19

964 67 2
                                    

*RA'AYI*
'''Na Safiyya.'''

*19*

Magana takeyi awaya a hankali tana ta doka murmushi, Aunty Zainab dake kallonta tun soma wayar nata sai uban harara take aikin watsa mata, kanne mata 1 eye Zarah tayi tako zabura ta falla mata duka a lap, siririyar k'ara ta saki tare da mik'ewa da sauri tabar wurin zuwa dinning area tana maicigaba da maganarta.

Ak'allah saida ta b'ata kusan 40 minutes sannan ta gama wayar sauke wayar tayi tare da kallo inda Aunty Zainab take zaune taga batanan, tab'e baki tayi ta janyo wani little cup dake samar dining ta had'a tea tasoma sha asannu tana mai sakin murmushi lokaci zuwa lokaci kuma sai cije lips tare da girgiza kai.

"Ke da wani wofin kika gama waya?" Aunty Zainab ta furta hakan tare da jan chair ta zauna tana mai fuskantan ta.

K'in tankawa tayi, tacigaba da kurb'an tea kamar ba ita ake tambaya ba.

"Zarah kin san Allah zan mugun sab'a miki inhar inayi miki magana kina bawa banza ajiyata." Ta furta hakan cikin fushi.

"Affuwan second Ammie bazan kumaba da yardan Allahu, fushinki kukan yaro." Tace hakan tana mai yimata jinjinar bangirma da hannu.

Harara ta wulla mata sannan ta kuma maimaita tambayar da tayi mata.

"Aunty Mu'azzam ne, guy d'innan dake zuwa gaisheku ke da Hajja sanda mukaje umrah."

"Uhmm naganeshi amma inason sanin alak'ar dake tsakaninku."

"Oh Aunty inaga daga nurse kinkoma journalist ce ko lawyer, haba wannan sonjin k'wan har ina sai kace nid'in wata baby wacce batasan fari da bak'i ba."

"K'aniyarki zanci wallahi yanzu in har baki bani gamsashshiyar bayani ba akan banzan nan mai kama da 'yan daudu ba."

Dariya tasaka "Kai Aunty ji wani sharri da rana tsaka wai d'an daudu, mutum mai nagarta irin haka ai yafi gaban amisaltashi da daudanci."

"Ina saurarenki ko sai naci miki mutuncinki?"

Ganin tabbas tana da shirin cin k'aniyar nata yasa ta mik'e da hanzari zata gudu, caraf ta dank'e hannunta ta zaunar.

"K'anwata dan Allah kidaina irin haka, ki kwantar da hankalinki wuri 1 ki amshi jininki Ahmad amatsayin miji kamar yarda sisters d'inki sukayi, dan Allah ki rufamana asiri ki so zab'in iyayenki kuma son danginki, dan Allah kada ki sake bari zuciyarki ta kuma jajibo miki wani lamarin wanda zai iya zamowa barazana agareki dama mu  masoyarki, kinji k'anwata abin alfaharina." Cikin sanyi take maganar kuma cikin sigar rarrashi.

Dariya Zarah ta kwashe da shi harda rik'e ciki, tsuru Aunty Zainab tayi mata tana kallon ikon Allah.

Saida ta gaji dankanta sannan ta gintse dariyar ta matso kusa da ita sosai ta kwantar da kanta samar table face nata na kallon face d'in Zainab, tasoma magana cikin natsuwa.

"Wallahi Aunty tunda nake bantab'a jin son Mu'azzam ba, inadai girmamashi ne dan wanda yake yana sonka yafi gaban wulak'ancin kuma ko d'azun da kikaji muna waya cemin yake na nema mishi mata amma intabbatar mai kama da nice akomi da komai dan tun had'uwarmu afarko nasanar dashi bikina ya kusa, yayimin fatan alkhairi."

"Oh yanzu naji batu k'anwata."

Murmushi tayi tare da tashi ta zauna sosai "Aunty in har nayiwa yaya Hero haka lallai nazamo butulu, tsirarafa ya ganni da waninsa amma yace yaji yagani hakanan yana sona, natabbatar ko Zainul da muka so zuwa kamar me bazai iya wannan jarumtar ba, shi yasa sanda naganni gaban d'akin Allah  addu'ata tafi yawa a kansa na Allah yayi ta ruwan albarkatu agareshi, yabar so da k'aunarmu cikin aminci."

"Amin Auta, lallai nayarda Zarah ta sanja tayi hannun riga da RA'AYIN nan nata nason kawo sauyin RA'AYI a Modibbo's family, Alhamdulillah, Allah yayi miki albarka."

RA'AYIWhere stories live. Discover now