Marubucin gskia baya rubuta abu acikin labarinsa batareda yayi bincike ko tambaya ba yayiwa abin cikakken sani kusani marubuci ba jahili bane sbd wata tambayar ko comment din tamkar wanka da jirwayene akewa marubuci dan haka kusani ni bana rubuta abinda banida sani akansa.
Juyawa tayi tabasa baya zuciyarta na wani irin bugu sbd zafin maganar daya gama fada mata,
Kobai fadaba tasani yafi ganin girma da qimar suhailat sbd ko babu komai itace uwar 'yayansa kuma macen data girmama dukkanin abinda zaizo mata dashi saidai tasan itama baza'ace bata masa biyayyaba,,,,Rintse idanuwanta tayi zuciyarta na sake jiyo mata zafin abin,
Da kishiyarta yake gaya mata maganar bata masa biyayya...sabon ciwon hakan taji ta rintse ido da qarfi tareda girgiza kai ta juya ta nufi qofa tana qoqarin maida kukanta.Riqo hannunta yayi daidai lokacinda tazo wucesa ya dawo da ita gabansa yana kallon fuskarta data qi kallonsa saidai yanayinta ya nuna jin zafinsa ne cikin ranta.
Kujera ya nufa ya zaunar da ita ahankali kafin shima ya zauna tareda riqo hannunta cikin nutsuwa da kulawa yace,
Kina tunanin wannan itace mafita???
Kina tunanin a halinda muke ciki yanxune lokacinda yakamata mu ringa samun matsala akan abinda nake buqata nakuma baki umarni?....
Kina tunanin sbd kare mahaifina nakeson dakatar dake daga abinda kike shirin aikatawa???A musulince duk Wanda ya kashe a kashesa amma idan kashewar zata kawo kashe kashen bayin Allah da basujiba basu ganiba to an yarda abar Wanda yayi kisar sai ayi masa wani hukuncin kwatan kwacin zafin abinda ya aikata.
Kina tunanin sultan mahaifanki kawai ya kashe?
Sultan ya bada umarni ankashe mutanen da sukafi mahaifanki abin tausayi,
Ya maida yara qanana marayu babu adadi,
Ya saka mata zaman takaba babu adadi,
Duk kina tunanin yin kansa ne kokuma ra'ayin kansa ne???
Dana barki da tun a shrkaran jiyar kinzama abinda yafi sultan ha'dari dan kuwa da yanxu jinin mutanen da kika zubar yafara ta6a qwaqwalwarki...Kinga abinda mu bamu ganiba labari kawai mukeji na asalin abinda ya faru har aka samu karagar kuma kinsan duk wata masifa dake bibiyar masarauta nan har yau ankasa samun Wanda zaiyi amfani da tunani da baairarsa domin kawo sauyi domin kuwa tun farko kisar cin amana ce ta samarda karagar kuma har yanxu kisar ce akeyi kina tunanin hakan shine mafita da sauyi tareda jin qan da talakawan qasar ke buqata bayan sune ake kashewa wainda basujiba basu ganiba.,
Kinason yankewa sultan hukuncin kisa bawai dan fadar musulunci ba saidan daukar fansar kisar iyayenka Wanda hukuncinki kwata kwata baiyiba a musulunce sbd kai tsaye fansa ne kika dauka,,
Kafin sultan anyi kashe kashe da dama wainda ma sukafi nasa dan haka...Ina sonki bazan iya bari kibi hanyar da sauran sukabiba,
Bazan iya bari rayuwarmu ta lalace ba sbd rayuwata zata lalace ne daga lokacinda taki ta lalace dan haka bazan iya bariba,
mahaifina tun tuni naso na kubutardashi daga hakan amma yayi aiki da qarfinsa na zama mahaifi agareni ya nesantani da kansa dan haka bazan sake aikata wannan kuskuren ba sbd ke din ikona ce.