfa sun min irin haka na k'yar nasha, sukayi tamin dariya".
"Asha! Aikam basu kyautaba, kuyi zamanku zaizo ya sameni inji inda zaiyi hukunci cikin rashin bincike".
Had'a idanu sukayi suka murmusa tare da samun wuri suka zauna tasoma basu tarihin Sahabbai da manyan malamai magada Annabawa.
Sun nutsu sosai suna sauraronta barinma Zarah wacce dama abinda ta karanta kenan a jami'a.
Wasan b'uya suka somayi da Imam hatta zuwa gaidashi da sukeyi da safe Zarah da Zeenat sun yanke sai dai Zubaida da Zulfa'a suke zuwa.
A wani yammaci Zarah tana zaune da Zainul suna hiransu kamar yarda suka saba duk in yazo gaida Modibbo zai nemeta susha hira kafin ya wuce.
Sun shagala sai labari yake bata na wani k'auye da al'adarsu, abin sosai yake bata dariya.
"Ke!!!!"
Arud'e suka dubi inda Kalmar ta fito, Imam ne tsaye fuskan nan kamar anyi gobara.
"Biyoni part d'ina ki gayamin dalilinki na had'amin mata da dog".
Har ya kusa shiga side d'in nasa ya juyo, sama ko k'asa yaneme su ita da Zainul yarasa, babusu babu sanmatarsu a wurin, k'wata yayi ya furta "Sai na karya yarinyancan zanji dad'i dan nagama fahimtar irin tsanar da tayi min a gidan nan, gashima har ta dawo kan matata da iskancin to zan ko sai ta mata tunaninta bada jimawa ba".
Zarah kuwa yana juyawa ta matsa tayiwa Zainul rad'a suka fice gate da sauri.
~Mrs j moon~

YOU ARE READING
RA'AYI
Romance"Mitchew!!" taja tsaki "Meke damuna ne ni ZARAH?' Ya Allah ka kawomin dauki alfarmar Annabin farko da k'arshe Amin.