37

11.7K 1K 40
                                    

Haske writers association

Not edited
Shiru tayi tana kallonshi cikin nutsuwa, ta rasa ta inda zata fara  taimakonshi satar kallonta yayi cikin nutsuwa, sannan ya sauke numfashi yace.
     
     Rayuwarsu a dajin wani irin rayuwa ce, mai ɗauke da soyayya da wani irin kulawa ba daga itaba har zuwa ita kanta. Mafi lokuta takan zauna tayita tunani anya ba wani kuskure bane yake shirin afkuwa na amincewa bil'adam, sai wani ɓangare na zuciyarta ya tuno mata tarin alkhairin da Jamal yake mata,

              Wani lokaci suna zaune ta kalleshi, a nutse kafin tace,

"Menene silar barowarka daga gida ka shigo wannan dajin har kake tunanin kashe kanka da rayuwarka."

               Kirjinshine ya bada wani irin sauti, kura mata ido yayi yana qoqarin qin barinta gano yanayin daya shiga cikin daidaita  nutsuwa sai ya sunkuyar da kanshi cikin nuna baqin ciki yace,

Idan kika san abinda ya baroni da dangina sai kema kin gujeni, labarina ba labari bane sbd cike yake da bakin ciki.

  Dafe goshinshi yayi yana dauke kai yana girgizawa cikin damuwa mai tsanani sannan ya cigaba da cewa,

"Idan kika san koni waye guduna zakiyi gwara mubar maganar haka dan babu alkhairi a ciki.

         Wani irin qayataccen murmushi tasaki cikin qasaitar mulkinta dabatamasan tayiba tace,

Kayi min halacci zama tareda ni kana kula dani tamkar nauyina yana rataye akanka dan haka bazan gujekaba fadamin.

           Girgiza kai ya cigaba dayi yana cewa,

Karki so jin waye ni, karki so jin waye ni, labarina cike yake da kayan haushi da bakin ciki.

           "Ko baka  yarda dani bane, dan idan ka yarda dani ai babu abin bakin ciki a jin kai waye saima karin amintaka a cikin zamanmu.
 
Gyara zama yayi zuciyarsa cike fal da farin ciki dan abinda zai fada mata shine matakin nasararsu.

      "Kamar yanda na faɗa miki ni marayane bani da uwa bani da uba, amma akwai kawunaina, kasancewar iyayena sun mutu basu bar min ko 'dayaba koda kuwa kaza ce yasa na zama abin tsangwama a cikin mutane, sannu a hankali na fara niman nawa na kaina sai dai...

           Kura mata ido yayi cike da jin ba daɗi da kuma hango yarda da Amana da tabashi sai ji yayi akaron farko bazai iya cika wani mugun kudiri a kanta ba, sunkuyar da kanshi yayi cikin wani irin yanayi na sanyin jiki wanda bawai dan maganar da yake mata bane sai dan akaro na farko da zuciyarsa ta hango masa  kuskure da suke shirin tafkawa ne Wanda zai iya bibiyarsu har jikokin jikokinsu na qarni mai zuwa.

         Cikin nutsuwa tasake kiran sunansa tace,

Karka damu nimai riqe sirrinkace.

   "A'a mineelik ina tsoron karki guje nine.

                "Ina tare da kai nace ka yarda dani.

    Gyaɗa kanshi yayi sannan yace,

"Nayi kokarin neman nakaina amma abu yaci tura daga nan kome na taɓa sai ya lalace kai ko kayan mutane na taɓa ya tashi aiki sbd baqin Jini da baqin qashin tsiya da'ake cewa inadashi daga nan mutane suka shiga jifana da mai kashin tsiya bani da albarka a rayuwa haka bai isheni ba sai na faɗa niman aure nanma mutane suka shiga korata a kofar gidajensu suna goranta min ynx waye zai yarda ya bani auren ɗiyar shi yanda tsiya da fatara ya kewaye rayuwata,
Qarshe ko qofar gidajen mutane sunhanani bi idan nabi qofar gidan mutum aranar saiya rafka babbar hasara tou tsangwama da qyama yasa nabar garin nashigo duniya shi yasa na shigo dajin nan sbd jin labarin ha'darinsa naso koma meyene aciki ya kasheni.

TARAYYAWhere stories live. Discover now