Not edited.⚠
Wani irin kallo sultana ta 'dago tayi masa cikeda mamaki da takaicin abinda yake shirin yi kafin ta bude baki tayi magana cikeda nuna isarsa da matsayinsa yace,
Lij(sadaukin kuma amintaccen mayaqin meneelik) duk wanda ya nuna rashin gamsuwa da hukuncin sultan ko a fuskane ko wanene shi arabasa da abinda yafiso ajikinsa,
Idan nace ko wanene ina nufin kowanene,
Jakadiya kije ashirya sabuwar surukar sultan nanbada jimawaba zata zama uwar magajin meneelik.Yana gama fada ya miqe yashige palonsa na hutawa tareda manyan masarauta dazasu tattauna wani abin,
Wasu majiya qarfin samudawa suka tsaya qofar Dan bata tsaro.Kai tsaye ya miqe yabar palon batareda fuskarsa ta nuna meke cikin zuciyarsaba.
Sultana ma miqewa tayi jikinta amatuqar sanyaye zuciyarta cikeda takaici da tunanin rashin ganin amfanin 'yantawarda tayiwa rumanah tunda hakan baisa ta tsirar da ita daga masifar datake gudar mataba ta haihuwar namiji a wannan masarauta ta mineelik.
Jakadiya kuwa wani irin zufa take yarfewa Tana qoqarin ganin ancika umarnin sultan saidai itama damuwarta da tsoronta yahana farincikinta wanxuwa musamman idan taduba yanayin tsoro da fargabar dake yawan samunsu idan sukayi tunanin rabon dazai shiga tsananin yarima da rumanah.,
Wannan masarauta batada tarihi mai kyau,
Jinin mutanen da ake kashewa yananan yana bibiyar duk wani hakkinsa,
Masiface acikeda masarautar wadda babu Wanda yasanta saisu dasuka ginu acikinta
Har abada bazata ta6a yiwa rumanah fatar shiga cikin jerin wainda masifar zata cigaba da shigarsuba aqarshe tabasu qarshe mai matuqar tausayi da kokawa saidai tasan bawa baya wuce qaddararsa,
Duk dubararsu da qoqarin kubutarda ita idan Allah yace tana cikin masu wannan mummunan qaddarar saita shiga.Zubewa sultana tayi kan daya daga cikin kujerun palonta na farko sbd bazata iya qarasawa na biyunba tareda 'dagawa kuyanginta hannu nan suka watse cikin girmamawa.
Dafe goshinta dake daukeda adon sarqar zinari tayi tareda rufe ido tarasa wane irin hali zuciyarta take ciki sbd takasa riqe tunani ''daya dazatayi cikin biyu auren maheer da rumanah kokuwa korarda sultan yamata gefe 'daya kuma tsoro ne fal yafi cika mata zuciya.
Ya Allah kadubi maraicin rumanah kazaba mata kyakkyawar rayuwa agaba.
Tana cikin wannan halin Jakadiya tashigo 'yan mata biyar na bayanta 'daukeda manyan trays suna qyalli kamar zinari suka jeru sanku sunkuye.
Kallo daya Jakadiya tayiwa sultana 'din tasan tana cikin tension murya asanyaye tace,
Allah taimaki sultana anshirya zuwa gurin shirya sabuwar amaryar yarima maheer sa albarki akazo karba.
'Dago fuskarta datai ja tayi takalli jakadiya batareda tace komaiba ta miqe tashiga bedroom dinta tafito da wani madaidaicin akwati yana kyalli.
Zama tayi tareda aje akwatin batareda takalli jakadiya ba murya ba kuzari tace,
Allah yasawa aure albarka.
Amin jakadiya tace tareda kai hannu tabude akwatin.
Sarqoqin zinari ne masu nauyi da marasa nauyi nakai dana qafafu taredana wuya da awarwaro har kusan basa qirguwa.
Hannu Jakadiya tasa tana zarosu tana zubawa acikin tray dinda suka shigo dasu harsaida tray din yacika suka fice,
Sashen adama suka isa tana zaune cikin royal kushins din dasuka qayata palonta cikeda girmamawa aka iso mata da saqon zuwansu Jakadiya tace sushigo.
'Yan matanda ke bayan Jakadiya 'daukeda manyan trays din takalla cikeda mamaki sbd alamu na sakawa aure albarka zaka bayar.,
Wane zaiyi aure kuma ayau batareda tasaniba?
Lallai ana wasa da ita amma karsu damu da zarar ta 'Dora mazaunanta akan kujerar mulkin mineelik tayi alqawarin bawa dabbobin dake zagaye da qasar naman wainda suke wasa da alamarinta.