*RA'AYI*
*16*
Hannunsa sanye cikin tafin hannunta yarik'e gam, tsira mata idanu yayi lokaci d'aya tayi fiyat dama gata ba aukin kirkiba.
Kwance take samar gadon marasa lafiya kamar gawa dan sai katsira mata idanu sosai zakaga motsin bugun zuciyarta.Numfashi ya sauke yana maijin matsanancin ciwon kai, tausayinta da k'aunarta duk sunbi sun kanainayeshi amma can k'asan ruhinsa wani abu mai mak'ak'i da mugun d'aci ke mintsilinsa wanda ba komai bane illah kishi tare da takaicin halin da ya risketa ciki da waninsa sukabi duk suka cunkushe masa har suka haifar masa da jin wancan yanayin.
Istigfari yake ta tisawa cikin ransa, cikin amincin mamallakin komi da komai salama yasoma wanzuwa gareshi.
Murmushi yasaki danjin dad'in da Allah yanufeshi da zamowa cikin musulman bayinsa masu amsar k'ddara a duk yarda tazo masu.
"Alhamdulillah ala kulli halin, Alhumma iggifirli warhamni wa'afini warzuk'uni nafi'an." Ya furta hakan cikin dafe goshinsa tare da kife kansa cikin tafin hannunta wanda yake rik'e dashi.
Turo k'ofar akayi tare da sallama, ya d'ago akasalance ya amsa, murmushin k'arfin hali ya saukewa wacce tashigon.
Doctor Safina ce tashigo d'auke da file a hannunta, zama tayi samar kujerar dake kallonsa.
"Ya mai jikin tak'araji doctor?" Tace dashi tana mai d'ora hannunta inda saitin heart d'in Zarah yake, danjin ya bugun numfashin nata yake."Alhamdulillah, sannunku fa da k'ok'ari, nagode Allah saka da alkhairi." Ya amsa mata murya a shak'e.
"No babu komi doctor, ai yiwa wani yiwa kai ne."
Jinjina kai yayi d'auke da murmushin yabawa.
"Am Doctor ga saka makon tests d'innan da kasa ayi mata sai ka duba kagani." Tana mai mik'a masa file d'in da tashigo dashi.
Amsa yayi ya soma bud'ewa akasalance, dan bak'aramin bugu zuciyarsa takeyi ba na fargaban kada yayi arba da akasin khairan.
"Duk da dai babu wani lalura da yasanya mata hasalima ta baya yayi rapping nata ko shima bai samu damar jimawa ajikin nataba sosai ba balle har yayi realise, jinin da yayi ta zuba mata kuwa ciwon da yaji mata ne yayin shigarsa da k'arfi da kuma period datake cikinsa, to firgici da d'imauta ya haifar da rushing na blood d'in haka har hankula suka tashi." Ta dakata tare da jan numfashi ta d'ora "Munyi treatment d'in wurin da yarda yakamata dan haka ka kwantar da hankalinka da zarar ta tashi zata dawo normal, sai dai d'an abinda ba'arasaba, shima dangin kuzari jiki ne, Allah ya k'ara tsare gaba." Tak'arasa da addu'a.
"Amin ya Rabbi." Ya amsa hankalinsa nakan file.
D'agowa yayi tare da sauke ajiyar heart mai sauti wanda har sai da Dr. Safina ta dubeshi cikin gaggawa.
Murmushi ya sakar mata, tamaida mishi da martani.
"Allah mungode maka da ka tsare mana baiwarka daga fad'awa lalura mai wuyar magani."
"Lallai kam Allah shine abin godiya dan na tabbatar wannan tantirin mutumin baza'a rasashi da cuta ba."
"Uhmm Allah dai ya kyauta, Yakuma tsare dukkan al'umman musulmai daga sharrin iblisai dangin shaid'an."
"Amin Dr. AA."
Shiru ya ratsa wurin zuwa can ya dubi Dr. Safina wacce take dad'a duba jikin Zarah da abin awo.
"Yanzu shi wawan yana ina?" Ya furta cikin takaici.
"Doctor Hameed ya tabbatarmin da farfad'owarshi amma fa lallai yana cikin mawuyacin hali dan yace da wuya in idanunsa d'aya bai lalace ba sabida har yanzu jinin dake fitowa cikinsa yak'i d'aukewa."
"Alhamdulillah, Allah yasama ya mutu ko arage mugun iri."
Kallonsa kawai Dr. Safina tayi batare da ta kuma cewa komi ba ta mik'e tana mai duba yarda trip d'in ke moving, ta nufi hanyar fita tana cewa "Anjima kafin inwuce gida zan dawo dan yi mata allura."
"Ok, ya amsa tare da mik'ewa ya gyaramata kwanciya ta yarda bazata gaji ba.
Yana zaune samar sallaya yana jan tasbaha bayan idar da Sallar isha'i da yayi, ya tsinkayi sallama.
Musbah ne ya shigo tare da su Abba, Modibbo tare da Hajja.Umma da su Zubaida Hajja tahanasu zuwa sai in Allah yakaimu gobe lafiya sai suzo dan yanzu dare yayi cewar Hajja dan ita tayi ruwa da tsaki kan lamarin.
Tayi mugun basu tausayi ganin yarda numfashinta ke sauka kamar babu shi.
"Ahmadu wai mitayi ma yaron nan da zafine haka da ya zab'i wulak'anta mata rayuwa ta muguwar hanya?" Modibbo kenan yake tambayar Ahmad sanda yagama yi masu bayanin abinda bincike ya nuna.
"Batayi masa komai ba kawai iskanci ne irin na kayan Allah shirya." Yaboye hak'ik'anin abinda Musbah yasanar dashi cewa sanadin marin datayiwa Jimie ne yayi sanadiyyar komi dan in har ya fad'a to dole labarin fitarta zuwa club zai fito kuma fitowar zaizama wani sabon tashin hankali agareta dama su wad'anda basu san tayi rayuwarba.
"To Allah yasaka mata cikin gaggawa."
"Amin." suka amsa atare.
Addu'o'i kam tashasu har ta gode Allah dan kowa dake wurin saida ya tofa mata kalan tashi addu'ar sannan suka tafi cike da jimamin halinda take ciki.
Hajja tare da Ahmad suka kwana wurinta, dan bayarda Abban Zarah baiyi dashi ba ya biyosu yasami hutu amma yak'i, kan dole suka barshi da Hajja.
Kwanarta biyu aka sallameta, duk takoma wata silent kullum cikin kuka, fatar idanunta duk a kunbure, aniyi rarrashin har an zuba mata na mujiya.
Tarairaya kam da kulawa tarasa wa zatace yafi batashi tun daga kan Hajja har zuwa su Abba, su Umma, Aunty Zainab, yayunta da su Zeenat hatta da k'awarta Hafsat ba'abarta abaya ba da iyayenta, balle kuma azo kan Modibbo wanda musanman yake takowa har side d'in Ummien Ahmad ya dubota dan a can take zaune, duk dan a k'ok'arinsu naganin tadawo real Zarahnta nada mai karsashi da walwala.

KAMU SEDANG MEMBACA
RA'AYI
Romansa"Mitchew!!" taja tsaki "Meke damuna ne ni ZARAH?' Ya Allah ka kawomin dauki alfarmar Annabin farko da k'arshe Amin.