34

12.3K 1.3K 250
                                    

Haske writers association.

Not edited.
Arazane sultan,adama,ammy,da baqin sarakunan dasukazo suka kalleta
Babu Wanda ta kalla acikinsu tayiwa kaleeb kallo 'daya idanuwanta na sake bushewa cikin gaggawar cika umarninta kaleeb ya daga shar6ebiyar takobinsa mai cire kai lokaci 'daya ya 'dora a wuyan nuratu dake hawaye ta qurawa rumanah ido.

Numfashin wahala mamani ta fitar cikin tashin hankali ta bude baki zatai magana adama datai mutuwar zaune tayi sairi tashi tsaye jikinta na wata irin tsuma zatai magana rumanah ta 'daga hannu batareda takalleta tace,

Duk Wanda yayi magana batareda hukunci ya gama tabbatuwaba abakin rayuwarsu ko wanene.

A gigice adama tasake kallonta cikin wani sabon tashin hankalin takoma ta zauna zufa na karyo mata jikinta na wata irin tsuma.

Tayar da ita akayi tana numfashin azaba takalli takobin datake qyalli a wuyan nuratu takuma tabbarda yankata din za'ayi.

Ahankali rumanah ta 'dagawa kaleeb kai alamar yacika aiki.
Atake ya 'daga takobin cikin wahalalliyar murya mamani tace,

Gimbiya adama ce.

Cak kaleeb ya tsaya sbd harya 'dora takobin a wuyan nuratu harma saida ya'dan yanketa.

Arazace sultan yakalli adama data jiqe jagaf da zufa jikinta na tsuma tanason kare kanta gashi ance duk Wanda yayi magana bbakin ransa kuma tasan tsaf rumanah zata iya sbd tasan abinda ka cikin karagar zaifi shigarta kasancewarta mace dan haka zatafi rashin tausayi da imani.

Sarakunan dake gurin duk ita suke kallo cikin mamaki yayanta kuwa kuka suka fashe dashi gashi babu ikon ko qwaqwaran motsi.

Rufe ido rumanah tayi wani irin yanayi na tsuma zuciyarta gawar 'danta da iyayenta tana mata yawo ido da irin tozarcinda ammy ta fuskanta akan hakan
Fuskar maheer ce ta fado mata da irin tashin hankalinda tagani ataredashi tsakanin jiya zuwa yau ta bude idanuwanta dasukai jajir tace,

Ni sarauniya ummu-rumanah bulama na halastawa takobin kaleeb adana jinin adama kisheer ayau agaban mijinta da 'yayanta tareda sauran alumma duk Wanda ko a fuska ya nuna hukuncina baimasaba a shayar dashi dafi daidai irin Wanda adama tashayarda qannen magajin mineelik.,

Baiwa mamani arufeta mai rubuta tarihi yaje tabasa tarihin sarauniya rumanah arubuta atarihin mineelik tana gamawa bazata qara minti biyar aduniyaba a shayar da ita Kofi 'daya na daafin macijin dayafi kowanne kaifin dafi,
Sultana zaarah da jakadiya sunfita da zargin da ake musu.

Sultan abdulshams arufesa a turakarsa babu shiga babu fita aabisaga zarginsa na qoqarin yanke hukunci batareda bincikeba harsai angama bincike akan niyarsa sultana zaarah ce kawai keda damar shiga da fita agurinsa sai yarima maheer.

Arikice sultan yakalleta ransa na mummunan 6aci da baqin ciki ace rana 'daya cikin mintunan dabasu wuce biyarba baiwa wadda bama asalin 'yar qasaba ta saukesa akan mulkin daya gada iyaye da kakanni,
Ta yankewa matarsa kisan wulaqanci agaban dubban jama'ar dasuke shakkar ko kallon inda yake sannan yanxu tace arufesa a turakarsa wannan shine tozarci mafi muni arayuwa...

Yanxu ta karbi mulki idan tagano shine asalin dalilin mutuwar iyayenta akwai masifa sosai sbd yanda sihirin karagar nan ke shigarta nan cikin qanqanin lokaci zata zamewa kowa masifa mai matuqar hadari musamman shi saidai duk masifa duk balai bazai bari yayi mutuwar wulaqanci a hannuntaba koda hakan na nufin hada hannu da balain da aka binne shekaru tun kafinsu.

Kama adama akayi aka fara janta tayi saurin kwacewa ta isa gaban rumanah ta zube tana kukan tashin hankali jikinta na mugun karkarwa saidai takasa magana sbd umarninda rumanar tabayar ko kallonta rumanah batayiba ta kalli su kaleeb atake suka fara yiwa adama jan wulaqanci.

Jikin ammy ne yadauki rawa cikin sabon tashin hankali take kallon rumanah tana girgiza kai sbd matuqar tafara mulkinta ayau da zubarda jinin wani to tabbas zaiyi wuya bata zamewa mutane abin tsorobas.

Qoqarin isa gurin rumanah din tayi aka dakatar da ita ta hanyar tareta tayi saurin kallon rumanah data rufe idonta tanajin wani irin baqon yanayi shigarta.

Cikeda rashin imani da tausayi kaleeb ya daga takobinsa yacire kan adama data mutu tana ihu da fizge fizge.

Tsit gurin yayi sbd tsoro da firgici sbd duk mulkin sultan ba'a taba kashe mutum agaban alumma ba sai yanzu nantake kowa yaji tsoro da fargaba tareda tashin hankali na shigarsa atake kaleeb ya 'daga takobinsa dake 'digar jinin adama sama ta bude idanuwanta ahankali takalli jinin dake diga qasa ahankali tasauke ajiyar zuciya ta miqe tsaye.

Cikin wani sauti da babban sauti sarkin na'di yace,

Dogon zamani MINEELIK ASSULTANA UMMU-RUMANAH UWAR MAGAJI.

Juyawa tayi wasu irin samudawan masu bata tsaro da kuyankinta mata suka mara mata baya tashige.

Tafiya kadan tayi ta tsaya cak sbd abinda takeji ajikinta
Wani irin abu takeji kamar yana tafiya da motsi ajikinta ta dafe qirjinta da takejin yana quna.

Ammy tayi saurin nufota aka sake tareda
Rumanar ta 'daga musu hannu daqyar alamar subarta ammyn tayi saurin qarasowa kafin tayi yunqurin ta6ata sukaga ta yanke jiki ta fadi jini na fita ta hancinta atake hankalinsu yayi masifar tashi ammy na qoqarin 'dagota suka gansa kansu idanuwansa jajir jijiyoyin sun firfito ya durqusa ya dauketa ya nufi sashenta da ita cikin qanqanin lokaci aka zuba wasu irin tsaro tundaga qofar sashenta har zuwa qofar masarautar atake labarin halinda take ciki ya yadu nan mutane suka sake shan jinin jikinsu atake aka rufe duk wata qofar shige da fice dake mineelik aka dauko duk masu bada maganin sarauta na asalin gargajiyarsu nanda nan aka hau dubata suna qoqarin tabbatarda abinda suke tunani.

Cikin wani irin tashin hankali da damuwa yake,
Zafi sosai yakeji acikin xuciyarsu akaro na farko dayaji zuciyarsa na karaya akan abu saidai yasan mutuwace kawai zata rabasa da rumanah dan haka duk abinda zata zama ayanxu ashirye yake daya sadaukar da rayuwarsa akan cetota daga masifar dake tattare da wannan karagar.

Jini ne sosai yake fita ta hancinta ahankali tafara wata irin jijjiga jijiyoyin jikinta suka ringa firfitowa Kore sosai nan take hankalin su negasi(masu maganin gargajiyar qarnin baya na sarauta) ya tashi
Maheer da idanuwansa sukai mugun rikidewa yayi saurin nufarta zai rungumota cikin wani irin sauti negasi yace,

Karka kusanci inda take ko kusa a wannan yanayin hadarine mai matuqar gaske dankuwa dafine yake yawo ajikinta yanxu idan jininta yafi qarfin dafin zataci qarfinsa ta tashi idan kuma dafin karagar yafi qarfin jininta shikenan sai hakuri sbd har abada bazata koma daidaiba zata zama rabi hankali rabi nakashe.

Cikin wani mumman tashin hankali ya dafe goshinsa akaro na farko yaji idanuwansa suna qoqarin tara hawaye ya fito dakin baya gani sosai sbd tashin hankali
Ahankali yaji andafasa yana juyowa yaga suhailat rungume da abeel baisan sanda ya fada jikintaba ta rungumesu gaba daya shida abeel din hawaye na gangaro mata cikeda tausayinsa dana rumanah taso tafiyarta ayau saidai ganinsa Cikin halinda bata taba ganinsaba yasata jin bazata iya tafiya tabarsa a lokacinda yafi buqatarta,tabbas idan tanada wata qaddara arayuwa to soyayyar maheer ce dan haka kamar yanda zai sadaukar da rayuwarsa gurin kulada rumanah duk halinda zata shiga mai kyau ko mara kyau to itama zata zauna ta sadaukar da rayuwarta gurin kula dashi da zame masa garkuwa duk lokacinda zai nemi hakan.

Ammy dake zaune tareda sauran 'yayanta yayun yarima sun biyu da Jakadiya da sauran masu tsaro da jiran tsammanin halinda ake ciki ta rafka tagumi zuciyarta na harbawa da qarfi sbd tasan me hakan ke nufi dan kuwa rumanarsu tariga ta tafi sbd idan har komai yagama shiga jikinta duk abinda yafaru shekara da shekaru tun kafa mineelik zata gani Wanda shine idan kaga masifun dake ciki yakeda wuya baka haukaceba idan ka farka.
ASALIN MINEELIK.......
#mamuhgee

Kuyi manage na fitane so mu kama gobe.

TARAYYAWhere stories live. Discover now