page 35

1K 41 0
                                    

Ra'ayi.
Mrsjmoon.

*35*

"Yallab'ai sakemu kada ka tashesu su hanamu barci."

Sake k'wak'umesu yayi yana sauke ajiyar zuciya da sauri da sauri, asannu yasoma sasauta rik'on da yayi masu har ya sakesu, ya zaune gefenta ya tsira masu idanu.

Murmushi tayi tare da mik'ewa, yayi saurin amsar yaran ya nufi d'akinsa da su, bayanshi tabi, samar wani gadon yara mai kyau ya shin fid'esu, ya jima yana jan addu,o'i sannan ya tofesu, ya juyo inda take tsaye tana kallonsa, ido 1 ya kashe mata tare da d'age gira, yace "Madam zo kimin wanka ki shiryani tsaf dan yau ango nake sai da riritawa."

Murmushi tayi tana mai kauda kanta gefe.

Hannunta ya kama zuwa bathroom, haka nan bayarda ta iya da rigimarsa tasoma yi masa wankan ta shiryashi, bayan ta kammala taja gefe tana kallonsa, langab'e kansa yayi kamar wani yaro, 'yar dariya tasaki, ta juya tafice zuwa room nata, bayarta yabiyo da sarsarfa, tanajin ta kunsa ta kwasa da gudu ya rufa mata baya, atare suka shiga d'akin suna dariya.

Cukumarta yayi ya jefa samar bed ya rufeta ruf da jikinsa tare da sakar mata nauyinsa.

"Washh!! Darling hero kayimin rai ka d'agani, kasanfa bangama k'wariba, bana da k'arfin d'aukanka yanzu."

D'agata yayi, ta tashi zaune tana jifarsa da hararan wasa.

"Oh dama wayau kikaimin, to bari kigani."

Kafin ta motsa ya maidata kwance, yasoma aika mata d'an sak'o, magana takesonyi ya k'i bata dama ta hanyar zira tongue nasa cikin bakinta.

Sun raya daren cike da farin ciki, tayi ta mamakin yarda yakoma mata kamar sabon shiga, albarka da sanbatu kuwa ta shashi har ta gode Allah.

Barci ne ya d'auketa mai dad'i bayan ta tsarkake jikinta.

Tsotson nonon yasa ta farko idanunta cike da barci take dubansu, ya sakawa Hussain nono abaki sai tsotsa yake cikin sauri yana ta sauke ajiyar zuciya, alamun yajima yana  kuka.

Tashi zaune tayi tallabe da yaron tana cewa "Ina Hassan?"

Da yatsa ya nuna mata gadonsu dake cikin room nata, lumshe idanu tayi "Kuka sukayi ko?"

"Eh, cikin barci naji kamar kukansu koda naje Hussain yaci kuka har ya gaji, Hassan ne ma baisoma kukanba saida yaga na d'auki d'an uwansa."

"Ayya affuwan yarona, laifin dadynka ne da ya gajiyar dani, sorry kaji."

Tana maganar ne cikin shafar kan yaron kamar yanajinta ya saki nonon ya tsira mata idanu ta lumshe nata sai kawai ya  washe baki ya sake kama nonon yacigaba da tsotsa, jinjina kai tayi ta furta "Thank you boy."

Ajiyar zuciya Ahmad yasaki cike da al'ajabin abinda yaron yayi, matsowa yayi yana lek'en face d'insa yaga har yakoma barci amma bai daina tsotsan nonon ba, kallonta yayi ta sakar masa murmushi, ya maida mata da martani.

"Sweetheart amma Hussain yafi Hassan tsotso ko?"

"Ai komi Hussain yafi Hassan, rigima, tsotso, fara'a, rashin hak'uri, duk Hussain ya tarasu amma kaga Hassan baruwanshi sam."

"Ikon Allah, to Allah yaraya manasu cikin amincinsa."

"Amin dear."

Washe gari koda ya dawo daga masjid taddata yayi tana bawa Hussain nono.

Zama yayi gefenta cike da tausayawa ya furta "Sannu my heartbeat, Allah ya biyaki da mafificin alkhairi."

Can k'asar mak'oshi ta amsa "Amin."

"Hope kinyi sallah dai?"

"Eh, nayi harma nayi wanka, lotion nakeson shafawa ya hanani."

"OK kawoshi tunda naga yasaki nonon da alama ya k'oshi kenan."

RA'AYIWhere stories live. Discover now