12

11.9K 1K 129
                                    

Akan nuratu jakadiya ta tsayarda idanuwanta tana nazarinta sbd zama da rumanah yasa itama takeda nutsuwa daidai gwargwado......

Tsaya to idan zama da rumanah yasa takeda nutsuwa ba kamar mahaifiyarba me zai hana su dauki Mai nutsuwar gabaki daya.

RUMANAH"""shine sunan dayazo ranta atake tasaki murmushi cikin farin ciki sbd tasan sultana idan taji ta inda jikokinta zasu fito bazataji damuwaba.

Sallamarsu tayi tareda juyawa kar tsaye ta nufi hanyar zuwa gurin sultan.

Tana zuwa akai mata iso cikeda girmamawa ta zube gabansa cikin bayyanarda farin cikinta tace,

Allah yataimakeka ansamu baiwa mafi nutsuwa da kyawu acikin bayin masarautar mineelik,
Baiwa ummu-rumanah 'yar tsohon aminyaccen bawanka bulama.

Shima wani irin murmushi yasaki tareda kallon Jakadiya yace,

Allah yayi saina hada zuria da bawa mafi soyuwa agareni
Aje ashiryata yau za'a fara rakata turakar yarima
Bulama Allah yaji qanka da rahamarsa,

Jakadiya kije idan ta haifi namiji ina miki albishir da akwatin dalolin amurka.

Miqewa tayi tana zuba godia da farin ciki tareda adduar asamu biyan buqata.

Lokacinda ta isa gurin sultana ta zube gabanta ta zauna cikin farin ciki tace,

Allah yataimakeki Ansamu wadda nasan zakifi kowa farin cikin fitowar jikokinki ta tsatsonta.

Kallon rashin fahimta sultana tayi mata cikin qoqarin Kore damuwarta sbd jin ansamu mafita.

Baiwa ummu-rumanah ta wajenki itace nakega tafi cancanta da'a za6a sbd ganin nutsuwa dakuma shakuwar dake tsakani.

Wani irin kallo sultana ta jefi Jakadiya dashi cikin mamaki da takaici.

Datasan rainon datakewa rumanah na idan tasamu sanin asalintane daga mamani ta 'yantata danta koma gida cikin yan uwanta ne.

Dauke kai tayi cikin bada umarni tace,

Kije kinema masa wata banda rumanah.

Kallonta Jakadiya tayi da sauri cikin mamaki tace,

Allah yataimaki sultana naga tafi kowace baiwa cancanta tazamo uwar jikinki koba komai tunda 'danki ne ba wani akace akaiwaba.

Girgiza kai tayi tareda juyawa takalli qofar bedroom dinta da rumanah ta fito cikin nutsuwa daukeda zanin gadon data cire ta fice tana mamakin kallonda suka biyota dashi kamar ta canza.

Laundry din masarauta ta nufa takai kayan ta karbo wasu sabbin zannuwan gado masu laushi farare qal tana fitowa mamani ta shigo part din laundry din daukeda kayan wankin adama itama takawo.

Saurin matsawa tayi tana cewa,

Mamani sannu da aiki.

Tsayawa mamanin tayi tareda kasa danne baqin cikinta da takaicinta akan rumanah din sbd ko yauma dai ba'a zabi nuratu ba sbd ko wanka batayiba.

Cikin takaici tace,

Rumanah tunda kika zuga nuratu Dan karmu samu farin ciki kema bazaki ta6a farin cikiba arayuwa,
Keda iyayenki kunzamarmin muguwar qaddara sun mutu sunbarmana masifa gashinan kin shiga tsakanina da yata kin shiga tsakaninmu da farin cikinmu....

Rintse idanuwanta dasukai jajir tayi Cikin dannewa tace,

Kiyi hkr mamani bawa baya wuce qaddararsa ko.......

Shaqota tayi cikin tsananin baqin ciki jitakeyi kamar ta cire takaicin iyayenta na shekara da shekaru akanta ta huta.

Hawayen wahala rumanah ke fitarwa sosai batareda tayi yunqurin kwatar kantaba.

TARAYYAWhere stories live. Discover now