03

1.3K 106 1
                                    

*RA'AYI*
'''Na Safiyya'''

*03*

"Kai meye haka kuke yiwa mutane ihu ko sakarcin naku na fama ne ya motsa?"

Duk kansu a k'asa sun kasa motsin kirki dan sun kwana da sanin halin Abba Umar sarai, bak'aramin aikin sa bane yanzu ya zanesu sabida shi bai d'auka raini sam alamuransa, shi yasa Zarah ta d'ebo d'abi'unsa kad'an na yanzu - yanzu zata gyarawa mutum zama in har yanemi ya raina mata hankali.

"Abba kayi hak'uri wani film d'in horror muke kallo sai tsoro ya kamani na saka ihu".

" Shashancin banza, to maza a kashe kallon, mashiritan banza, kusani in anga abin tsoro addu'a akeyi ba ihu ba, amma ke dan sokanci kin wage baki kina ihu, Allah ya yaye miki wannan Hali".

Ahankali ta kuma cewa "I am sorry Abba I confessed my mistake, i'll not repeat it again".

"Allah yasa to, amma hak'ik'a Zarah kina da sakaci wurin addu'a dan haka zansa Ahmad ko Mahmud wani ya rik'a zama daku yana tunatar daku addu'o,in kariya daga afkawa sharrin shaidanun mutane da aljannu da kuma k'ara sanin dokokin addini, dan naga kamar k'arancinsa atare daku".

"Mungode Abba, Allah k'ara girma".
Zarah ce mai k'arfin halin amsa masa.

"Amin, Bakomi hakkinmu ne kula da ku kafin ku koma k'ark'ashin kulawan mazajenku".

Sunkuyar da kanta Zarah ta kumayi k'asa sosai tana smiling, shima murmushin yayi dan yarda tayi sai ta tuno masa da mahaifiyarta, hakan ta kanyi in taji zance yayi mata nauyi. She was a shy woman, har yanzu bai daina kewarta ba, shi yasa duk zafinsa indai akan Zarah ne yakan koma cool dan mafiyawan d'abi'unta duk na mahaifiyarta ce musanman wurin saurin amsa kuskure, natsuwarta, tausayinta, muryanta, tafiyarta da dai sauran various things, sai dai in ta murd'e da wrestling ita da Zulfa'a sai ta dawo Abbanta ziryan.

Yana fita Zulfa'a ta sauke ajiyar zuciya mai k'arfi, ta d'ago kanta tana share sweat, wani kallon banza Zarah ta sauke mata tare da yin k'wata "Lallai kin cika babbar horrible Zulfa, ashe dama kece kike lalibe mana boobs cikin dare, muyi ta blieving dream ne?, kai Allah yayi wadaran halinki kam, Allah kuma sai ya saka mana, foolish kawai, sai yanzu nagano gaskiyar maganar Zaheeda da takan ce miki mayyan mata, ashe tasan iskancinki ne ciki da bai, oh Ya Allahu!!, Allah ya shiryaki dai".

" Amin tare da ke".

"Uhmm Zulfa lallai baki gama sanin ko wace ce Zarah ba da kikazo mata da wannan salon tantirancin naki amma don't worry u will know who I am soon".

" Ke!! Zarah kadafa ki raina min hankali, sanin wacece ke ai tuni nagama sani, 'yar club, mai bin maza wata k'ilma har da matan kina latsawa, yo meye a ciki dan na gwadaki nagani, shine zaki nemi lak'amin sharri, to wallahi baki isaba ehe".

"Zulfa!! Nice kebin maza da lesbian?"

"Ya wuce wai, kodan kinga nayi miki shiru kina cimin mutunci? To jira nake ki dasa aya nakoro miki bayanai, dan haka kisani ni ba irinki bace mai 2 face, a tsarkake nake tsaf bana tare da k'azantan komi".

Punch Zarah ta kai mata with sudden ko kafin ta farga tuni ta rufeta da duka da naushi legs and hands, kuma ta hanata ihu dan data bud'e baki zata sakar mata sadakar punch, sai da ta lallasata  san ranta sannan ta d'agata ta barta kwance, toilet ta fad'a ta sakarwa kanta shower.

Idanunta lumshe ruwan sanyin yake ta zubo mata  hawaye kuwa kamar bakin tap haka yake biyo kumatunta , her heart was heavy, hands d'inta dafe da chest d'inta dan jinsa take kamar and'ora mata k'aton dutse.

A k'alla ta d'auki 15 to 20 minutes ruwan yana zobo mata, zuwa lokacin ta sami peace of mine da tai makon istigfari da tayi taja cikin ranta, tayi off shower ta d'auro babban towel tafito.

RA'AYIWhere stories live. Discover now