*RA'AYI.*
*12*
"Assalamu Alaikum".
Ya dakata har sai da suka amsa sallamar sannan ya d'ora."Mak'asudin taraku anan shine dan na aiwatar da alk'awirin dana d'auka akan zuri'ata na had'asu aure da junarsu.
"Ina mai farin cikin sanar daku nan da 3 weeks masu zuwa za'ayi bikin jikokina su 8 maza hud'u mata hud'u."
"Masha Allah." Kalmar da yayi tafowa kenan abakunan iyayen, yaran kuwa sai sunne kai sukeyi alamar kunya musanman matan.
"A saurara." Dattijon ya furta cikin natsuwa.
Duk sukayi tsit.
"Muhammad da Zubaida sun had'a kansu tun da jimawa haka zalika Munir da Zeenat suma sun had'a kansu, sunzo sun sameni kuma nasa musu albarka, Allah ya k'ara masu albarka."
"Amin ya Rabbi." Suka amsa.
"Ahmad yazo shi kad'ai ya tabbatarmin uwata yakeso kuma ta amince masa, suma Allah yayi masu albarka".
"Amin ya Rabbil Alamin." Suka kuma amsawa.
Dam!!! Gaban zarah ya buga, ta dubi inda Ahmad yake zaune suna had'a idanu ya sakar mata murmushin tabbatarwa, d'auke subanta tayi ta maida kan Zainul, ya marairaice kwallah cike da idanunsa sai kawai taji hawaye sun zubo mata tayi hanzarin gogesu tare da maida hankali kan maganar Modibbo.
"Mahmud shima shi k'dai yazomin har karo biyu na farko akan yana son Zubaida ce na biyu kuma ya fasa dan yafahinci waninsa ya rigashi dan haka yanemi alfarma da innema mishi auren Zaheeda."
"Ni Zaheedan ko wa?!!"
Tafurta hakan akid'eme."Shut up!!" Abba Aliyu ya umurceta cikin tsawa.
"Bita asannu Ali." Cewar Modibbo.
"Nanema mishi kamar yarda na d'auki alk'awari amma na samu anbada ita ga d'an yayar Abbanta dan haka na yanke had'ashi da Zulfa'a dan dama itace zab'ina agareshi, suma Allah yayi masu Albarka".
"Amin alfarman Annabin farko da k'arshe."
"Wannan kenan, yanzu zakuji jigon lamarin."
Duk suka k'ara natsuwa sosai.
"Uwata Zara'u tashigomin zuri'a da bak'on lamari ta haryar kawomin yaron kirki Zainul abideen amatsayin mijin da takeson ta aura haka shima ya tabbatar ita yakeso."
Hayaniyar da ya kaure shi yaja Modibbo dakatawa da jawabinsa.
Abba Abubakar ya tsawar sannan aka natsu amma fuskan kowa a bace yake dan sai aikawa Zainul harara sukeyi musanman yaran.
Abban Zarah kuwa jiyake kamar ya tashi ya mak'ure Zainul ya mace kowa ya huta.
"Ina mai bawa Zainul hak'uri dan Uwata dai dan uwanta zata aura wato Ahmad".
Wani shewan murna parlon ya d'auka, Zarah ta kwalla ihu ta zube gaban Modibbo tana cewa "kaimin rai Modibbo, wallahi banason yaya hero, Zainul nakeso, natsani auren zumuncin nan, nidai ka taimaka kabani zab'ina dan sonka da Ma'aikin Allah S.A.W."
Dafa mata kai yayi cikin sanyi haba "Uwata daina kukan hakanan badai kyason RA'AYINA saide naki ko?" Ta gyad'a kai, tana sauke ajiyar zuciya.
"Oh wato Zainul kika zab'a akan jininki Ahmad kenan?"
Shiru tayi tana jan hanci, ta zubawa Zainul idanu tana kallon hawayen dake shareware sai ya kuma karyar mata da zuciya ta kuma sakin kuka mai sauti.
"Modibbo dan girman Allah kada kabiye mata, mu muka haifeta ba ita ta haifemuba dan haka Ahmad shine zab'inmu bata isa ta kawo mana bare wanda baida cikakken asali cikin zuri'armu ba".
"Tabbas yaya Abubakar nima abinda nace da Modibbo kenan tun kafin kuzo". Abbanta ya amshe.
"Ya isheku hakanan, meye haka kukeyi mahaifinku na fad'a kuna fad'a kuma agaban yaranku, to bana son sakejin wani ya tofa kalma inba umurni aka bashi ba." Hajja kenan take tsawatarwa su Abban Zubaida da Abban Zarah.
Numfashi Modibbo yaja ransa abace yasoma magana "Shin nike da iko da yaranku ko kuke da iko da kayanku?"
"Ayi hak'uri Modibbo mun tuba, muda duk abinda muka mallaka naka ne, ikon kane kayi yarda kaga dama dashi". Abba Usman ya furta cikin ladabi.
Shiru yayi kamar bazaice komi ba zuwa can ya dubi Zainul yace "Yaron kirki kayi hak'uri haka Allah yaso bazaku auri juna ba dafatan zakayi nesa da zuri'ata dan gujewa afkuwan wani abin mara kyau."
Gyad'a kai yakeyi hawaye na zuba mishi da k'yar ya iya bud'e baki yace "Zan barta amma na tabba sonta shi zaiyi ajalina dan abinda nakeji bamai sauk'in fita bane, sannan ina umurtanku da Ku sa idanu akanta sosai dan....
"Dan me!!?, Oya get out from here!!! Bama son jin komai daga gareka, anriga da ansallameka."
Ya dubi munir "Send him out, bama buk'atar sonjin soki burutsun zancensa anan, sanda muke kula da ita da taimakon kane ko iya fi'ili."
Abban Zarah kenan ya tari numfashin Zainul, cikin tsawa.
Atake Munir ya kamashi yayi waje dashi yana ta zubar da hawaye tare da waiwayen Zarah wacce ta k'udundune kanta cikin laps d'in ta tana ta kuka dan baza ta iya kallon sanda za'afice da Zainul ba.
Jinjina kai Modibbo yayi batare da yace komi ba amma He pity him a k'asan zuciyarsa, nunawa ne dai bai yiba.
Addu'a yayi mai tsawo sannan suka shafa atare, taron ya watse.
Zarah ce first d'in fita Modibbo na kiranta amma ina ko waiwayensa batayi ba, Abbanta ya zabura zai bita, Modibbo ya dakatar dashi tare da gargad'insa akan duk ya doketa ransa zai b'aci.
Ahmad kam tsabar ta kaicin ganin yarda Zarah ke kuka wai duk akan bata sonshi, waninsa take so shi ya haifar masa da ciwon kai mai tsanani, dan tunda ya shige room d'in bai kuma fitowa ba hatta sallar magrib da isha'i a d'aki yayi su bai sami zuwa masjid ba, ya kwanta samar rug sai juyi yakeyi, ya rasa tunanin me zai samu yayi wanda zai sami sassaucin akan halin da yake ciki.
Abin mamaki sai k'arajin wutar sonta da k'aunarta suke kuma ruruwa cikin ruhi,jini, jiniyoyi tare da dukkanin part d'in jikinsa.
"Hasbunallahu walni'imal wakil". Shi yayi ta maimaitawa har barci ya kwashe shi.
Damben bala'i yake sha da wasu k'attin mutane, sai dukansu yakeyi yana jefer dasu kamar ya sami yayan mango, da kyar ya iya masu suka tsere ya k'arasa inda take kwance cikin jini ya rungumeta yasaki kuka, Zarah!!!!!!!!!!!!!;;
Afirgice ya farka ya duba agogo 12:pm darema baiyi ba sosai, addu'ar neman tsari da mugun mafarki yayi.
Jikinsa ba'inda baya rawa dan sosai mafarkin ya d'imautashi, mik'ewa yayi jiki ba k'wari ya fice zuwa part d'in Hajja dan yanaji ajikinsa can zai sameta domin ya tabbatar da lafiyan.
~Mrs j moon~
YOU ARE READING
RA'AYI
Romance"Mitchew!!" taja tsaki "Meke damuna ne ni ZARAH?' Ya Allah ka kawomin dauki alfarmar Annabin farko da k'arshe Amin.