05

1.1K 96 2
                                    

*RA'AYI*
'''Na Safiyya'''

*05*

Ran musbah ya yi mugun baci sanda ya farka yaga abinda Jimie ya yi masa, ayanzu yafi kowa k'yamar wannan watsatstsiyar rayuwa da sukeyinsa, kansa kamar zai rabe biyu yakeji, haka nan ya tashi ya tsarkake jikinsa ya gabatar da sallolin da ake binsa, ya d'auki 'yan mintoci yana istigfari sannan ya shafa yana mai fatan samun yafiya wurin mai duka, had'a kayansa ya yi cikin trolley, ya bud'e wata drawer ya d'iba kud'i mai yawa, ya saba jakarsa yafice zuwa wani hotel da k'udirin yiwa garinsu tsinke gobe, cike kuma da fatan Allah yasa mahaifiyarsa tana raye.

*****
A sannu ta bud'e idanunta wanda sukayi mata nauyi, mik'a tayi bakinta d'auke da salati, muryan Abba taji a gefenta yana tayata salatin.

"Sannu Zarah'u".

" Yawwa Abba".

Ajiye k'aramar AL-QUR'ANIN dake rik'e hannunsa ya yi a gefe, ya dafata kanta, cikin taushin murya yace "Ina kikejin yana miki ciwo yanzu".

"Babu, jina dai nakeyi kamar an d'aukemin k'aton dutse a samar kai kuma k'irjina kamar an wankemin shi numfashina ya dawo normal kamar da can".

"Alhamdulillah, Allah mungode maka, Allah ya k'ara tsareki tare dana 'yan uwanki".

" Amin Abba, amma meye ke faruwa da ni ne Abba?"

"Tashi ki d'auro alwala ki rama sallolin da ake binki, kinga har 2:30am kuma ko magrib bakiyi ba".

Da sauri ta kalli agogo, "To Abba in hanzarta dan inajin ko la'asar bansamu nayiba".

"Allah ya kyau, insha Allah k'arshen wasa da ibadarki yazo".

Sai da ta gasa jikinta da ruwa mai zafi, ta d'auro alwala ta fito ta soma rankan sallalolin tare da istigfari a dukkan nin sujjadar datayi dan neman gafarar Ubangiji.

Koda ta idar zama tayi a wurin tana lailalah da babban fingers d'inta.

Motsin shigowa taji yasa ta d'an juyo, Umma Amarya ce da Abba suka shigo, Shafa addu'ar tayi ta fuskancesu.

"Sannu Adon mata". Umman A tace da ita.

" Yawwa Ummata". Jin tayi sannan tace "Amma meye ke cikin farin ruwan nan da kika bani?, dan tunda na shashi naji jikina yana rawa daganan ban san me yafaru ba sai dai na farka najini kamar an sanjamin komi na jikina, kuzarina, natsuwar ruhina duk sun dawo karmar da".

"Masha Allah, hakan shi ne burinmu da fatarmu,  hak'ik'a farin cikinmu bazai misaltuba a yau, Allah mungode maka daka dawo mana da d'iyarmu cikin natsuwarta, Allah ka k'ara tsare mana ita".

"Amin ya Rabbi". Abba ya amsa.

" Zarah'u" Abba ya kira sunanta.

"Na'am Abba".

Gyara zama ya yi tare da kama hannunta yasoma magana "Hakika nasha mamaki sanda Ummanku tazomin da labarin wai yawon bin club kikeyi kamar yarda itama Ahmad yasanar da ita".

Shiru Abban yayi yak'i cigaba da maganar dan yarda yakejin d'acin lamarin cikin ransa.

Hakan ya haifar mata da k'arin fad'uwar gaba akan wanda take ciki tun sanda taji kalmar Club yafito abakinsa.

"Haka Allah ya tsaro miki cikin rayuwarki, wanda shine ake kira da incredible, k'addararren al'amari wanda Allah ya wanzar da samuwarshi tun fil'azal, dan haka ina rok'onsa Allah yasa anzo k'arshensa kenan".

" Amin". suka amsa ita da Umman.

"Please pardon me Abba and Umma". Tace cikin shashshekan kuka.

Rungumeta Umman tayi tana taping mata baya, sun dad'e ahaka Umma tace "Ai yawuce dan mun san bayin kanki bane".

"Nagode, Umma sanar dani abinda nake cikin wasi wasinsa".

RA'AYIDonde viven las historias. Descúbrelo ahora