3

13.4K 919 21
                                    

Haske writers association💡

Asma'u bilalu bulama shine asalin sunan mahaifiyarta asalinta 'yar qasar Nigeria ce ubanta bilalu dan Maiduguri sai mamarta ummu-rumana shuwah ce.

Bilalu bulama Nada tarin dukiya mai yawa hakama matarsa ummu-rumana kasancewarta tanada gadon iyayenta dasuka barmata.,
'Yarsu qwaya 'daya tak aduniya Nana asma'u wadda duk wata soyayyarsu da burinsu sun 'dorasa akanta.

Bilalu bulama Nada qanne biyu jabir bulama da salmanu bulama
Kowannensu matarsa 'daya da 'yaya uku uku banda bilalun dakeda 'ya daya,

Jabir babban dansa shine ishaq sai qannensa mata biyu hassana da husasaina,

Salmanu kuwa sunan babban dansa bulama sbd sunan mahaifinsu yaci sai qaninsa babaye da yakurah.

Kowannensu nada arziki daidai gwargwado amma ba kamarna bilalu ba sbd shi ba qaramin arziki Allah ya hore masa Wanda hakan yasa shedan yashiga kwadaitawa qannensa dukiyarsa nan kowannensu yafara qoqarin ganin ya cusa dansa gurin Neman 'yarsa Nana asma'u,

Tun kowanne natura babban 'dansa a 6oye gurin neman soyayyar asmaun hardai kowa yafito fili yanuna buqatarsa tason nemawa 'dansa auren,

Alhaji bilalu baiyi tunanin komaiba saima farin ciki dayayi saidai abun daga baya lalace sbd fada da tashin hankali daya shigo ciki sbd tuni kawuna suka rarrabe sbd alamarin ganin haka sai alhaji bilalu yace abari asma'u tazaba Wanda takeso acikin yaran dakanta sbd ya fahimci bulama shine Wanda tafiso kuma maganar gaskia yafi ishaq nutsuwa da tarbiya ga hankali amma shi bazai fadaba saidai ita asma'u tafada Wanda takeso dakanta.

Tashin farko da'a tambayeta gaban kowa ba 6oyo ta za6i bulama

Hakan datayi shiya qulla wata irin qiyayya da sabani tsakanin jabir da yayyunsa bilalu da salmanu.

Bayan auren da wata biyar aka wayi gari gidan alhaji bilalu ya qone qurmus dagashi har matarsa ummu rumana babu Wanda yafita kuma a iya binciken da akayi aka gano wutar dai kunnata akayi da man petrol.

Haka akayi zaman makoki aka watse dakyar aka samu asma'u ta dangana Wanda saida aka hada da adduoi da sauke al-qur'ani kafin tadawo daidai.

Duk inda hankalin alhaji jabir da ishaq yake yasake hargitsewa sbd sai yanxu kukaga wautarsu ta kashe su alhaji bilalu sbd yanxu duk tarin maqudan dukiyarsa yarsa zata gada tokuma ai mijinta da uban mijinta suzasu juya dukiyar kenandai alhaji salmanu yayi arzikinda ba ranar qarewarsa shikenan shi yatashi abanza.

Cikin watanni hudu shida ishaq sunkasa sukuni suna qulla yanda zasu qwato dukiyar su raba su salmanu da ita.

Ranarda suka gama qulla suka aika 6arayi gidan alhaji salmanu tsakiyar dare,

Gurin karbar takardun bulama da mahaifinsa sukai gardamar bayarwa Wanda yaja nan take aka harbe alhaji salmanu da matarsa bulama naganin haka ya buge babbansu da flower verse ya fizgo matarsa asma'u suka gudo tareda takardun dukiyar
Yakurah da babaye dama suna schools hostels suke zama.

Gudu suke sosai atsakiyar ko gani sosai basayi sbd duhun dare amma haka suke gudu hannunsa damqe Dana asma'u suna keta duk hanyarda suka samu sbd sunajinsu abayansu biye dasu.

Basu ankaraba suka gansu har sun fara barin anguwanni suna qoqarin ketawa daji amma haka suka cigaba da gudu agalabaice cikin tsananin wahala da gajiya
Can wajen gari sukaga wani kangon gida daya qone suka shige tareda boyewa.

Wani irin kuka asma'u tasaki jikinta na karkarwa
Bulama yayi saurin saka hannuwansa ya toshe mata baki sbd takun su ishaq da barayin daya jiyo yana kusantonsu.

Dudduba koina sukayi suna haskawa Allah yasa basu gansuba
Iska ishaq ya daka cikin zafi da tsananin 6acin rai yana huci yakira abbansa yafada masa

Cikin takaici da baqin ciki abban yace,

Kutafi tashoshin motar duk garinnan kudubasu banason kowannensu da rai takardun kawai nakeso Ku karbo saiku harbesu
Hakama atura su tiger duk wata station su zauna daga nesa da anhangosu sunzo station kafin sushiga aharbesu.

Aje wayar yay yakallesu yace kumuje tashoshin mota amma wasu su tsaya anan sbd nasan idanma sunanan kusa idan gari ya waye zasu fito idan sun fito Ku harbesu kawai.

Barin gurin sukayi sukuma su bulama najin haka koda gari ya waye sake lafewa sukayi sukaqi fitowa saida duhu yasakeyi suka fito cikin sanda suka fice tareda qarasa kutsawa cikin dajin suka fara gudu

Jini sosai qafafuwansu ke fitarwa sbd ko takalmi babu maishi acikinsu ga yunwa ga wahala da kishirwa amma hakanan suka cigaba da tafiya sbd komawarsu nada matuqar ha'dari yanxu.

Basu hadu da qauye ko dayaba har asuba tayi musu atsakiyar daji gashi tuni asma'u tafara riqe ciki tana murqususu cikin tsananin azaba ta durqushe agurin awahalce tace,

Bulama marata zan mutu.

Da sauri ya aje takardun ya durqusa ya tallafota jikinsa shima daqyar yake hade yawu sbd bakinsa daya bushe qyam ko yawu daqyar yake samun na hadiyewa a maqoshinsa ga wata irin rana mai tsananin azaba,

Ko tsuntsaye babu adajin sbd a bushe yake babu damshin ruwa ko kadan itatuwan dajinma duk abushe suke babu mai inuwa.

Jinin dayaga yanabiyo qafafuwantane yasa yayi saurin kallonta murya na rawar wahala yace,

Asma'u cikine dake dama bansaniba?
Innalillahi-wainnalaihirrajiun.

Ganin tana Neman fita hayyacinta yasa ya goyata tareda daukar takardun yacigava da tafiya daqyar shima sbd shima yafara daina gani daidai.

Ahaka rana takuma faduwa wani Daren yayi musu a tsakiyar jeji wannan karon kam ya tabbatarda wata duniyar suka fado sbd  kalar yanayin dajin ya sauya sosai
Tun yana gani har duhu yasake yi dare Yakuma tsalawa sosai cak ya tsaya tareda yanke jiki ya fadi asma'u dake bayansa ta fado da qarfi kafin ya bude idanu daqyar Dan taimakonta sai ganin yayi kamar tana gangarawa
Bude idanuwansa yayi awahalce da sauri saiyaga Ashe bakin cliff suke mai tsananin zurfi da ruwa masu tsananin yawa yana miqewa daqyar kafin yakamota idanuwansa suka rufe yasake yanke jiki yafadi tareda fadawa shima.

********
Ahankali ya bude idanuwansa dake gani dishi dishi harsuka bude daqyar suna kallon sama,
Lumshe idanuwan yasakeyi yabudesu yaga tabbas rufin sama bukkar karace yake ciki,

Qoqarin motsawa yakeyi Dan ya yunqura yatashi aka shigo bukkar yayi saurin dagowa.

Tashin namijine kamarsa dago fari tas sanyeda kayan saqi na fulani.

Qarasowa yayi da sauri tareda dafasa yana cewa,

Yi ahankali kana kariya aqafa.

Kallon qafar bulama yayi sai alokacin yaji azaba ya lura da 'dauri amma bai damuba cikin dasashiyar murya da fargabar amsarda za'abasa yace,

Ina matata?
Inane nan?
Ina takardun dake daure ajikina?
Kwana na nawa anan?

Cikeda mamaki da rashin isashiyar hausar fahimtar me bulaman ke fada yake kallonsa kafin ya gyara masa zaman qafar mai 'dori yace,

Kayi hkr sbd bansan mezan fada makaba amsa daya zan iya baka shine kwananka takwas anan sauran tambayar anjima idan mahaifina yadawo ya amsa maka.

Yana fadar haka ya fice
Saigashi yadawo da qwaryar magani da akushin wani irin abinci kamar tuwa kamar kunu ya zauna tareda miqawa bulama yace,

Gashi kaci saikasha magani.

Kallon abincin bulama yayi yaga shi kama ma abincin yayi masa da aman tuwon semo amma sbd yunwa da matsuwar jin inda matarsa take ya karba ya dauke numfashi ya shanye.

Ruwan magani ya miqa masa suma ya karba ba musu ya shanye.
#Mamuhgee

TARAYYAWhere stories live. Discover now