Haske writers association💡
Sashen sultana zaarah aka nufa da Asma'u dake waiwayen qofar sashen da aka baro bulama tanaji ajikinta shikenan sungama rayuwarsa atare saidai jiran lokaci kuma.
Lokacinda aka kaita gaban sultana aka gabatarda ita amatsayin kyauta daga yarima.
'Dagowa tayi cikin wani irin farin ciki da murmushi takalli asma'u cikin sanyin lafazi tace,
Allah yayiwa yarima albarka bisaga wannan kyauta.
Sake kallon asma'u tayi dake durqushe gabanta tasaki murmushin farin ciki murya a tausashe tacewa jakadiyarta.,
Akaita abata 'daki sashen bayi abarta tayi kwana biyu ana koyarda ita aiki kafin tadawo nan tafara aikinta.
Angama sultana.
Daki aka bawa asma'u kuma cikin sa'a aka basu daki daya da mamani suka zauna jigum jigum kowa babu da'din zuciya kafin aka sake zuwa aka tafi dasu bayin bayi kowannensu yayi wanka aka rarraba musu uniform dinsu sukabi layi aka basu abinci kowa da 'yar tasarsa
Anan ne asma'u suka hadu da bulama saidai iyakacinsu kallon juna sbd Layin maza dabam na mata dabam hakama ga dukkanin alamar tsaro da dokokinda suka lura dasu agurin babu bawanda ya isa ko yakeda ikon yiwa baiwa magana sbd tsaro dakuma gudun 6arna irinta zina.Duk wanda aka bawa samun guri yake a babban filin ya zauna yafara cin abincinsa.
Daga ita harshi ba wanda ya iyacin abincin sai kallon juna suke daga nesa ba ikon magana har aka gama aka gargadasu aka rarrabasu zuwa sassan dazasu riqa aiki kullum.Kwanansu biyu da zuwa jikinsu ya'dan murmure daga yunwa sbd issashe kuma lafiyayyan abincinda ake basu sbd Sam babu yunwa ga bayin masarautar.
Asma'u da bulama iyakacinsu da ganin junansu idan suka hadu gurin cin abinci.Ganin basuda yunwa kuma babu azabtarwa a masarautar yasa hankalinsu yadan kwanta suka fara maida hankali ga ayyukansu damuwar bulama 'dayace cikin jikin asma'u da mamani.
Sosai asma'u ta dangana ta rungumi rayuwar dasuka tsinci kansu ayanxu tabi uwargijiyarta sbd ganin tana sake mata ba laifi.
Aiki da bauta takeyiwa sultana tuquru babu kyuya ga tsafta da tsananin ladabi.
Tunda sultana zaarah ta lurada cikin jikin asma'u tayi mamaki sosai ziciyarta tashiga wasu wasi takasa hkr ta tsare asma'un ta tambayeta cikin ladabi kanta na qasa tabata labarinsu kaf saidai ta boye mata asalinsu da dalilin barowarsu gida.Cikin tsananin tausayawa sultana tace,
Karki damu asma'u Allah baya bacci kuma insha Allah za'a dauki mataki akan masu kamo bayin koba yanxu ba nasan zasu dawo.
Sosai sultana tasa jakadiya sassautawa asma'u ayukanta sbd yanayin cikinta daya tsufa kuma sosai sultana keyiwa asma'u kyautar fresh fruits masu yawa sbd anason mai ciki ta yawaita cinsu.
Kasancewarsu kusan sa'anni yasa sosai sultana tasa asma'u tasaki jiki da ita tun tana noqewa harta 'Dan sake idan tagama ayyukanta zata zauna gaban sultana suna 'Dan ta6a fira wani zubin harda jakadiya.
Cikinta na isa haihuwa cikin ikon Allah suka haihu rana 'daya da mamani dake aiki sassan sarauniya adama.
Dukkaninsu 'yaya mata suka Haifa sultana dakanta tasa akai mata iso ga sarki tasanar dashi matar mafi soyuwar bawansa ta haihu tasamu mace.
Shiru yayi cikin jinjina alamarin bayi kuma da haihuwa amma saiya share sbd bayason sanin komai yanxu tunda anriga anyi haihuwar yabawa bulama dama yaje yaga yarsa yayi mata huduba.
Koda bulama yaga 'yarsa hawaye 6alle masa sukayi sbd tarigada tafado daga bayi irinsu shikenan ita rayuwarda Allah yaxabarmata kenan.
Huduba yayi mata kafin ya 'durqusa har qasa yamiqawa sultana cikin girmamawa yace,
