*Ra'ayi.*
*10*
K'udundune take cikin bargo tunani ke cikin ranta fal, tun sanda tabaro side d'in su Ahmad tarasa dawowa cikin natsuwarta, ta rasa da wanne zata fara cikinsu da zararar takamo wannan zata saki ta kamo wancan, ganin ta rasa madafa yasa ta sakko jiri na d'ibanta ta shiga bathroom ta d'auro alwala ta hau samar sallaya ta soma jero nafilfili bayan ta idar ta d'ora da jan tasbaha, ta d'auki kimanin 3hrs tana mik'awa Allah kukanta, abin mamaki addu'ar nata yafi karkata akan Allah ya d'orata kan Modibbo ya amince da zabin ranta.
Bayan ta shafa addu'ar sai ta zame a wurin ta kwanta, atake ko barci ya yi gaba da ita.
Gudu ta ke irin na ceton rai wasu k'atti majiya k'arfin maza suke binta da gudu burinsu su kama ta, tun tanayi da k'arfinta har ta gaji ta fad'i k'asa warwas, a dai dai lokacin kuma k'attin sun iso gareta, cak suka d'auketa tana ta tsala ihu.
"Yaya Hero!!, yaya Ahmad!!!!!."
Afirgice ta farka duk ta had'a gumi sai mai da numfashi takeyi jikinta ba inda baya rawa.
"Innalillahi me hakan ke nufi kenan?, su waye wad'an nan jifga jifgan mutanen masu kama da 'yan jiwaye?, to meye dalilina na kiran yaya Hero alhalin da haushin wulak'ancin da ya yi min na kwanta?"
Tambayoyin da Zarah tayi ta jerawa kanta kenan amma bata iya samu amsa d'aya ba.
Jin ana kiran sallar subahi yasa ta mik'e ta shige toilet dan haramar gabatar da sallar amma fa brain d'inta cike ya ke taf da tunani barinma son jin abin da ya kai Zulfa d'akin Ahmad da son jin abin da suka zanta akai.
Misalin 9:30am duk jikokin gidan manya sun halarta a side d'in Hajja suna yin break fast, dan kullum break and supper anan su ke gabatarwa lunch ne dai kowa yakeyi a in da yaso.
Bakajin sound d'in komi sai na spoons.
Ahmad ya matsa cikin dabara ya sa cover d'insa ya murjewa Zarah toes, tari ta soma yi dan azabar zafin dataji dama tea ta ke sha ta ke ko ta sark'e ta soma tari, ya yi saurin mik'ewa kamar bashi ya haddasa faruwan komi ba.
Kamata ya yi ya soma shafa mata baya yana ta jera mata sannu. Zubaida ta bata ruwa har tarin ya lafa ta juyo ta kalleshi ya sakar mata murmushin gefen baki, irin na muguntar nan.
Kauda kai tayi batare da tace dashi komi ba.
'Yan uwanta sai sannu suke jera mata tana amsawa cikin dushewar voice dan har zuwa time d'in bata gama zama normal ba.
Mik'ewa tayi batare da ta kammala yin break d'in ba. Bedroom d'in Hajja ta shiga ta kwanta ta fad'a kogin tunanin muguntar da Ahmad yake yi ma ta yanzu.
Bataji motsin shigoqarsa ba sai jin maganarsa ta yi a fegen kunninta.
"My Star ya dai, jikin ko garin?"
Banza tayi masa tare da juyawa ta kwanta rub da ciki, juyo da ita ya yi, tayi saurin tashi zaune ta rufe idanunta tare da d'aga masa hannu.
"Ya isheka hakanan abin da kake min yaya Hero!! Wato wulak'anci dakayimin jiya bai yi maka ba sai yau ka kuma fito da wani sabon salon muguntar, kalla kaga yarda yatsun k'afana sukayi ja dan azaba". Tana nunu mishi tare da d'ago masa leg d'in sama.
Kallo yabi yatsun da shi ya saki murmushi mai sauti.
"Alhamdulillah, kinji irin zafin da naji daren jiya cikin heart d'inta".
Kallon sonjin k'arin bayani ta yi masa, ya dalla mata harara, tayi saurin sauke kanta k'asa.
"Allah ka d'ai yasan halin da zuciyata ta fad'a duk kuma kece sanadi, wai ace kama na da tarin matsayin dana ke da shi agareki amma in baki umurni kik'i aiwatarwa sannan in kiraki kina kallo kik'i d'agawa, amma sai akarin banza ki kwaso jiki wai kinzo, to inmiki me a lokacin?"

YOU ARE READING
RA'AYI
Romance"Mitchew!!" taja tsaki "Meke damuna ne ni ZARAH?' Ya Allah ka kawomin dauki alfarmar Annabin farko da k'arshe Amin.