*RA'AYI*
Na Safiyya.*06*
Asalinsu fulanin borno ne , masu tarin arzikin shanu da tumaka da amfanin gona, yawan tashi daga nan zuwa can shi ya kawosu wani daji dake tsakanin Kaduna da Zaria suka yada zango, a nan Allah yayi zamansu tsawon shekaru, har yaransu suka soma karatu a makarantar 'ya'yan maki ya ya, cikin yaran har da Abdul waris (modibbo kenan ) cikin ikon Allah yasami ilimin boko har matakin kammala secondary, daganan akayi masa aure da Mariya( Hajja) wacce take d'iya ga k'anin ard'o wato mahaifinsa kenan.
Ilimin islama kuwa wannan gadon sune dan haka yasami tarin ilimin addini wurin mahaifinsa dan Ard'o shine sarkinsu kuma limaminsu haka shine ke koyar da mutanen rigan ilimin addini gabi d'ayansu, to anan modibbo ya yi ilimisa shima har ya taimatawa mahaifinsa ya koyar da wasu.
Kwatsam sai gwafnati ta d'auki nauyin karatun yaransu biyu masu hazak'a zuwa k'asar Germany, ciki har da modibbo.Yatafi yabar matarsa da k'aramin ciki tare da iyayensa cike da kewa.
Shekaru 4 yayi a can ya dawo cike da nasarori, atake ya soma aiki a garin Kaduna cikin lokaci k'alilan ya maido da iyayensa kusa da shi, sai aka nad'a mahaifin Hajja Ard'o.
Iyayen Modibbo su biyu suka Haifa, shi da k'anwarsa maimunatu, ita tayi aure a garin Zaria.
Modibbo yazama magidanci mai tarin arziki dan harda kasuwanci yake had'awa kuma Allah ya albarci abin.
Ya haifi yaran 5 shida matarsa Hajja, hudu maza mace d'aya.
Abubakar, Umar, usman da Aliyu sai autarsu Bilkisu. Sun horasu da son junarsu da tarbiyya na gari.
Sabida hazak'ansa aka cillashi garin Abuja tare da babba mik'ami. Cikin lokaci k'an k'ani yazamo shahararren mai kud'i wanda ake kwatancen sa, ga yaransa son zakowa k'in wanda yarasa, koda suka isa aure dukkan ninsu a dangi yanemo masu mata haka k'anwarsu itama d'an amininsa kuma d'an uwansa yabama aureta, tana zaune Kaduna da yaranta maza da mata Zaheeda tana daga cikin yaranta.
Ard'o da Dada sun rasu sakamakon had'arin mota da sukayi akan hanyarsu ta zuwa ziyaran 'yan uwansu dake Riga. An jimamin rashinsu ainun, har aka hak'ura aka bisu da addu'ar samun rahamar Allah.
Modibbo ya gina masu estate nagani nafad'a acikin garin Abuja suka tare da iyalansa kuma a lokacin ya aurar da jikokinsa na fari wato Zainab,Maleela, mamun da takwaransa suna kiransa da Imam.
Burin Dattijon kenan had'a kan zuri'arsa wuri 1 ta hangar auratayya a tsakanin su, ya gina estate d'in mai d'auke da several parts.
Iyayensu mata kuwa sun zamo abar sha'awa, ba'atabajin kansu ba, hakan ya k'ara k'arfafa jan RA'AYIN dattijon na ganin zuri'arsa sun kammalu wuri d'aya shi yasa yaci alwashi ganin duk wanda ya taso ya kai minzalin aure to had'asu da junansu zaiyi.
Zuri'ace wacce take d'auke da wayewa ta ko wani fanni ta wadatu ba gidadanci cikinta sabida Modibbo yasan dad'in ilimin zamani da ta addini dan haka yasa ya ginasu da both.
Zainab ta yi dace abokin rayuwa amma Maleeka batayi dace ba ita, a sanadin bak'in cikin da Imam ya yi ta k'unsa mata bata fad'awa kowa ba shine ya haifar mata da ciwon zuciya wanda ba'fargaba sai da yazama chronic, and'orata akan magani ba jimawa ta ko ma ga mahaliccinta tabar yarinya d'aya mai suna Najiba.
A yarda Imam ya yi ta kuka da sanbatun duk irin muzgunawar da yayi mata ne aka kane shine silar kamuwarta da ciwon zuciya, iyayen sun gigita dajin irin abubuwan da yayi tayi mata amma bawan da yasani dan Maleeka zufin cikinta har ya baci.
Sunyi fushi da shi mai tsanani amma Modibbo yasa su dole suka yafe masa, kuma wannan abin bai sa modibbo ya janye R'AYIN sa akan had'a zuri'arsa aure ba sam.
Abba Abubakar da Umma sune suka haifi mamun, Munir,Zulfa'a da sauran su.
Abba Umar shi da Ammi su ne iyayen Zainab, Muhammad, Zarah, bayan rasuwar Amminsu ya auro k'anwarta wacce suke kira da Umma Amarya ita kuma ta Haifa yara 2 Noor da Muniba.
Abba Usman da Ummie sune iyayen Imam, Ahmad, Zubaida, da sauransu.
Abba Aliyu da mummy sune iyayen, marigayiya Maleeka, Mahmud, Zeenat da sauransu.
Zuria ce wacce ta ke d'auke da kyau da kwarjini gasu duk sunyi kamanni da junarsu musanman ta idanuwa da hasken fatarsu dan yarda kasan shuwa haka suke sabida dama fulanin borno sunfi zubi da shuwa, shi yasa in bakaji suna fulatanci ba bazaka ce asalinsu fulani bane kai tsaye.
Modibbo ya kan sanar da jikokinsa auren had'i shine RA'AYIN sa akansu duk in suntaru ana hira irin na jika da kaka amma sai gashi Zarah ta ta lashi takobin bore akan RA'AYIN nasa dan itama tana d'auke da irin nata *RA'AYIN* na kawo k'arshen auren zumunci da kakan nasu yaci burin aiwatarwa akan su dama sauran masu tasowa gaba.
_Continuation_
Zaune take a k'asar bishiyar cashew dake gefen d'aya a harabar gidan, an k'ayata wurin da chairs masu kyau tsakiyarsa k'aton table ne mai ban sha'awa, yankakkun fruits ne a plate ajiye samar table d'in tana sha a sannu kuma tana kallo a
cikin laptop d'inta, Zeenat ce ta iso ta zauna ta soma shan fruits d'in tana cewa "Ko za amutu ne wurin ciwon mara ya yin period kam sai musha zak'i mun more rayuwarmu.D'an dariya Zarah ta yi ta amsa "Kedai bari Kawai sis yanzu haka inajin itching kad'an kad'an kuma nasan abin ne zaizo dan time d'ina yayi amma kin ganni nan da chocolates and biscuits nayi break fast gashi kuma na tasa fruits ina ta d'urawa ciki barin ma Orange mai bada matsala".
"Allah dai ya kawo mana sauk'i amma zak'i kam abar so ce, mi za'ai da d'aci, ai asha zak'i shine dai dai".
"Zako kuwa ku yabama aya zak'i yara barinma wannan uwar 'yan rakin taji" tanuna Zarah, Zubaida ce kefad'an haka sanda ta iso inda suke.
"Madam ashe kin tashi ramakon barcin dan inajinki jiya kin raba dare kina waya, shin ko ke da waye kuke zuba love haka?"
Harara ta wulawa Zeenat, "To uwar sa eyes, wacce bata gani bata maganta ba, to da masoyina muke rak'ashwewa".
Dariya da sowa suka ka.
"Uhmm manya ansoma gane auran had'i bai da tsari kenan".
Duka Zubaida ta faskama Zarah, "Wallahi sis tun wuri kiyi watsi da banzan RA'AYIN nan taki tun bata kaiki ta baroba, ni bantab'a jin tsanar cikan burin Modibbo akanmu ba shiyasa ma tun kafin ya had'amu muka had'a kanmu kuma har gabansa munje ya kuma sa mana albarka dan haka kema ki bawa yaya Ahmad had'in kai kuje yasaka maku albarka".
Afusace ta mik'e "Allah ya tsareni tab'ewa da auren zumunci, kuma koma zan yisa badai da yaya Hero ba, dan haka kada kisake yi min wannan banzan zancen tam".
"Shima cewa yayi yana RA'AYIN ragowar club da har kike wani zak'alk'alewa haka". Zulfa'a ce ta amshe zancen da isowarta wurin.
"Zulfa!! Had'uwarmu dake ba zai miki kyauba Billahil azim". cikin k'araji Zarah take gargad'inta.
"Ina ruwanki ne da zancenmu ko dai salon sai tasake karyaki?"
"Mantawa kikayi Uwar dai zata karya ba ni ba".
Afusace Zeenat tayi kanta Zarah ta rik'eta gam, Zubaida ta zuwa tagumi tana binsu da kallo, suna ahaka motar Muhammad tashigo ta Munir na biye dashi.
Kamar walk'iya duk suka bace a wurin dan sun san in har Muhammad yasamesu awuri bak'aramin bata musu rai zaiyiba, barinma da ya hangosu kamar suna fad'a.
~Mrs j moon~

KAMU SEDANG MEMBACA
RA'AYI
Romansa"Mitchew!!" taja tsaki "Meke damuna ne ni ZARAH?' Ya Allah ka kawomin dauki alfarmar Annabin farko da k'arshe Amin.