Haske writers association
Not edited.
*Asalin Labarin mineelik*Soyayya da cin Amana haɗi da Yaudara suka, kafa daular, asalin masifar ya fara ne, daga ranar laraba ga watan maris 1836. Mafarin rigimar daga mutane huɗune, jigogin masarautar, Musaman Sultan Jamal wanda shi ya haifar da kome....
Tafiya suke a gajiye ga dare ya fara rabawa, yunwa da kishirwa ya addabesu, dan haka suka yanke hukuncin da zaran sun sami, wani guri a can gaba zasu yada zango kasancewa sun fito daga yanki sham, fatauci duk cikinsu babu wanda yake iya magana sai Jamal, sabida Allah yayoshi mutune magananne, da kuma son raha,
"Kayyasa! Ajani karda ka gaji da tafiyar dan naga kaman rakuminka ke janka ba kai kejanshi ba.""Wai shin Jamal baka gajiya da magane, haba tun da muka fito kaiɗai ke surutu gaskiya kacika surutu kayi mana hakuri haka dan yunwa muke ji." inji Kojo.
"Shi kenan kojo nayi shiru kuma bazan sake magana ba, amma kusan matuƙar muka ce zamu shiga Ehtophiea a wannan daren akwai damuwa mu yada zango anan gaba."
Shirun da sukayi ya tabbatar da amincewar sauran.
Tafiya sukayi sosai har suka isa dajin kurfa, wanda yake cike da ababen tsoratarwa, ɗan tafiya kaɗan sukayi ɗayansu amari yaga wani irin Haske mai tsananin kyalli cikin duhu ya ware ido sosai yasake kallawa domin kuwa ya tabbatarda mage yake gani mai shegen hasken nan kamarna zinari cikin zaquwa da fargaba yace.
"Ku dakata naga wani abu, kamar Zinari."
"Amari nima nagani tsoron siffar abin yasani shiru gashi can kamar mage ko?" Inji Jamal,Linzamin rakumarsu suka ja, suka tsaya Jamal da Amari suka sauka, daga bisa rakumansu, Ajani da Koja suna tsaye suna kallonsu, tafiya sukayi me ɗan nisa suna niman Zinarin basu ganshi ba,
Tsaki Ajani yayi wanda ya kasance shine babbansu, cikin fushi yace.
"Dalla kuzo mutafi kusan inda muke ciki wannan dajin kurfa cike yake da al'ajabi da ban tsoro matumar kuka ce zaku bi na gane gane mutuwa zamuyi ku fito muje."
Murmushi Amari yayi cikin nutsuwa yace.
"Na rantse da abin bautana bazan bar dajin ba, Jamal idan zaka bisu ba damuwa amma ni sai naga abinda ya turewa buzu naɗi"Shiru sukayi sunsan Amari da kafiya da kuma taurin rai, matukar yace zai yi abu ba makawa sai ya aikata,
Cikin laluma kojo yace.
"Shikenan zamu tayaku nima! Ai duk cigabanmu ne, Ajani kayi hakuri mu tayasu niman zinariyar."Tsaki Ajani yayi sannan ya koma inda suka ajiye rakumansu, suka kafa tanti karan dake wajen dajin suka tsinta, suka kunna wuta suna shan ɗumi,( bawai dan lokacin sanyi ba'a mutanen da suka kuna wuta su zauna suna hira, musaman fatake matafiy idan suka yada zango.)
Zama sukayi a gurin, sannan suka ciro guzirinsu suka fara ci, bushashiyar gasashiyar fulawa sai bushashen inabi, sai ruwa suna ci suna hira, har dare ya raba sannan kowa ya koma tantinsa.
Kasancewa dajin mugun gurine koda suka shiga sai da suka kafe ilahirin gurin dan kar wani mugun dawa ya iya shigowa ya cutar dasu.
Asalinsu wadanan, Fataken yan garin Ethiopia ne, sun kasance marayu basu da uba basu da Uwa, sai wani marikinsu wanda shima bai jima da mutuwa ba.
Ajani shine babba a cikinsu sai mai binshi Kojo, sai kuma Amari da karamunsu jamal.
Dukda kasancewarsu marayu haka bai hanasu kaunar junansu ba, dan ko ciwo ɗaya keyi duk sai sun kwanta kamar marasa lafiya, dukda haka suna da mabanbanta halaya, Ajani baida yawan magana, amna kwai saurin fusata sai amma haka bai sashi ya gaza zama mai hakuri ba,Sai Kojo, mutune mai matukar fahimta ga daɗin zama da kowa kuma duk inda zai zauna zai matukar wuya kaji ance ana rigima dashi, sabida ya iya zama da kowa, sai Amari, masifaffe mara hakuri amma kome zaiyi akan gaskiyarshi yake, yana da matukar taurin kai, dan shi duk abinda yasaka agaba toh sai yaga bayanshi, amma mutune mai me tsage gaskiya.
![](https://img.wattpad.com/cover/173119568-288-k389906.jpg)