Ra'ayi
Na safiyya.29*
Kai da kawo take ta faman yi tsakanin parlor da kitchen a k'ok'arinta na ganin ta kammala girkin datake had'awa aminin Ahmad, Bashir wanda yace zai kawo masu ziyara tare da iyalansa.
Duk inda tabi idanunsa na kanta musanman ma zaunarta wanda sukayi mugun cika da fad'i na ban mamaki. cike yake da son kasancewa da ita amma baiga fuska ba.
Tunda su Umma Amarya suka wuce Riga take k'unci, tak'i bashi fuska sam, shima kansa yasan bai kyauta mata saboda dai dai da sallama ya rakata zuwa yimasu shi yasa fushinta ya k'aru, yana lura da take takenta kad'an take jira ta yayyafeshi da ruwan tsiwarta dubi da yarda take aiwatar da aikin baki ture dagani dakon ya tankata takeyi.
Sosa sumar kansa yayi da biron hannunsa yasaki doguwar mik'a, lissafin da yake aiwatarwa ne yaji ya kasa gane komi dan haka ya tattarasu gefe ya kwanta rigingine idunsa na kollon samar ceiling.
Tab'e baki tayi sanda ta iso daf dashi zata d'auki yankakkun vegetables da yatayata yanwa.
K'afa yasaka mata ta fad'o k'irjinsa, matseta yayi yana fatan samun relief a yanayin dake ciki.
"Sakeni malam, bakaganin aiki nakeyi ne?" Cikin tsiwa tace dashi.
"In ank'ifa?"
Kauda fuska tayi gefe cike da jin haushinsa.
"Nace in ank'i sakin naki fa?"
Tarin fitina ta hango kwance cikin idanunsa dan haka sai tayi k'asa da voice cikin marairaicewa tace "Dan Allah Yaya hero kasakeni kada abincina ya k'one."
Bakinta ya kaiwa kiss bata hanashiba, kad'an ya tsotsa bakin sannan ya saketa, tamik'e da hanzari.
"Baruwana kai ehe."
Ya yunk'ura zai biyota tayi hanzarin fad'awa kitchen ta kullo.
12:pm ta kammala girkinta ta jerasu Samar dining sannan tashiga wanka tana cikin shafa mai tajiyo isowar bak'in nasu.
Koda fito sai taja tayi turus ganin Bashir shi kad'ai batare da aminiyar nata ba.
"Yawwa Sweetheart kada ki kulashi da saninsa yak'izuwa miki da ita, ba wani lauyewa da zaiyi miki kan ki aminta da shi."
Hararan wasa Bashir ya sauke masa sannan ya had'e hannayensa "Affuwan madam wallahi bansan tana da biki ba sai da nace tafito mu wuce, wai ashe k'anwar mamanta tana aurar da 'ya dan bana garine yasa bata halarci programs d'in ko sau d'ayaba gashi har yau ake yinin biki, amma hak'ik'a taso zuwa, tace agaisheki tare da baki hak'uri, dafatan za'a duba uzirinmu."
Murmushi ta saki "A babu komai ai zumunci yana da dad'i kuma mai sadar dashi yana da babban ladama mara adadi, Wanda ya tauyesa kuwa wannan yafi kowa sanin hukuncinshi wurin ubangiji."
Sosa kansa Ahmad yayi yana jifarta da wani kallo dan yasan sarai magana ta tura masa amma tak'i yarda suhad'a eyes.
"Thank you madam Dr. AA Modibbo."
"You're welcome."
Jagora tayi masu zuwa dining.
Bayan sun kammala suka dawo parlor suka soma hiran business nasu ganin haka sai ta shige bedroom ta kwanta, ta bud'e data.
_Dad'i miji ina hanyar zuwa gidanki, saura kibari har in'iso baki tanajeni ba, salon sai nazo kisani shiga kitchen da kaina._
Dariya ta saki sanda tagama karanta sak'on Hafsat.
"Hafsatuwa hoo bata wasa da ciki."
Kwanciya ta gyara tana bin labarin littafin *MARUBUCIYA CE* _na Sadia Lawal Bala._

ESTÁS LEYENDO
RA'AYI
Romance"Mitchew!!" taja tsaki "Meke damuna ne ni ZARAH?' Ya Allah ka kawomin dauki alfarmar Annabin farko da k'arshe Amin.