page 30

2.2K 41 0
                                        

Ra'ayi.

Na safiyya.

*30*

"Alhamdulillah mun iso lafiya sweetheart."

Lumshe idanu tayi murmushi kwance a fuskanta "Masha Allah, dukkan yabo da godiya sun tabba ga Allah da ya amince mana isowa cikin nasara."

Kiss ya manwa lips nata, ta bud'e idanu da sauri tana waige-waige.

Dariya yasaki "muna cikin mota wa kike tunanin zai gani?"

"Oh hakane kuma."

"Nagaji my Hero bari nashi ciki."

"Ohk nima ana kammala d'aurin auren zan shigo."

"Allah ya baka iko."

"Amin."

"Am bakiji ba."

Dakatawa tayi da fitowar amma k'afafunta suna waje.

"Kada kimanta by 9:00pm kifito mu wuce masaukinmu."

Shiru tayi masa tana kallon cikin idanunsa, shima ita yake kallo cikin serious.

Murmushi ta saki "Kada kasamu damuwa zan fito ai."

Cikin jin dad'i ya kamo hannunta ya mannawa yatsunta peak.

Batare da ta kalleshi ba tafice cikin takunnan nata mai cike da k'asaita.

Bayarta yabi da murmushi yayi release jikin seat hannunsa samar sajensa yana shafawa cike da nishad'i yace "Sweetheart manya komi nata daban yake dana kowwa, Allah ya saukeki lafiya mata ta, Amin."

Da Umma Amarya tasoma cinkaro ta tafi da sauri ta rungumeta "I really miss you sweet Umma."

"Uhmmm Adon mata kun iso lafiya?" Ta furta cike da kulawa.

"Lafiya lau Ummana."

"Madallah, ina Ahmad d'in?"

"Zai shigo da zaran an gama d'aurin auren."

"Ohk, kingaji taho ki huta."

"To Ummana." Tana shirin janye jikin Zaheeda na tafito daga cikin parlor.

"Harara ta soma tsilla mata sannan tace "Umma Amarya yanzu wannan k'atuwar kika bari take lole miki jiki kamar wata baby?"

"To kanwa uwar had'i, an lole d'in, halan jikin ki ne?"

"Kashh!! Namanta nace bazan kulaki ba ko da kinzo mitchew."

Sakin Umma tayi ta kamo hannun Zaheeda wanda yasha lallen amare mai ban sha'awa.

"Affuwan Amarsu ta Ango mai dad'in miya."

"Dalla ni sakeni baruwana dake ehee."

"Laaa jibeta Ummana, wai fushi take dan ba'azo bikinta da wuri ba, ikon Allah yaran zamani ba kunya sam."

"Innalillahi! jimin sharri da rana tsaka dai."

"Eh fa ba wani sharri tunda ga alamu nan kin nuna kina turemin d'iya daga isowarta ko ruwa bakiyi niyyar bata ba balle wurin zama, to taho abinki ni da kaina na wadataki da kome kike da buk'ata." Cikin zolaya Umman ke zancen, yayin da Zarah ke yiwa Zaheeda gwalo.

Da gudu Zaheeda tanufi side d'in da k'awayenta suke cike da jin kunyar.

"Thank you sweet Umma kin kashemin bakin wannan saura na 'yan sa idanun can kuma."

Kamo kunninta Umma A. tayi ta d'an ja "Ai ke da Ahmad baku data ido sam dan haka ina goyon bayarsu, su cashemin ke da kyau."

"Ummana please."

RA'AYIWhere stories live. Discover now