*RA'AYI*
'''Na Safiyya.'''*17*
Duk wannan kulawar da suke bata bai hana mata jin k'unciba, duk inta tuna basik'in nan Jimie yaga tsiraicinta har yashiga jikinta, kuka take shak'a ma'ishi, Ummie tayi ta bata baki tare da nuna mata hakan rubutaccen al'amari ne, indeed it's your DESTINY, it was written already and nobody can stop ur faith zarah, believe in Allah alone nobody can escaped from his/her destiny, so be thankful to Allah. Allah loves you and he is the one that can protect you from being harm. Ke musulma ce ki yarda da alkhairin sa da sharrin sa kamar yanda yazo mana acikin Tauhidi kuma kaddara abuce wanda baza ki tab'a iya kauce masa ba.
Kuka takeyi mara sauti dan bata son Ummie tajiyota, cikin shashsheka tasoma maganar "Dama ace k'addaran zuwa club bai faru dani ba, da bazan had'u da wannan tantirin ba, da bazan mareshi ba balle ya k'ullaceni har yayimin wannan wulak'ancin." Sai ta kuma sakin kuka tare da toshe bakinta da bargo dan hanawa saitin kukan fitowa.
Dafa bayan ta akayi yasa ta juyo da sauri.
Zulfa'a ce tsaye tana kuka da hanzari Zarah ta yanyota jikinta ta rungume cikin rawar murya take tambayarta."Zulfa waye yarasu, ba dai Modibbo ba?"
Cikin kuka ta amsa "Bawanda yarasu, nazo ne in rok'i gafararki akan abubuwan dasukayi ta faruwa dake."
Raba jikinsu tayi ta koma samar Cushing dake room d'in ta zauna tana mai k'arewa Zulfa'an kallo up to toes.
"Ban fahimceki ba Sis." Ta furta hakan cike da mamaki.
Cikin sanyi Zulfa'a ta matso ta zaune gefen Zarahn tare da kama hannunta ta sark'e da nata, tayi k'asa da murya yarda Zarahn kawai zata iya jin abinda zata fad'a.
" 'Yar uwata Zarah ki gafarceni, akan duk abinda yayi ta samun ki a rayuwa, kama daga yawan club, had'uwarki da Zainul har zuwa wannann bak'in lamarin da yasameki."
Tayi shiru kanta sunkuye."Uhmm inajinki 'Yar uwa, mekikeson sanar da ni?"
Shiruta tayi tak'i cewa komi, sai hawaye take sharewa wanda suke ta zubo mata kamar an bud'e tap.
"Zulfa'a ko kinason sanar dani cewa kece wacce tayimin asirin danayi ta zuwa club, kece kika turo Zainul cikin rayuwa ta, kece kika had'a plan d'in da yaran Jimie suka saceni zuwa wurin sa?"
Cike da tarin nadama ta d'ago kanta ta dubi Zarah, dakyar ta iya amsawa "Duk nice sanadinsu Sis, nasan ban kyauta miki ba dan Allah kiyafemin, nayi nadama mara iyaka, nayi danasan bin sharrin zuciya alhalin nasa ita d'in mugunyar nama ce, forgive me my blood sis."
Idanu waje cike da tsoro game da mamaki Zarah ke dubanta, tama rasa bakin magana, cikin tarin mamaki take nuna Zulfa'a da finger.
"Me natare miki? me nayi miki da zafi haka?, me su Abba sukayimin batare da ke ba?' Me Hajja, Modibbo, su Umma, Aunty Zainab dasu yaya sukayimin batare da ke ba?, tell me wani banbancin ake nuna miki tsakanina da ke da har yake bak'antamiki rai da kika d'auki wannan muguwar hanyar dan ki musgunamin?"
"Babu ko d'aya ciki Sis, sharrin zuciyane da bin kid'in gangan shaid'an duk yajamin amma ina rok'on garafarki ko nasami sauk'in k'unar da zuciyata keyimin tun faruwar abin."
;Me nayiwa wannan baiwar Allah ne, yasa tun tasowarmu bama zama inuwa d'aya kamar masu ganin hanjin juna;
"Dan soyayyarki da Manzon tsira (S.A.W) ki yafemin, ki kuma rufamin asiri maganar ta tsaya tsakaninmu kamar yarda kika saba dan girman Allah."
Magiyar Zulfa'a yadawo da ita tunanin da ta fad'a.
Share hawayen dake bin cheeks nata tayi, ta dubi Zulfa'a sai tacije lips.

YOU ARE READING
RA'AYI
Romance"Mitchew!!" taja tsaki "Meke damuna ne ni ZARAH?' Ya Allah ka kawomin dauki alfarmar Annabin farko da k'arshe Amin.