14

10.1K 914 20
                                    

Gyara tsayuwa suhailat tayi daga bakin tafkeken windon bedroom dinta iska na daga curtains suna ta6o har fuskarta sbd sosai take buqatar iskar sanyin AC bazai mata ba she's feeling suffocated already.

Gyara tsayuwarta tayi akaro na ba adadi tana tsananin buqatar Wanda zai bata kulawa ayanxu sbd wani irin kishin mijinta dakecin duk wani jini dake yawo acikin jijiyoyin jikinta,

Tana tsananin so da qaunar maheer,
Maheer na respecting relationship dinsu sbd 'yaya dakuma zaman fahimta dasukeyi Saidai maheer na buqatar macen dazaiji dadin yin rayuwarda yakesonyi da ita Wanda bata fatar yasamu hakan daga wata macen bayan ita,

Yanda labari yazo mata baiwa rumanah ce aka za6a
Tsoronta na qaruwa aduk lokacinda ta tuno kamanni da tsarin rumanah din Saidai kuma bata tunanin tafi bata tausayi sbd sanin waye maheer bazai ta6a iya kwana da wata mace ba musamman wadda ba matarsaba.

Girgiza kai tayi tana mayarda dogon gashinta daya barbaje baya ta zauna bakin lafiyyan gadonta tana cewa,

Ya Allah ka yayamin wannan azabar danakeji cikin raina
Hawayen datake dannewa tun lokacinda zancen yazo mata suka 6alle ahankali tafara fitarda sautin kuka tana rufe fuskarta.

Kallo daya yayiwa gefenda take ya nufi bedroom yashiga ya tube yashiga cikin bathtub yakwanta tareda rufe ido yana qoqarin samun nutsuwa azuciyarsa har tsawon lokaci kafin yayi wanka yafito 'daureda towel milk colour yanufi closet yadauki kaya yashirya cikin kayan bacci ya fesa turare mai sanyin qamshi ya nufi gadonsa ya kwanta hankali kwance cikin nutsuwa tareda shigewa lallausan duvet ya zira hannu yakashe wuta ya lumshe ido sbd shi baimasan ta yaya zai saka zancen sultan aransaba bare harya cika kwata kwata shi ba mutumne mai yawan maganaba idanuwansa da kallonsa suke bada magana ko umarnin abinda za'ayi kuma shima mutumne dazai iya 6ata lokacinsa gun abinda baima shafesaba kokuma abinda baidauka da mahimmanciba shiyasa ko kallo baiwar bata ishesaba idan sungaji da kawota zasu daina Dan Kansu ko yanxu yabartane aringa kawota sbd abinda sultan yafada akan ammynsa if not baisan yama za'ai yaringa kwana daki daya da wata macenba bayan ko matarsa basa kwana daki daya.

Tunda yashigo ta lafe jikin kujerar tareda tsayarda duk wani motsinta ta sunkuyar dakai numfashinta na tsananta fita
Tana rabe kanta sunkuye yayi duk abinda yakeyi ya kwanta tana ji tana jiran taji ya tunkarota amma ko kallon inda take baiyiba harya kwanta.

Ajiyar zuciya tasauke ahankali hawaye masu sanyi suka gangaro fararen idanuwanta bada damu data sharesuba sbd duhune adakin ta kwantarda kanta kan gwiwoyinta hawayenta nacigaba da gangarowa.

Asubar farko Jakadiya tazo ta tsaya palon qarshe riqeda doguwar rigar dazata rufe kayan barcin  dake jikinta.

Miqewa tsaye tayi jikinta ba qwari sbd kuka da rashin bacci ta nufi qofa.

Alarm din gefen gadonsa dake tadashi sallah sbd ba'a shigowa ko palonsa na biyu bare atadashi sallah yasa yakeda alarm na tadashi sallar asuba kawai.

Ringing alarm din yasa ya cira hannunsa daqyar cikin bacci ya danna hasken wutar dakin
Tayi saurin juyowa afirgice sbd takai tsakiyar dakin takusa isa qofa daidai shikuma ya bude oily eyes dake cikeda bacci suka sauka akanta,

Dishi dishi yake ganinta ya lumshe idanun yabudesu itakuma hartayi saurin ficewa.

Tana ganin Jakadiya tsaye wani irin tsoro da mamakinta suka kamata amma saita sunkuyar dakai jakadiya ta miqa mata rigar ta sanya tareda janyo hular rigar ta rufe fuskarta suka fice.

Kallo daya Jakadiya tayi mata tasan babu abinda yafaru tsakaninsu tasaki numfashi tana cigaba da tafiya.

Suna fitowa qofar part din bayinda aka bari da Daren still sunan suka Mara musu baya suka kaita sabon gurinta suka wuce batareda Jakadiya tace da ita qalaba.

Zamewa tayi qasa bakin gado ta ta qurawa window ido ta fada dogon tunani fuskarta cikeda damuwarda tayiwa rayuwarta dabaibayi.

Tadauki lokaci kafin tamiqe tashiga makeken bathroom din dake dakin tayo alwala ta zame kayan jikinta tareda mayar musu da kayansu cikin wardrobe tasaka doguwar Riga tayi sallah.

Koda gari ya waye ankawo mata abinci bata iyacin komaiba hakama da rana ankawo amma takasa koda kallon abincin.

Arayuwa yanxu batada wani sauran buri ko mafarki sbd yanxu ta yarda mafarki baya zama gaskia,
Ita ayanxu tamkar wata dabbace da duk yanda akaso ayi da ita haka za'ayi ta yarda da qaddara tabarwa Allah alamuranta.

Sultana bawani doguwar nutsuwa bace acikin zuciyarta sbd har lokacin zuciyarta da gangar jikinta sunkasa nutsuwa da alamarin tsoro take ciki sosai sbd tana tsoron abinda zai iya juyewa gaba.

Koda gari ya waye Jakadiya tasanarda ita babu abinda yafaru tsakaninsu hakanan tasamu kanta da ajiyar zuciyarta tayi shuru tsawon lokaci kafin takalli jakadiya cikin wata irin murya tace,

Jakadiya zansa acirewa rumanah mahaifa sbd fargabata tana yawa Wanda hakan nabani cewar zata iya haihuwar namiji Wanda nibana mata fatar zamowa MINEELIK-ASSULTANAH kuma kinfi kowa sanin me hakan ke nufi,
Tayi yarinya da riqe wannan matsayin sbd bala'i da masifar dake ciki yafi qarfin shekarunta Dan haka abin zaifi ta6ata.

Shiru Jakadiya tayi kafin tagyara zama cikin son gyara zancen tace,

Allah yataimaki sultana cire mata mahaifa tamkar mun qarasa nakasta rayuwartane,
Ke tamkar uwa kike agareta muyi mata fatar samun 'ya mace ta yanda idan tasamu yantawa akorata nesa da nan taje tayi aure tafara gina wata sabuwar rayuwar.

Ajiyar zuciya sultana tasaki tareda lumshe ido tana fatar Allah karya bawa rumanah cikinma kwata kwata ana dakatarda ita daga zuwa gurinsa ta 'yantata ta turata nesa da nan.

Mamani duk wani baqin ciki da quncin duniya yataru axuciyarta tun lokacinda aka tafi da rumanah ko ruwa ta kasa sawa cikinta jitakeyi kamar zuciyar naci da wutane saidai tana addua da fatar Allah yasa ko cikin 'ya mace karta samu bare na namiji.

Sarauniya adama kuwa komawa tayi tamkar zata mutu sbd baqin ciki acikin dakinta laifi qalilan zakayi tasa arabaka da lafiyarka sbd ta daura damarar yaqi da duk Wanda zaishiga tsakaninta da abinda take buri tun tana qanqanuwarta.

Kamar jiya qarfe goma aka zo tafiya da ita bayan anshiryata cikin rigar da gwara ta jiya da ita suka tafi.

Yauma a qofar shiga bedroom dinsa ta zame rigar sama da ribbon gashinta ya zubo dakanta yau ta bude tashiga batada kuzari ko kadan ta nufi inda ta ra6e jiya tazauna tareda kwantarda kanta kan gwiwoyinta ta rufe idanuwanta ahankali.

Kwance yake duk yau ko ina bai fitaba iyakacinsa palonsa na biyu inda nan yake cin abinci sbd nan ne dining room dinsa,

Ko suhailat ma so 'daya takirasa awaya tana qoqarin boye damuwarta da kishinsa tagaidasa tabasa su amah sukayi masa 'Dan surutunsu Wanda duk sukeyin abinsu iyakacinsa sauraransu suka gama.

Ammynsa ma yau awaya yagaidata koina bai fitaba yayi kwanciyarsa.

Tun lokacinda tashigo yaganta ya rufe idanuwansa ahankali tareda gyara kwanciya sai alokacin ta fahimci yana 'daki sbd duhu bata luraba amma ko motsawa batayiba tayi Shiru ko tunanin bata iyayi yanxu
Ahaka asuba tayi ta miqe jikinta amatuqar sake ta fice.

Ahankali kwanakin suka ja kusan sati biyu ana kaita amma baitaba ko kallon inda takeba.

Abu 'dayane daya fara canzawa shine qamshinta daya kama koina acikin dakinsa har toilet dinsa Wanda hakan ne kesakashi 6acin rai wani lokacin.

Itakuma ayanxu tarigada tasan bazai ta6a yin komai da itaba shiyasa kowane irin kaya aka bata bata damuwa sawa takeyi.
#mamuhgee

TARAYYAWhere stories live. Discover now