40

13.6K 1.3K 204
                                    

Haske writers association

Not edited.
Kallonta yayi yana sake kafeta da manyan idanuwansa ransa na qoqarin 6aci da zancenta zuciyarsa na qoqarin hana faruwar hakan ya bude baki zaiyi magana ya fasa ya kama hannunta da qarfi ya jata part din ammy dake kusa
Tsakiyar palon ya saketa tareda kallonta cikin sautin dake nuna bacin ransa yace,

Me kika fada yanxu?

'Dauke kai tayi kai tsaye tace,

Kana qoqarin kare sultan ne akan laifukanda yariga ya aikatasu ne cikin son rai da ganganci saidai kuma nariga nayi alqawarin duk Wanda ya cutatar da wani sai anbi masa haqqinsa sbd wannan shine adalcin assultana,wannan shine banbancin mulkin son rai da adalci....duk Wanda ya kashe a kashesa wannan shine hukuncin a musulunce.....

Riqota yayi da qarfi ransa na qarasa 6aci yace,

Kina tunanin na hanaki hakane sbd sultan yana nahaifina?
Kisa dai matuqar ina raye kuma da aurena akanki bazan ta6a bari kiyiba ko adama kin kashetane a lokacinda bana kusa da bazan taba bari ki kashetaba and da.....

Qwacewa tayi tana kallonsa tace,

Nice na kashe adama kana qoqarin cemin mai kisa ne????
Bayan kasan mutanen nan sun cancanci kisa tako wane sashe na sharia,
Anyiwa iyayena kisan wulaqanci da son rai,
Anyiwa 'dana kisar son rai da ganin dama duk basune masu laifiba nice danake shirin qaddamar da adalci wa kaina amma y.......

Idan kina maganar abeel Hussain ne ni mahaifinsa nabarwa Allah duk Wanda keda saka hannu nabarsa shida ubangijinsa maganar iyayenki kuma amatsayina na mijinki nake baki umarnin kibarwa Allah bazaki qara yankewa kowa kisar wulaqanciba ki tabbatarda idan kika sake hakan ni maheer abdulshams mungama zama tare abakin aurenki gabak......

Cikin tashin hankali suhailat dake palon basusan da itaba tayi saurin katsesa da cewa,

Abu abeel ka.....

Shut up and stay out of this suhailat"""""yafada ransa a matuqar 6ace.

Rumanah datai mutuwar tsaye tana kallonsa idanuwanta sun kada jajir suna zubo hawaye zuciyarta takai qololuwa gurin tashin hankali da baqin ciki ta bude baki cikin baqin ciki tace,

Basaika datse alaqar dake tsakaninmuba nasan bana ranka ko gabanka kayi qoqarin barina da aurenka har zuwa yanzu da baka sallameni bayan haihuwataba sbd itace amfanina daman shiyasa kace haka sbd sanin sirrin zuciyata saidai........

Fixgoto yayi da qarfi zaiyi magana ta fixge jikinta tana sakin wani irin kuka mai qarfi da ciwo sbd zancensa ya girgiza duniyarta gabaki 'daya ya kasheta jitake zuciyarta kamar zata babbake ta kama da wuta sbd masifar dake ci mata zuciya.

Cikin tsananin damuwa suhailat ta dauki abeel ta nufi palon qurya tafadawa ammy dake zaune cikin tunani abinda yake faruwa.

Da sauri ta taso tana shigowa palon ya juya zai fice ammy tayi saurin riqo rumanah dake kuka kamar ranta zai fita takira sunansa ya tsaya cak batareda ya juyowa sbd qaran kukan dake sake hargitsa nutsuwarsa da tafasa zuciyarsa.

Rungume rumanah tayi tana qoqarin rarrashinta saidai kukane takeyi sosai Wanda ke nuna tsananin ciwo da baqin cikin da zuciyarta ke ciki.

Kasa tsayawa yayi ya rintse ido da qarfi ya fice yanajin baqin cikin kukanta da maganganunta.

Suhailat dake tsaye ji tayi jikinta ya qara wani irin sanyi da kukan da rumanah keyi ahankali ta fice daga sashen sbd ganin suna buqatar tattaunawa tsakanin 'ya da uwa dan jin tayi tazama baquwa acikinsu su duka din har maheer 'din.

Shiru ammy tayi da ita rungume a jikinta batareda tace mata komaiba sbd halinda take ciki tana buqatar tayi kukan ko dan ta rage nauyin dake zuciyarta,

TARAYYAWhere stories live. Discover now