Saki jikinsa yayi sbd wutar data daukewa jikinsa da wani irin qarfi ammy ta jijjigasa tareda kiran sunanda da qarfi ya durqusa tareda jawota jikinsa ya dauketa gabaki 'daya yabar gurin da ita.
Anso tsayarda nadin sarautar amma haroun ya fitarda saqonta na gaba dake cewa duk abinda zai faru kar a tsayarda nadin dakuma takardarta tagaba dake cewa a raba mara masarautar biyu a rushe Rabin a gina masallacinda yafi kowane girma a qasar Ethiopia.
Hakan yasa aka cigaba da nadin yayinda sultan dake zaune har aka gama bai motsa daga inda yakeba saida aka watse aka gano ya rasu zaune agurin gakuma jinin da aka ganin ya digo daga hancinsa.
Lokacinda su negasi suka rufu akanta dan ceto rayuwarta alokacin ne aka zo da saqon rasuwar sultan Wanda ya girgizasu ya qarasa wargaza dukkanin sauran nutsuwarsu musamman ammy data kasa riqe kukanta maheer yayi saurin rungumeta yana riqe nasa hawayen sbd Allah yasani yana qaunar mahaifinsa duk mugun halinsa sbd koyaya ya zama mahaifinsane.
Cikin qanqanin lokaci rasuwar sultan da halinda assultana take ciki tareda canza karagar mineelik suka yadu 'yan jaridu da kafafen yanda labarai sukaiwa masarautar wani irin dandazo ana yada abinda ke faruwa.
Dukkanin iyalan marigayi abdulshams sun halarto cikin tsananin baqin cikin wannan rana data riskesu musamman 'yayan marigayiya adama dasuke ganin sun rasa uwa da uba.
Da maraice akai jana'izarsa inda dubban alumma na nesa dana kusa suka hallara inda yawan jama'arsa yasa maheer jin sanyi sanyi aransa tareda yiwa mahaifinsa adduar samun rahamar Ubangiji.
Duk damuwar dayake ciki ta halinda rumanah take ciki bai koma gurinta ba sai dare bayan an watse.
Kai tsaye sashen ammynsa ya nufa inda ya tararda ita tareda sauran 'yan uwansa ya qarasa kusada ammyn ya zauna yana kallonta cikin nutsuwa da tausayawa ya riqo hannunta ahankali ya iya furta,
Allah yaji qansa ammynah.
Kwantarda kanta tayi kafadarsa tareda cewa "amin" da muryarta data shaqe kafin ta 'dora da fadin,
Kaje gurin rumanah dan sanin halinda take ciki duk da meenah da jakadiya na gurinta.
Jinjina kai yayi jikinsa na qara sanyi da tuno wani tashin hankalin dayake ciki.
Lokacinda ya isa sashenta har lokacin bata farfado ba sai jinin daya tsaya Wanda suke sakaran jinintane yayi matuqar qasa sosai.
Zaune ya kwana gabanta yana mata addua cikin wani irin hali dabai ta6a tsintar kansa aciki ba.
Washe gari koda akaga bata farkaba hankula sukai matuqar tashi musamman da jikinta yayi wani irin fari fari Kore Kore ga 'yan jarida dasuka kasa suka tsare a masarautar sunason ganawa da sarauniyar data kafa sabon tarihi a qasar daba tataba.
Duk wani kalar likiti na turai da gargajiya an nuna qwarewa amma abu yaci tura gashi alamunta na sake 6aci ranar da akai uku aranar gabaki dayansu suka tattara suka nufi Georgia..shi,ammy da jakadiya data samu 'yancin rayuwarta itama sai sauran 'ya'yan da kowace takoma inda take aka bar sabon sultan dan gabatarda mulkinsa cikin aminci.
Suna sauka kai tsaye motar asibiti tazo daukarsu aka wuce asibiti dasu cikin tashin hankalinda yafi na farko sbd saki jikinta daya farayi.
Matsayinsa a babbar asibitin garin yasa ana isa da ita dukkanin likitocin dake nan suka taru aka fara qoqarin gano matsalar cikin gaggawa cikin tashin hankali da mamakin yanayin matsalarta sbd basu taba cin karo da irin hakanba.
Ammy daqyar ta iya zama gida saidai gabaki 'daya hankalinta da damuwarta na asibitin gabaki daya cikin kwana ukun ta rame tayi wani irin sanyi ko doguwar magana bata iyawa.