20

1.2K 85 3
                                    

*RA'AYI*

*20*

Jin kukanta yake kamar ana d'iga masa ruwan dalma a heart, yanajin yarda sound d'in kukan nata kefita har da ciccira, rintse eyes nasa yayi tare da dafe saitin zuciyarsa, baijin zai iya yi mata magana ba ayarda yakejin kansa, dan haka ya k'yaleta tayi mai isarta sannan tayi shiru tana ta jera ajiyar zuciya.

Jin ta daina kukan ya d'ago ya goge face d'insa  da tissue wanda yajik'e da gumi, reverse yayi suka koma cikin gari.

Tafiya sukeyi kamar kurame, dan ko kallo bata isheshi ba ita kuma tacika fam ganin halin ko in kukan da yanuna mata,  ta janyo tissue ta goge face d'inta, ta maida kanta gefe d'aya tana mai jinnawa miskilancinsa.

Abakin wani mall yayi parking ya fito ya kulleta ya shiga ciki bai jimaba yafito rik'e da leda mai dan girma, bayan ya zauna ya d'an kalleta fuska a had'e ya cilla mara ledar samar cinyarta batare da yayi mata magana ba ya tada motar ya hau kwalta, da kallo take binsa cike da tarin masifa amma sai da sami kanta da kasa sauke masa kwandon fitinar datayi niyya sakamakon hango face d'insa da tayi kamar anyi gobara, komawa tayi ta lafe a seat ta d'aga kanta sama idanunta lumshe kamar mai barci.

A harabar hospital nasu yayi parking ya kashe motar ya juyo da dubansa site nata, tsira mata idanu yayi, face d'in ta har ya tasa musanman inda tasha mari haka samar fatan idanunta suma sun tasa amma duk da haka tayi masa kyau, lumshe idanunsa yayi ya cije lips sai kuma yasaki murmushi tare da tura yatsunta cikin sumar kansa, ahankali ya furta "Mai kyau ako yaya yake mai kyau ne shi."

Tar ta bud'e eyes nata dan dama duk abinda yakeyi tana kallonsa kawai pretending tayi makar mai barci.

Harara ya watsa mata ya d'aure fuska kamar bashine yanzu yagama murmushi ba, itama had'e rai tayi, ta tura baki gaba.

Ba zato taji saukan nock akanta ta dafe wurin idanunta ya kawo ruwa ya murd'e mata kunni da k'arfi ta saki ihu ya bige bakin ta rufe bakinta da hannayenta tana mai zuba mishi manyan idanunta wanda suke zubda hawaye.

A dak'ile yace "Sutirta jikinki ki fito muje, dan bazan iya fita dake acikin irin wannan shigarba." Yana mai nuna mata ledar dake samar cinyarta.

Ba musu ta bud'e ledar doguwar rigace lemon colour mai adon duwatsu  k'anana golden sai d'aukan idanu sukeyi, ta sanya tare da yane kanta da gyalensa.

Yana gaba tana biye dashi, duk inda suka wuce sai taji ana gaishe dashi cikin girmamawa har itama ta sami nata rabon gaisuwar.

Suna shiga office d'insa ya nuna mata wurin zama ta zauna a d'arare, tana k'arewa office d'in kallo kamar yaune shigowarta na farko.

Shiryawa yayi yafito a cikakken doctor nasa ya manna farin glass sai sirrin kyawunsa yafito.

Tunda yake shiryawa take binsa da kallo har ya kammala idanunta na kansa, sosai taga yau yafi mata kullum kyau.

Takowa yayi zuwa gabanta ya sunkuya numfashinsu na bugar juna, yayi k'asa da voice "Wannan kallon haka fa? Kardai ki cinyeni lokacina baiyi ba."

Wani matsanancin kunya taji ya diran mata na kamatan da yayi tana kallonsa.

Hannunta tasa ta tura k'irjinsa yayi baya ta mik'e da hanzari ta nufi k'ofar fita ya damk'e dantsenta fuskansa ba wasa ya maidata Cushing data taso.

"Kijirani har indawo dubo patients d'ina, bazan jimaba in Allah yaso."

Gyad'a masa kai tayi kanta a sunkuye dan sosai takejin kunyar had'a idanu dashi yanzu, murmushi yayi mai sauti "Mara kunyar k'arya." Ya furta gakan can k'asan mak'oshinsa.

Yana fita ta mik'e ta kama k'ugu "Kaine mara kunya ehe, kuma ni ba mayuwa bace da zakace kada nacinyeka sai kace kaid'in wani abin dad'i." Tak'arasa cikin murgud'a baki cike da tarin tsiwa.

RA'AYIWhere stories live. Discover now