25

12.9K 1.2K 236
                                    

Haske writers association

Not edited
Zama tayi tareda rafka tagumi cikin zullumi da rashin sanin madafar tunaninta
Abu 'daya tasani shine tana tsananin qaunar rumanah kamar itace ta haife musamman a yanxu datake hango soyayyarta mai tsanani a idanuwan Maheer 'dinta saidai duk wannan qaunar da yardar zata rushe tazama qiyayya da tsana mai tsanani idan sirrin rasuwarsu asma'u da bulama ya bayyana ga rumanah abinda bazatasoba kenan.

Qarfe goma da mintuna goma sha biyu suka farka yatashi zaune tareda tayarda ita zaune yana gyara mata gashinta daya barbaje.

Kallonsa tayi tareda sakin kasalallen murmushi
Ya shafi gefen fuskarta tareda bude baki yace,

Yaya?

Lumshe ido tayi cikin laushin murya tace,

Yayi sauki yanxu banajin ciwon kan.

Lumshe ido yayi tareda jinjina kai kafin yakalli agogo yace,

Ya salam" yana sauka daga kan gadon.

Tare suka shiga toilet din dakinta sukayi wanka Wanda yadaukesu dogon lokaci sbd tsayawa shiririta.

Koda suka fito kan cinyarsa ya zaunar da ita tana goge masa ruwan jikinsa yana kallon gashinta dake 'digo masa ruwa sbd wasan dasukai acikin bathtub yasa dole suyi wankan tsarki.

Riqo hannunta dake goge gashinsa yayi tareda Shafo gashinta har zuwa fuskarta ya zarce cikin towel dinta ya shafo cikinta dake lafe yana kallonta cikin wani irin yanayi da galabaita da zuciyarsa ke ciki.

Daqyar ya bude baki cikin wani irin taushin murya yace,

I have something precious inside you so daga yanxu bazaki sake ganin albinon malaminkiba sbd gudun daukar jajayen ido da qaton baki.

Murmushi zancensa yasa tasaki tareda zare hannunta taci gaba da goge masa gashi batareda tace komaiba.

Sake riqe hannunta yayi yana tsareta da ido yace,

I will miss this smile dakikeyi danki hanawa suhailat mijinta.

Kallonsa tayi gabanta na faduwa sbd jin sunan suhailat yasatajin faduwar gaban ta sunkuyar dakai tareda tashi daga jikinsa ta dauko hand dryer ta jona tafara busar masa da gashinsa mai tsananin laushi.

Shidakansa ya shiryata cikin pink gathered neck top da black straight skirt ta Sanya black hula ta fito ta nufi dakin sa ta dauko masa kayan dazai saka takawo masa yasaka suka fito palon hannunta na cikin nasa tanata 6anbare hannunta amma takasa ahaka yajata har gaban ammy dake sintiri a tsakiyar bedroom dinta tana ganinsu tasaki murmushin qarfin hali tana qarajin tausayinsu dan ko ayanxu datake ganin yanayinsu bama zasu iya rabuwa da junaba saidai duk soyayyarsu qila basuda rabon hada zuria sbd bazata so rumanah ta zamto itace zata fara haifarwa  maheer namijiba gwara dai wata kokuma suhailat duk da itama bazataso wani Abu yasametaba saidai so sone amma sonkai yafi.

Cikin kulawa tace,

Rumanah yajikinki?kan yadaina ciwo ko?

Kai ta daga tana sake janye hannunta amma Sam kamar bashine riqeda hannunba.

Abinci sukaci a dining ammy madai hartafi rumanar jin kunyar abinda maheer din kemata kuma ko ajikinsa tamkar bashine yakeyiba.

Daqyar sukaga sungama ammy tarigasu barin gurin tana girgiza kai sbd batasan haka 'danta yake 'dan duniyaba.

Ammy na barin gurin takallesa kamar zatayi kuka yazuba mata ido tareda sakin wani miskilin murmushi kafin ya miqe tsaye ya ranqwafa yayi kissing kanta yace,

Ki kula.

Ya fice yana duba agogon hannunsa sbd lokacin tafiyarsa yayi sosai.

Bayansa tabi da kallo hawayen datake riqewa suka gangaro tasa hannu ahankali tashare tareda miqewa ta nufi dakinta ta zauna bakin gado sai kawai siririn kuka ya kufce mata.

Yini tayi adaki kwance bayan sallah babu abinda ke tayarda ita ko abinci yau ammy daki tasa aka kai mata sbd ta fahimci halinda take ciki na tafiyar maheer 'din.

Da daddare ma kasa bacci tayi harsai kusan asuba ya saceta koda ammy ta leqo taga bacci takeyi bata tadataba sbd tasan balallaine tasamuyin bacci da daddare ba.

Koda gari ya waye sosai guraren qarfe goma ammy tadawo ta tararda ita cikin wani zazzafan zazzabi nan hankalinta yafara tashi musamman yanda jikinta yayi wani mugun zafi banda amai babu abinda takeyi

Ganin abin na girmama yasata sanarda s salma nan aka kirawo Dr faduwa tazo tadubata tareda fara mata pregnancy test dan karta maganin da baikamacetaba awon farko ciki ya tabbata nan ammy taqara shiga damuwa ga farin ciki ga fargabar abinda zai iya zuwa yadawo.

Magani tarubuta tareda Wanda zaita tasamu dan bacci kota huta daga aman.

Kallonta ammy tayi bayan fitar Dr faduwa tasauke ajiyar zuciya tareda mata sannu cikin tsananin kulawa da qaunarta.

Abinci ammyn tasamu taci daqyar kafin tayi sallah tayi wanka ta kwanta wani sabon baccin yayi gaba da ita.

Tunda yatafi bata sake lafiya ba sosai ciwo ya kwantarda ita komai taci baya zama cikinta
Duk inda hankalin ammy yake ya ninka tashi drip kuwa tasha ledoji qarshemadai daina samata ruwan akayi.

Batasan 'daga masa hankali kokuma shiga haqqin suhailat shiyasa bata fada masa saidai duk yanda taso tare alamarin fin qarfinta yayi dan yanxu wata biyu da tafiyarsa ga mamakinta cikin harya fara tasawa gashi har lokacin ko zaman arkiqi bata iyayi koyaushe akwance take.

Gyara zama tayi ta fuskanci Dr faduwa cikin nutsuwa da damuwa tace,

Yanxu wata hudu kenan cikin yake?

Abinda scanning dina yabani kenan"" dr faduwa tafada tana sake kallon takardar scanning din.

Cikin tsananin damuwa sultana takalli Dr fadwa tace,

Inason axubarda cikin tunda yaqi bata lafiya wuyardatake sha tayi mata yawa banason wani Abu yasameta tunda mijinta baisan dashiba.

Kallonta Dr tayi cikin nazarin zancenta sbd tanaga idan anyi hakuri duk wannan wuyar zata wuce duk da itama tana tsananin tausayin rumanah din.

Cikin nutsuwa tace,

Inaga tunda haryakai wata hudu aqara hakuri idan yakai wata bakwai duk wannan wahalar zata rage sosai.

Girgiza kai ammy tayi cikin damuwa tace,

Acire kawai shine abinda nakeso yanxu.

Kallonta Dr tayi cikin nazari kafin ta bude jaka ta fiddo takarda ta rubuta allura tace aje yanxu akawo zatayiwa rumanah din sai zuwa dare idan ciwon mara yataso idan tafara zuba sai akai mata ita asibiti.

Cikin qanqanin lokaci ammy tasa akaje aka kawo allurar nan suka nufi dakin rumanah dake kwance tana baccin datasamu yadan dauketa.

Yawu masu 'dacin damuwa da wasi wasi ammy ta hadiye cikeda tsananin tausayin rumanah dakuma takaici da baqin cikin abinda zatayi

Bude ido rumanah tayi cikin wani irin laushin ciwo suna hada ido da ammy
Ammyn tayi saurin sunkuyar dakanta sbd tasan haqqoqan rumanah bazasu barsuba komai daren dadewa saidai idan har zubar mata da ciki shine abinda zai kare mata ita daga masifar mineelik to ashirye take data ringa zubar mata da ciki idan tasamu.

Cikin tausayawa Dr ta kalli rumanah tace,

Sannu rumanah,
Allura za'ai miki kisamu 'dan qarfin jiki.

Murmushi qarfin hali tasaki daqyar tareda 'dan muskutawa tabada bayanta cikin nutsuwa tasoka mata allurar tayi mata tana mata sannu.

Saurin barin dakin ammy tayi sbd hawayen dake qoqarin ciko idanuwanta
Cikin tsananin sanyin murya takalli Dr faduwa data fito dakin tace,

Awa nawa allurar zatayi kafin cikin ya lalace yafara zuba sbd........

Wani wawan jiri taji yayi mata muguwar diba tana kallon qofar palon saida Dr ta riqota tareda juyawa itama sukai ido biyu dashi tsaye yana kallonsu babu mai iya gane yanayinsa acikinsu shiya mugun tayarda hankalinsu.

Manage wlh ciwon kai ke damuna yau.
#mamuhgee

TARAYYADonde viven las historias. Descúbrelo ahora