43

11.6K 965 19
                                    

Haske writers association

Not edited.
Murmushin qarfin hali tasaki tareda sake damqe hannunsa dake cikin nata tana kallon fuskarsa dashima ita yake kallo yana yiwa Allah hamdala cikin ransa.

Tashi zaune takeson yi ganin kamar batada qarfin jiki yasashi tayarda ita zaune tareda cire mata cannula dake hannunta ya gyara mata zama sosai.

Cikin sanyin murya da kulawa yace,

Ya kikeji yanxu?

Girgiza masa kai tayi tana kallon fuskarsa.

Jakadiya ce tayi knocking qofar dakin ahankali ta sanarda zuwan sultana.

Zare hannunta tayi cikin nasa tareda lumshe ido sbd yanayin datakeji ajikinta har lokacin.

Cikin nutsuwa ammyn tashigo idonta kan rumanah din
Hankalinta ya'dan kwanta ganin ta farka harta tashi zaune.

Qarasowa tayi tareda miqawa maheer hannu ya kama hannun da hannunsa daya cikin nutsuwa yace,

Ina kwana ya ammy?

Murmushi tayi tace,

Lfy klau..tana kamo hannun rumanah tace,

Ya jikin?

Naji sauqi ammy"""ta fada cikin qarfin hali da danne ciwon datakeji.

Miqewa yayi ya fita yana amsa kiran khaleefa dake kiransa kan maganar test result 'dinta dasuka fito.

Ammy dakanta ta kamata takaita toilet tayo wanka da brush tana fitowa taga doguwar riga mara nauyi akan dressing chair ta dauka tasaka ta shirya tana qoqarin busar da kanta sbd wankan tsarkin datayi na haihuwa ammy tashigo tareda nuratu dake daukeda babban tray Jere da breakfast ta ajiye zata juya rumanah takira sunanta ahankali.

Tsayawa tayi tareda juyowa cikin ladabi
Rumanah ta miqa mata hand dryer cikin sanyin murya tace,

Taimakamin.

Ammy na ganin hakan tasan magana zasuyi ta kalli nuratu tace,

Tayi breakfast.

Jinjina kai tayi alamar tou.

Ahankali take busar mata da gashin babu Wanda yayi magana acikinsu.

Tana gamawa ta daure mata gashin tareda ajiyewa a natse.

Miqewa tayi itama ta nufi inda take sallah tana idarwa ta dawo kan couch din dakin ta zauna har lokacin nuratu na tsaye kanta a sunkuye cikin tarin damuwa da kadaici.

Ahankali takamo hannunta ta zaunar da ita kusada ita ta kalli fuskarta kafin ta sauke kanta itama ta qurawa gabanta  ido cikin sanyin murya tace,

Kiyi hakuri nabarki alokacinda kike tsananin buqatata,
Kin kuladani kin tayani kuka kin rarrasheni alokacinda na rasa nawa iyayen saidai ni nakasa miki hakan alokacinda kike buqatar wani ataredake..

Kallonta nuratu tayi hawayen datake riqewa suka gangaro mata tace,

Wlh idan nace miki bana buqatarki ataredani na miki qarya rumanah saidai yanayin rayuwa daya kawo bambamci arayuwarmu ayanxu rayuwarki daban take data baiwar datafi kowace baiwa baqin jini sbd mahaifiyarta data.....

Rintse ido tayi tareda budewa idanuwanta na cikowa da hawaye ta juyo ta kalleta cikin sanyin murya tace,

Ada damuke bayi rayuwarmu tafi kwanciyar hankali da nutsuwa tareda dadin gudanar da rayuwarmu,
Rayuwar bayi wata rayuwace mara yanci amma wlh wani lokacin tafi rayuwa irin wadda nasamu kaina aciki,

Nuratu idan zaka roqi Allah abu ka roqi alkhairinsa sbd wlh rayuwata ina baiwa tafimin kwanciyar hankali akan yanxu.

Gangaro mata hawaye sukayi sbd jin tausayin kanta da abinda zata fada tace,

TARAYYAWhere stories live. Discover now