page 31

520 32 0
                                    

Ra'ayi
Na Safiyya.

*31*

Cike da kasala tasamu ta kammala shirin barci ta nad'e cikin bargo, bajimawa barci mai dad'i ya d'auketa.

Cikin barci taji yana lalibanta.

"My hero please am tired kaji tausayina man."

Ko kulata baiyiba, haka nan ta soma biye masa badan tasoba.

Mamakin yarda yakebi da ita ne yakasheta. Sai kace mayunwacin zaki haka ya koma mata, tuntana jurewa har tasoma tureshi tana sakin nishin wahala, shikam sai k'ara k'ank'ameta yakeyi cike da sauk'i.

"Wallahi yaya zan had'aka da Ummie, nagaji nace maka ko so kake sai nasoma yima kuka sannan zaka k'yaleni?"

Shitttttt Sweetheart in ana sallah ba'a magana." Yace da ita cikin rad'a, jin zata sake magana sai ya had'e bakinsu dan kawo k'arshen k'orafin.

Washe gari cikin k'arfin hali take aiwatar da hidimar had'a breakfast sabida ciwo da maranta keyi mata amma tak'i bari Ahmad ya gane.

Karyawa sukeyi wurin yayi so silent sabida sarkin tsokanar yau sai a slow.

Farfesun kayan ciki take ci a hankali kamar maicin magani.

Yana hankalce ta dukkanin motsinta, yana lura da yarda take ta cije lips fuska a yamutse, sai da ya kammala sannan ya matsa kusa da ita amsar spoon d'in da take cin farfesun yayi ya d'ebo  ya nufi bakinta, ganin ya had'e rai ba wasa yasata amsa kan dole saida yaga ta cinye duka sannan ya kafa mata tea cup shi kuma kad'an tarage ya k'ara tura mata ragowar tasoma yunk'urin amai yayi sauri janye kofin ya kwanto da ita jikinsa yasoma shafa mata baya.

Ruwa yabata ta sha, ya kalleta cikin tausayawa yace "Sorry sweetheart, bazan k'araba in Allah yaso."

"Uhmmm koda yaushe haka kake cewa Ai amma da an kwana biyu zaka kuma maimaitawa."

"Sweetheart duk fa ke ce kija na d'imauce."

"Uhmmm bawani nan kai dai cinzalin d'inka yamotsa."

"Trust me Alfahin Ahmadu, Allah bansan inda kaina yake ba lokacin."

Harara da dalla masa tare da mik'ewa "Inajin dai asirin aka kuma yi maka, dan haka tun wuri ka samo mafita dan Wallahi yanzu bazan iya d'aukan wannan lamarin ba, inkuma ba so kake na koma side d'in Ummie har zuwa sadda zan  haihu."

Dariya tabashi amma ya kanne bai yiba.

"Nace affuwan bazan k'araba, da kike kuma maganar asiri kinsan wallahi Allah kenan ayanzu nasan nafi k'arfin duk wani mugu ko da can da akayi nasara akaina sai da aka samin shagala da addu'a tare da ibada sannan aka sami nasarata dan haka yanzu inada yak'innin ba dai sharrin mutun da aljan ba sai dai in k'addar Allah wacce take tabbatacciya ce ita akan kowa."

"To Allah ya k'ara tsaremu"

"Amin."

"Amma Allah karage tun wuri kada na fece tam."

Dariya yake tayi mata tare da tsokanarta raguwa.

Taimaka masa tayi yashirya duk cikin dauriyan ciwon dake kamunta, shi kuma sam bai lura da yanayinta ba

Awani yammaci lokacin cikinta yashiga wata na biyar, ta dubeshi tana yamutsa fuska.

"My hero wai halan duk likita jarababbe ne?"

Yana matsa tafin hannun ta ya amsa "Me kika gani?"

"Komai ma nagani akanka yallab'ai."

Knock yabata kad'an akai, tasaki siririyar k'ara, sai kuma ta mik'e da sauri tanufi room nata.

Bayanta yabi yasamu ta shiga toilet, zama yayi gefen bed ya d'auki wayarta dake samar bedside drawer yana dubawa.

Shiru shiru tafito bata fito ba, gabansa yaji ya fad'i ras!! Ya mik'e da sauri tura door d'in yayi ya shiga.

Tana tsugune sai nishi takeyi, ta had'a zufa ga blood nan sai zubowa yakeyi ak'asanta.

"Meye haka Zarah!!?" Ya tambayeta ciki k'araji.

A wahalce ta d'ago kai muryanta so cool ta amsa "Jini ne yaya, tun jiya yasoma zubomin sai ya d'auke to yanzu da nazo fitsari na ganshi ya dawo mai yawa kuma harda ciwon mara nakeji cikina wani abu na motsawa da k'arfi."

Jikinsa ba inda baya rawa yasoma ambaton Allah cikin ransa, shi ya taimaka mata ta gyara jikin, ya d'aukota direct waje yayi da ita ya saka a mota ya fizga da gudu.

"Nasan ni najanyo miki shan wannan wahalar sweetheart, gashi nan zan rasa babyna, ya Allah kakawo min d'auki kada narasa cikar burina."

"Amin." Ta amsa idanunta kulle, hawaye nazubo mata.

Shi da Dr. Safeena sukayi nasaran tsaida jinin, allura akayi mata dan  samun hutu.

"Thank you dr. Safeena."

"You're welcome."

"Dan Allah dr. kakiyaye samuwar ingantuwan lafiyarta, kadai ga irin tsallake rijiya da bayar da tayi, kak'yar muka samu nasaran cikin bai fitaba kuma duk yawan takurawar ne wurin saduwa ya haifar mata da zubar jinin dan haka be careful please."

Yana murmushi tare da sosa tsinin hancinsa da biro ya amsa "Don't worry dr. I will do my best ganin  lafiyarta dana babyn bai kuma samun tangard'a ba, I learned a lesson about my neglect. I don't want to loose my baby.

"Tam Allah ya taimaka."

"Amin."

"Inda hali bed rest za kabata kamar na 2 weeks to 3, lokacin tasami sauk'i kuma mahaifar ta k'ara k'wari and koda ta dawo duty to abita asannu tunda kasan yarda take bamai juriyar... kadai gane."  Ta k'arasa cikin 'yar dariya.

Shima dariyan yayi yace "Dr. Ashe kina da surutu haka?"

Juyawa tayi ta nufi hanyar fita batare da ta amsa mishi ba, sai kuma tajuyo.

"Yawwa dr. AA miyasa mafi yawancin doctors maza sunfiye takura matarsu da yawan buk'atuwa ne?"

Dafe kansa yayi tare da kafeta da idanu.

"Da alamu kema yallab'ai na takuraki kenan ko?"

Da sauri ta murd'a handle "Mubar zancen tunda abin hakane, ina tambayarka kana cillomin wani tambayar."

Dariya ya saka "Ki amsamin sai kiji amsarki."

"Bye, Allah bawa mmn twins lafiya." Ta katse zancen tare da ficewa.

"Ohk bye." Yace yana dariya.

Rik'e yake da hannunta yana ta tofa mata addu'o, I'm sorry dear, daga nan side Ummie zan kaiki direct dan ki samin hutu yarda yakamata sabida in ina ganinki agaba lallai da matsala bazan iya jurewa ba, gara muna nesa da juna har zuwa sadda zaki dawo normal." Haka yayi ta surutunsa batasan yanayi ba.

Washe gari duk 'yan dubiya sun watse sai shi kad'ai zaune gaban gadon da take kwance tana barci, hannunsa rik'e da k'aramar Al-qur'ani tilawa yakeyi, sannan kuma yana dakon isowar mommy sannan ya samu tafiya duba patients nasa.

Knocking akayi, ya kallo k'ofar "Yes come in."

Wata budurwace ta shigo tana dogara sanda bayanta kuma wata matashiyar mace ce.

Wurin zama ya nuna musu, suka zauna tare da gaisheshi, amsawa yayi cike da tarin tambayoyi.

"Sunan Lawisa k'awar Rahila, wannan kuma mahaifiyarta ce."

Bata rai yayi jin sunan Rahila, ya tsuke fuska tamau.

'Dole Rahila ta rud'e akanka, wannan irin kyau da kwarjini da Allah ya baka ko ni nayaba kam'

"Uhmm me ke tafe daku?" Maganarsa ya katsewa Lawisa tunani.

Gyara zama tayi ta dubi Umman Rahila, Umman tagyada mata kai.

RA'AYIOnde histórias criam vida. Descubra agora