04

1.3K 103 0
                                    

*RA'AYI.*

*04*

"Wai Musbah meke damunka, gabaki d'aya a 'yan kwanakinnan ka koma wani silent, aikinka kenan jan tasbaha, jam'in sallah baya wuceka yanzu ga yawan azumi da tsayuwar dare kamar wanda ya sami labarin cewa mutuwarsa ta kusa isowa ko mai son zama sufi?".

Murmushi yabii jimie da shi kawai, yaci gaba da jan casbinsa bakinsa na motsi alamar hailalah ko istiggifari yake aiwatarwa.

"Dalla jimin banza kawai ya ina magana zaka shareni, wai ko duk tsaban begen 'yar kan uban yarinyancan ya maidaka haka?"

Sai da ya Shafa addu'arsa wannan yace "Wacce yarinya kenan?".

"Zarah take ko Zainu ohoo?"

"Oh! Allah sarki baiwar Allah, Zarah sunarata ba Zainu ba malam. kwana biyu na daina ganinta, visa gadukkan da alamu sunyi hannun riga da yawon zuwa club, inko hakan ta kasance zan fi kowa murna dan irinta mai cikar kamala kuma wacce ta fito daga babban gida irin tasu lallai zuwa club zai zamo abin zubba mutunci ne".

"Uhmm kaji Mr love ba, to ai sai ka zage dantse ka soma kafa gwafnatinka, ko kaima kazama d'an babban gidan masu mutunci".

'Dan dariya ya yi atak'aice  "Kai yallabai ni nace maka ba so irin ta aure nake mata ba, so irin ta addinin islama nake mata, wanda Allah SWA ya sanar da  manzo SAW shi kuma ya koyar da mu da muso 'yan uwarmu musulmai a duk inda muka had'u dasu kuma mukare masu mutuncinsu bakin iyawarmu".

"Allahu Akbar, antuna da karatun islamiyya kenan yau ya sayyadi". Yafad'a hakan cikin izgili.

"Ina rabata da wannan abin fa oga tam".

" Nabari alaramma".

"Uhmm yallabai kenan to bari kaji  bama karatun islamiyya nake tunawa kad'ai ba a kwanakin nan kam harma da wacce tayimin jagorancin zuwa islamiyyar amma nasa k'afa na ture a wancan lokacin na biyoka yawar dandi, wato innarmu ba, uwa mai tarin nagarta da gudun duniya, samun uwa kamarta a zamanin nan sai antona".

"Hmmm haka ne zancenka amma ba irin tawa uwar ba mai sani sato kaji da agwagi ba, wacce itace silar zamowata komi ayanzu, ai ni wallahi ko sau 1 bantab'a tunowa da ita ba balle kewarta ya bi dameni haka kawai ina tsaka da holewata Allah ya kiya sheni tab'ewa".

Iska mai huci Musbah yafeaar ya dafa Jimie "Wannan kuma RA'AYIN ka ne Jamil amma dai kasani uwa duk yarda take uwa ce kuma dole a girmamata ko da rai bai soba".

"Malam rabani da zancen Iya kawai".

" Tam shike nan, Allah ya shiryaka".

"Ya shiryamu dai banza kawai".

Murmushi yak'e ya yi masa tare da cigaba da sanar ashi abinda ke samunsa. "Ayarda nake yawan mafarkin innarmu nasan cikin biyu za'ayi d'aya, ko dai bata da lafiya ko kuma Allah ya amshi rayuwarta, hak'ika hankalina da tunanina yakoma gida kacokan yanzu, ina son ganin mahaifiyata da 'yan uwana ainun, shekaru goma ba fa kwana goma ba ne, shin ko yanzu awani hali suke oho." Hawaye mai zafi ya zubo masa bai damu da ya goge suna.

"Anya ni Musbah inason rahaman Allah ya baibayeni kuwa ranar mahashar?"

Ya tambayi kansa amma ba amsa sai ruwan hawaye da suke zarya a fuskarsa kamar bakin tap.

Jimie wanda yazuba tagumi yana kallonsa k'uri ya sauke numfashi tare da matsowa jikinsa yasoma yi masa magana cikin sigan rarrashi amma dagani baikai zuciba "Abokina kuma yarona be a man, kada kabani kunya mana ace  tunanin gida da tsohuwa sune zasu maidamin da kai ragon maza haka, ka koma mace, haba my friend ka dubafa kagani yau kusan kwana 4 kenan ba ka fita operation kuma in an samo arzikin ko an ba ka kak'i amsa, duk ka jagula mana lissafi, jikinmu duk ya yi sanyi, ka daina barin ana moranka cikin jin dad'i, shin ko ka san inbaka rok'emu gafara ba akan wuyar da kake kan bamu  Allah bazai barka hakaba sai ya bi mana hakk'inmu?"

RA'AYIWhere stories live. Discover now