*RA'AYI*
'''Na Safiyya'''
*18*Sai da Jimie yayi 2 weeks sannan akayi discharge nasa, amma idanunsa 1 ya tsiyaye.
Daga hospital direct kotu aka wuce dashi d'aure cikin sark'a.
Sanda yayi arba da yaransa su mika bak'aramin rud'ewa yayi ba dan gabaki d'aya kamanninsu duk ya sanja, sun rame ga uban bak'i da sukayi da tarin k'asumba babu kyan gani, Monkey hannunsa nad'e da bandage saka makon harbin da Jimie yayi masa, sai ruwa yakeyi sabida da rashin kula da bai samuba.
Ba bata lokaci alk'ali ya yanke ma yaransa zaman prison na 25yrs ba beli, saka makon kamasu da akayi da laifin sace Zarah, k'wace, fashi da makami tare da safarar miyagun k'wayoyi.
Shi kuma Jimie d'aurin rai da rai aka yanke masa, ba fita har mutuwarsa tare da horo mai tsanani, sabida shine shugabansu kuma an sameshi da kisan rayukan mutane bila'adadin, fyad'e da dai sauran mugan laifuka da ya cancan ci hukunci mai tsauri.
Kuka yake kamar ransa , Musbah ya iso wurin cikin zubar kwallah ya dafa kafad'ansa.
"Jamil kaga irin ranar danake guje maka tazo, itace ranar danasha sanar dakai zuwanta amma ka maidani mahaukaci, yanzu meye amfanin zuwarka duniya? Kazo a guje zaka koma a guje, wannan shine ake cewa zuwar zomo, Allah kayi mana tsari da irinta.""Amin yaro." Dad d'in Zainul ya amsa daga bayansa.
"Hakik'a naji dad'in hukuncin da akayi masu, dama ina naimansu dan insa ahukuntaminsu sai gashi ankamasu kuma anyi masu hukunci daidai da laifikansu, kai masha Allah."
Yana gama fad'an haka ya wuce yabar Musbah da baki bud'e.
Ahmad ne ya iso yaja hannun Musbah amma sai Jimie yarik'eshi kam yasoma magana.
"Musbah nayi nadama lokacin da bashi da amfani, kaicho na da rayuwata, dan Allah idan kaje gida kace ina naiman gafaran su Inna da Baba, su yafemin ko nasami rahamar ubangiji."
"Inna tajima da rasuwa Baba kuma ya makance ya kurumce baiji bai gani, nasameshi kamar mahaukaci nasami wani bawan Allah yasoma kula dashi ina biyansa kaga kenan bayarda za'ayi sak'onka ya isa mishi amma ina baka shawara da ka komawa Allah, kasoma ibada mai kyau kayita tuba akan zunuban da ka'aikata, Allah gafurun rahimin ne, Allah yayafe mana baki d'aya."
"Amin." Ahmad ya amsa.
Yana ganin Jimie zai soma mishi magana yatareshi cikin sauri.
"Na yafe maka, tafi kayi ta naiman tuba wurin mai duka, haka itama My Star zan neman maka yafiyanta, nasan bazatak'i ba.""Na..go...d..e" Ya furta cikin in'ina cikin zubar hawaye.
Ahaka ma'aikatan gidan yari suka tisa k'yeyarshi zuwa cikin motarsu inda yaransa suke, yana ta waiwayen su Musbah cike da tarin nadama.
Ahmad yayiwa Musbah jagora zuwa wurin Modibba ya gabatar da shi tare da sanar dasu Abba irin taimakon da yayi akan b'acewar Zarah.
An karramashi ainun, Modibbo yayi masa addu'a, su Abba sukayi ta yimasa godiya har saida yaji kunya yarda manya suke tayi masa godiya.
Abban Zarah yayi masa kyautan bangirma haka Ahmad ya bashi irin tasa kyautar, yayi ta godiya tare da yaba kirkin da karamcin Modibba's family.
*****
Angwaye da Amare sunyi kwanar farin ciki mai cike da begen juna mara iyaka, sai albarka mazajen keta sanyawa matayen nasu, sunyi masu kyauta dan jin dad'in kawo masu martabarsu da sukayi gidajensu, sai riritasu suke tayi kamar kwai.Amma a side d'in Zulfa'a abin yasha bambam dan bata sami riritawan nan ba, yadai bata kyautar kamar yarda brothers nasa suka bama sisters nata dan tare suka saya masu.
YOU ARE READING
RA'AYI
Romance"Mitchew!!" taja tsaki "Meke damuna ne ni ZARAH?' Ya Allah ka kawomin dauki alfarmar Annabin farko da k'arshe Amin.