Haske writers association💡
Not edited.
Dagowa tayi takallesa tana qoqarin tsayarda hawayenta
Suna hada ido ya miqe tsaye ya nufi bedroom dinsa batareda yace qalaba ko waiwayenta.Kallon hannunta tayi dake radadi sosai tasaka 'dayan hannun ta share hawayenta ta miqe ahankali taja hular rigarta ta rufe kanta ta nufi qofa ta fice.
Tana saukowa ta tararda Carolina a palo tana qoqarin fara aikin gyaran gidan sbd su amah zasu school.
Kallonta Carolina tayi cikeda mamakin ganinta tana saukowa daga saman a wannan time din saidai kuma ba abinda yashafi aikinta bane sai kawai taci gaba da aikinta
Itama rumanah nauyin Carolina din taji yasa takasa yimata magana ta nufi dakinta tashige.Toilet tashige tayo alwala daqyar sbd ciwon hannunta tafito tayi sallah tana gamawa ta fito ta nufi kicin saidai duk yanda taso tayi aiki kasawa saidai takoma daki ta zauna ta qurawa hannun ido tana tuno yanda ciwon yasamu.
Lumshe ido tayi tuno kalamansa"""inada nauyi ne?"""
Sai a lokacin mamakin maganarsa yake shigarta
Tasake tuno qaqqarfan jikinsa saikuma tayi saurin lumshe idanuwa sbd kunyar ganinsa dataji saikuma taji sanyin qamshin turarensa yashiga hancinta tayi saurin bude ido taga babu kowa zuciyarta ta buga da qarfi.Mikewa tayi ta nufi jikin window ta tsaya
Wani sabon qamshinsa taji yashiga hancinta har zuciyarta ta rufe fararen idanuwanta ahankali tareda budesu takoma bakin gado tasake zaunawa har lokacin hancinta da idanuwanta sunkasa daina jiyo qamshinsa
Zuciyarta takasa sukuni
Rashin sukunin hakan yasata miqe tafito jiki asanyaye ta nufi kicin.Duk yanda taso yin aiki a kicin kasawa tayi sbd rashin nutsuwar datake ciki gashi hannun yafara kumbura saidai batajin zafin kamar yanda takejinta cikin rudu da rashin sanin abinda yake damunta.
Kallo Carolina tabitadashi ganin kamar tana cikin damuwa gakuma hannunta daya kumbura cikin tausayawa tace taje daki ta huta tana kwatanta mata da hannu.
Murmushi qarfin hali tayi zatayi magana doorbell yayi qara atare suka kalli agogo da Carolina sukaga qarfe bakwai da minti goma,
Wanke hannu Carolina tayi ta fito cikin din ta nufi qofa ta bude.
Dawowa tayi riqeda leda fara ta kalli rumanah tace taduba mata chips data zuba ta nufi sama.Knocking tayi ahankali saidai ba amsa hartagaji bail budeba harta aje saidai tadawo qasa dashi takalli rumanah tace magani ne batasaniba ko urgent yake buqatarsa gashi bata shiga bedroom dinsa ta miqawa rumanah tace ta taimaka mata taje gurin sultana tafada mata kozata kirasa awaya tasanar masa.
Qura mata ido rumanah tayi sbd sanin bata tada sultana idan tana bacci ataqaicema lokacinda take tashi bacci baiyiba saidai zuciyarta na fargaba da idan yana buqatar maganin ne a gaggauce.
Karbar maganin tayi ta fito palo ta nufi dakin sultana saidai kuma tasamu kanta da tsayawa cak sbd qila yana cikin wani haline yake jiran maganin.
Juyawa tayi ta nufi saman tana qoqarin danne faduwar gabanta harta isa ta shiga palon ta nufi qofar bedroom din tayi knocking.
Shiru ba amsa tasake yin knocking din still ba amsa
Kasa juyawa tayi ta rabe qofar dakin gabanta na tsananta faduwa hakama takasa tafiya sbd fargaba.Jin shiru sosai yasata qara kwankwasawa cikin nutsuwa tana qoqarin sake kwankwasawa aka bude dakin hakan yasa saura kadan ta fada masa tayi saurin daidaita tsayuwarta tareda sauke kanta qasa daqyar ta furta,
Ga saqo aka kawo.
Batareda yakalletaba ya karbi maganin cikin maqoshinsa yace,
Wait.