13

917 71 0
                                    

*RA'AYI*
'''Na Safiyya.'''

*13*

Tura k'ofar yayi yajita b'ud'e dama yasan b'ud'e zai sameta dan haka k'ofar Hajja take koda yaushe, ta kance koda ana neman taimakonta basai ansha wuyar nock ba.

Sallama yayi can k'ansan mak'oshinsa yarda bawanda zaijiyosa saishi kad'ai.

A sannu ya shigo, hangota yayi kwance samar 3 seater jikinta babu riga, Hajja ce zaune a gabanta samar rug tana aikin goga mata towel bayan ta matse ruwan jikinsa wanda take tsomosa cikin wani bowel mai d'an fad'i, sai kuka takeyi mara sauti dan daga inda yake tsaye yana jiyo shashshekanta, haka yana kallon duk abinda kefaruwa duk da rashin yalwan hasken dake parlorn.

K'arasowa yayi cikin sanyi ya tsugunna a gefen Hajja yana mai cewa "meke damunta?"

Zabura Hajja tayi tana salati dan ba karamin tsoro yabata ba, sam bataji motsinsa ba sai sautin managarsa taji.

Zarah kuwa juyawa tayi ruf da ciki tana mai k'ara sautin kukanta wanda baya fitowa sosai sabida da dushewar da voice d'inta yayi.

"Amma dai Ahmadu ka iya shegantaka, kashigo wuri sululu kamar maciji, gaskiya kasanja d'abi'a wannan kam ba tadan arziki ba ne."

"Am sorry Hajja, nayi sallama badai kuji ba ne."

"Oh, to ya akayi?, wani abin kake da buk'ata?"

"A'a bana buk'atar komi, nadaizo duba lafiyar tane, sai kuma nasamu kamar batajin dad'i ko?"

"Uhmm ai uwar masu gida kafiya take dashi Ahmadu, kaganta nan tak'i cin komi, daidai da ruwa tak'i sha, sai kuka takeyi kamar ance Umaru ne yarasu, gashi nan hakan ya haifar mata da zazzab'i mai zafi wanda yasa jikinta d'aukan zafi har ya hana mata barci, shinefa nake rage mata zafin jikin ko ta sami barci."

Kallon bayan ta yayi sai kuma ya mik'e yafice da sauri.

Yana fita ta juyo hannayenta kare da Boob's d'inta ta tashi zaune "Hajja mik'omin rigata dan Allah."

Mik'o mata tayi ta zira tare da mik'ewa jiri na d'ibanta ta nufi bedroom, Hajja na biye da ita tana  mata fad'an yakamata tarage wannan taurin kan nata tun kafin ya kaita ya baro.

Koda ya dawo bai gansu a parlor ba sai kawai yanufi bedroom d'in da yasan suna ciki.

Har barci yasoma d'aukanta, ta cinkayi muryansa yana sanar da Hajja allura zaiyi mata.

Azabure ta mik'e tsaye zata gudu toilet ya damk'ota yarik'e gam.

"Yimata asannu dai Ahmadu".

"Tam, Hajja bamu ruwan zafi d'an daidai tasha kafin ayi alluran."

"Lallai hakan yafi, bari in had'o mata yanzu". Hajja ta amsa tare da ficewa.

"Nace bana so!!,  kabarni inmutu kowa ya huta tunda antsaneni ba'ason farin cikina." Cikin dusasshiyar murya take zubamishi masifa tare da buren kufcewa daga rik'on da yayi mata.

A k'irjinsa ya jefata ya matse gam, bugun zuciyoyinsu su had'u wuri 1, sai ya haifar masu da shiga wani yanayi mai wuyar fasaaruwa. 

Cike da tsoro ta d'ago da kanta ta kalli fuskansa, ya watsa mata wani mugun kallo, da sauri ta tura fuskanta cikin k'irjinsa tana cigaba da shashshekan kuka, yarrr yarrr yarik'aji sautin kukan nata na haifarmasa cikin jininsa, sai yasami kansa da sake k'amk'ameta yana fizgan numfashi da k'yar.

Ita kam tsoronsa ne yayi mata diran mikiya, gashi dai ya matseta da kyau har tanajin zafi amma ta kasa motsin kirki balle ta k'wace jikinta.

Ahaka Hajja tashigo ta samesu hannunta d'auke da cup wanda ta had'o tea.

RA'AYIDonde viven las historias. Descúbrelo ahora