4

13K 984 33
                                    

Haske writers association💡

Jingina jikinsa yayi jikin darnin ginin qasar dakin da kusan rabin ginin karane ya dafe goshinsa ahankali tareda rufe ido yana zuciyarsa na tsananta fargabar kar asanardashi ba'aga matarsaba kokuma ta rasu.

Qurawa qofar shigowa ido yayi yana sake tabbatarwa da kansa tabbas wata qasar suka fado sbd yanayin shigar Wanda yafita dazu da yanayin abincinsu da maganarsa tareda yanayin muhallin.

Ya jima yana tanane tunanen fargaba da rashin sukuni kafin wani dattijo sosai daya manyanta ya shigo dakin da gwararriyar sallamarsa.

Saurin 'dogowa daga jinginar yayi yatashi zaune daidai duk da rashin qarfin jikin dake tattareda dashi tareda zubawa mutumin ido Dan amatse yake dason jin ina matarsa take.

Kallon bulama dattijon yayi kafin yajuyo yakalli 'dansa dake bayansa cikin wani yare yayi masa magana kafin cikin hausarsu da bata fita yace,

Dama yatashi baka fadaminba kutti ?

Bai dadeba da tashi baabah magani natsaya bashi kafin naje kiranka saigashi kadawo.

Kallon bulama baaban yayi yace,

Sannu da kaji,yanzudai babu inda yakema ciwo ko?

Cikin qarfin hali yace,

Banajin komai yanxu qafardaice idan na motsata da 'Dan zafi,
Nagode sosai baabah amma Dan Allah ina asma'u mata.....

Kwnatarda hankalinka matarka nanan tareda kai saidai itama tayi jinya ta rasa cikin jikinta amma ta warke sosai.

Ajiyar zuciya yasake a6oye sbd ba qaramin dauke numfashi yayiba Dan gudun jin muguwar amsa.

Kutti ne yasake shigowa dakin wannan karon Asma'u na bayansa bakinta daukeda siririyar sallama.

Qura mata ido yayi sanye takeda kayan saqi irin nasu da wani juyayyen 'dankwali dako kanta bai rufe dukaba tayi wani irin mummunan baqi ta rame gabaki 'daya kamanninta sun fara sauyawa
Wani irin tausayinta Dana kansa ya rufeshi amma dai tunda sun tsira kuma suna cikin qoshin lafiya daidai gwargwado to alhmdllh.

Cikin sanyin jiki ta durqusa qasa tace,

Ina wuni baabah.

Lafiya lafiya mai sunan innejo mijinki ya farka daga yanxu kar asake kuka Dan ba'a kuka agidan baabah namiki uzirine kema.

Duqar dakai tayi cikin sanyi ta 'daga kai sbd akwanakin datayi agidan taga dokoki da sabbin alamuran rayuwa a gidan da mutanen garin wanda cikin qanqanin lokaci ta fahimci tsantsar jahilci da rashin wadataccen ilimin addini suke ciki Dan acikin duhu suke sosai.

Fita baabah yayi kutti yabi bayansa ta 'dago kai ahankali takallesa sai kawai tasaki qaramin kuka ahankali tareda toshe bakinta.

Hannu yamiqa yajawota kusadashi ya rungumeta shima daurewa kawai yayi amma yasan gararin rayuwa yasamesu.

Rarrashinta yayi daqyar yana cewa,

Asma'u kiyi hkr insha Allah komai zai daidaita Dana sake warwarewa zamu koma gida mu fuskanci su......

Kallonsa tayi amatuqar razane tana girgiza kai tace,

Yaya Dan Allah mubar maganar komawa yanxu kwata kwata nan inda muke wani yankine dabashida suna acikin wani lungun daji mai nisa daya ruwa masu yawa ya raba tsakaninsu da Nigeria dakuma wasu qasashen,

Sunada kwanciyar hankali duk da suna cikin tsananin duhun ilimi da rayuwa,
Jin dadi ba komai bane idan ga kwanciyar hankali da Wanda kakeso,

Bamuda uwaye ko 'daya duk ankashesu su yakurah komawarmu yanxu zamu saka rayuwarsu acikin hadarine suma,
Mu gwada bawa rayuwa wani chance anan sbd kwanciyar hankali da nutsuwa,
Mubari gaba idan komai ya Dade da shidewa saimuje da zuriar da Allah zaibamu anan cikin kwanciyar hankali.

TARAYYATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang