26

13.5K 1.2K 152
                                    

Haske writers association💡

Dan Allah daga yanxu yanzu idan kasan labari baya maka dadi zaifi idan zaka daina bi sbd wata maganar batada dadi kuma kowane marubuci idan harya fara rubuta labari to shi yasan saqon dayake son isarwa kuma idan har mai karantawa yayi hakuri ahankali zai riqa fahimatar abinda akeson isarwa dan haka pls mu riqa sanin maganar dazata fito bakinmu,
Nidai nasan abinda nake rubutawa idan kasan baka iya magana mai dadiba to zaka iya tsayawa daga nan sbd bazanso kaci gaba dabiba dan abinda zaizo agaba.

Not edited.
Ammy ya qureda idanuwansa dasuka mugun qara sanyata damuwar abinda tayi muryarta na rawa takira sunansa daqyar.

Ya lumshe idanuwansa yasake kallonta Dr faduwa na ganin haka ta sulale ta fice dan ita ko kallo bata ishesaba.

Gaban ammy yaqaraso ya tsaya cikin wani irin yanayi na tsananin 6acin rai da bata ta6a ganinsa acikiba yace,

Bantaba samun tarba irin wannan ba ko sakin fuska babu bare murmushinki da murnarki.

Da mamaki ta kallesa da sauri zuciyarta na qara tsinkewa dan kuwa abinda take hangowa acikin idanuwansa ta tabbarda yajisu.

Murya cikin sanyi da tsananin damuwa tace,

Maheer nasan kaji komai amma dan Allah inaso ka fahimci manufata tayin hakan dan nikaina ba'ason raina nayi hakan ba wlh zanfi kowa farin cikin ganin rumanah ta haifa maka 'yaya saidai I can't risk her life.......

Oh please ammy karki fara kawo maganar risking life anan sbd babu Wanda ya isa yahanawa bawa shiga qaddararda Allah ya dora masa,
Ammy  kinsan meyasa kuke wahala da masifar mineelik haryansu shine sbd kuna sake qarfafawa abin ne,
Meye alaqar 'yayana da wannan tunanin naki dazaki min haka?
Meyasa zaki rabani da abinda ko hannuna bai shigaba?
Shin ammy ina iliminki da saninki yayi dazakiyi tunanin namiji zata haifa bayan bakida masaniyar hakan......

Cikin 'daga murya da takaicin abunda ke faruwa ayanxun tace,

Kana tunanin ina nuna kamar nasan zata haifi namijine shiyasa nayi hakan?
Amatsayina na uwa nayi hakan sbd sanin matsayin dazata hau idan ta haifi namiji Wanda kasan mezata zama idan harta zauna wannan matsayin musamman da jinininta bai zamto na sarautaba saitafi wainda suka gabata zama baraza da abin fargaba......

TARAYYAWo Geschichten leben. Entdecke jetzt