*RA'AYI*
'''Na Safiyya'''*09*
Tafiya suke kamar kurame shi hankalinsa na bisa titi ita kuma nata na kan phone d'inta, sai latsawa ta keyi murmushi d'auke a fuskanta.
Kallonta ya yi a ta k'aice ya maida hankalinsa kan hanya, traffic light ya dakatar dasu, ya juyo da hankalinsa kanta ya mik'a hannu ya fizge wayar ya jefa a aljihun gaban rigansa, idanunta ta d'ago cike da tsiwa sai kuma tayi hanzarin mai da su k'asa sakamakon wasu kibiyoyi da taci karo dasu cikin k'wayar eyes d'insa.
Cikin sanyin murya tace "Yaya kabani wayata, hira fa na ke da k'awayena ka amshemin".
"Oh yanzu hiran da kikeyi da k'awayenki har yafini mahinmanci ke nan?" Yace da ita hakan ahankali kamar baison maganar tafito.
Shiru tayi masa tana wasa da yatsun hannunta wanda suka sha jan lalle.
Shafar yatsun ya yi ahankali, ta dubeshi da hanzari ya kanne mata 1 eye "Sun burgeni sosai, ki yawaita yinsa yana yi miki kyau".
Kauda kai tayi gefe "Uhmm, ni dai kabani wayata". Tare da mik'a masa hannu, tafin hannunta yabi da kallo sunyi fari sol da kuma cika.
Murmushi ya saki mai sauti "Uhmm wannan time d'in banji ankirani yi miki allura ko baki magani ba, ko dai anyiwa kai fad'a ne shi yasa abin baizo da neman agajina ba?"
Cikin rashin fahimtar zancensa tace "me ke nan ba?"
"Abin naku na mata man".
Kallonsa tayi da mamakin yarda akayi yagane tana period, gira ya d'aga mata _kinmanta cewa I'm a qualified doctor?"_
Numfashi ta sauke tare da kauda fuska, cikin jin kunya tace "To yau likitancin naka ya fad'ama gaibu".
Dariya ya saki tare da jan motar ganin sun sami hanyan wucewa.
"Tunda zancena gaibu ne to in mun isa inda muka nufa ki sani dole sai kinyi min gudu kuma ki kamin dash-dash ni da ke ne".
"Wallahi ba mai sani gudu sai kace wata kwaila, taf uhmm lallaima."
Kallon bakinta ya keyi har steering motor ya kusa kubce masa.
"Ya salam!!". Ta furta da k'arfi.
"Ni dai dan Allah ka duba hanya da kyau, kada asami matsala."
Baice da ita komi ba har suka isa gate d'in wani d'an ma dai-dai cin flat, horn ya yi Gateman ya bud'e, ya shiga mai gad'in yana tayi masa sannu da zuwa kamar zai sunkuya k'asa, kud'i mai yawa ya fiddo ya mik'a mishi, yako damk'e tare da fad'in "Allah yabarku tare da juna ya rabaku da sharrin mak'iya ya kuma bada zuri'a nagari".
"Amin, Amin Baba Iro." Ahmad ya amsa cike da jin dad'i.
Baki ta tab'e, "Iska na wahalar da mai kayan kara".
Bayan ya gyara parking ya jingina da seat ya zuba mata idanunsa, itama idanun ta zuba mishi cike da tambayoyi.
"Me kike nufi da kalamanki".
"Me kuma nace?"
"Zan baki mamaki k'warai da gaske, ciki gaba ina tambayarki kina maidomin da tambayar."
"Affuwan dan Allah yaya."
Gyara zama ya yi "Gidan abokina Bashir mukazo, matarsa ta haihu har anyi suna bansamu damar zuwa ba sai yau shi yasa nazo dake ko sayimin sauk'in k'orafi dan ganin idanunki".
Jinjina kai tayi cike da gamsuwa "Amma kasan barka zan rakoka shi ne za muzo haka hannu sake ba ko d'an yiwa baby sayayya".
Dafe goshinsa ya yi "kashh! wallahi sam na sha'afa ne."

YOU ARE READING
RA'AYI
Romance"Mitchew!!" taja tsaki "Meke damuna ne ni ZARAH?' Ya Allah ka kawomin dauki alfarmar Annabin farko da k'arshe Amin.