Ra'ayi
Mrsjmoon.
*32*
"Munzo baka hak'uri ne akan abinda Rahila tayi maka." Ta furta kanta sunkuye.
Baice komi ba illah mikewa da yayi yasoma gyarawa Zarah kwanciya.
"Dan Allah dr. kayafe mata ko tasami sauk'in laluran datake fama dashi." Maman tace haka cikin zubar hawaye.
Cikin k'aushin murya ya amsa "Tuni na yafe mata, dan tunda nagane ita tayimin asiri ban rik'eta ba, sabida da na san son datakemin ne ya janyo hakan, ita aganinta in matata tagaza d'aukan laluran da ta assamin dole nazo wurin da zancen aure ko?, to ta makaro Allah ya yayemin lamarin cikin salamarsa."
Cike da kunya maman ta kuma cewa "Ayi mata hak'uri dr. Yarintane da wafta yake damunta gashi nan taje tajawoma kanta lalura mai wuyar magani."
"Nace ya wuce mama Allah kuma yabata lafiya."
"Amin." Lawisa ta amsa.
Shiru duk sukayi na wani lokaci zuwa can ya dubesu "Zaku iya tafiya hakan in kuma wani abu kuke nema ina saurarenku."
"Dr. Alfarma nake nema da ka auri 'yata ko Allah zaisa ta warke ganin tana tare da kai, sabida tana mut.....
"Aa!!!! Dakata haka nan mama!, ban aureta sadda take cikin hankalinta ba sai yanzu da tazama da ita da babu duk d'aya, banson sakejin wannan zancen banzan da wofi, please leave here in peace I beg you."
Ya nuna masu k'ofa.
"Dr. Kafi kowa sanin duk halin da ta fad'a kaine sila dan haka aurenta a duk yarda take shine tausayinka gareka, dubi da yarda take maka mahaukacin so, kodanshi ka tausaya mata ka zamo mijinta, natabbata zata sami lafiya intana tare cikin kulawarka."
Rintse idanunsa yayi, bayason yiwa matar tijara amma da alamu ita abinda takeso kenan.
"Mama wallahi Allah kenan to koda a duniya mun rage mu biyu ne rak bazan tab'a auren 'yarki ba, kuma kada kik'ara d'aukan alhakina nacewa nine sanadin haukacewar Rahila, ga qawarta nan ki tuhumeta sanadin haukanta amma bani ba, haka so da kike ikirarin tanayimin ba na Allah da manzon sa takeyimin ba nina sani, to dan Allah kubar nan wurin kada hayaniyarku yata sarmin da patient."
"Doctor....
"Mama get out!! Don't let me go upset, I don't want to hear a single word from you, just work out of my house.
Da sauri suka fice jin irin tsawar da yadaka masu wanda yayi sanadin farkawan Zarah.
Idanu ta zuba mishi, ya tako zuwa wurinta yana mai kauda fushin dake tattare dashi.
"My hero kai da suwaye haka nake tajin hayaniyar ku?"
"Oh forget it, sweetheart."
Lumshe idanunta tayi tare da shafo k'irjinta "I'm feeling tasty Yaya."
Kamata yayi ta tashi zaune ruwan yasoma bata sannan ya zubo mata ferfesun hanta yayi laushi sosai yasoma bata a hankali.
Mommy ce ta turo k'ofar d'auke da sallama bayarta Imam ne d'auke da kayan abinci.
Cike da girmamawa ya sunkuya ya gaisar da ita, ta amsa tare da tambayarsa mai jikin.
"Alhamdulillah." Ya amsa, sannan ya gaisar da Imam.
"Ke Ashe raguwace haka, kin kusa b'arar mana da baby ko?" Imam ne yake cewa da Zarah haka cikin zolaya.
Da kallo tabishi dan bata tab'a gaminsa cikin irin wannan yanayin ba na raha, mutumin da yake Ko da yaushe a d'aure kamar cow shine yanzu yake magana cikin wasa, wonders shall never end.

YOU ARE READING
RA'AYI
Romance"Mitchew!!" taja tsaki "Meke damuna ne ni ZARAH?' Ya Allah ka kawomin dauki alfarmar Annabin farko da k'arshe Amin.