5

13.2K 1K 67
                                    

Haske writers association💡

Saida gari yayi haske sosai yayi tsit su kutti sukaji tsit suka fito daga ma6oyarsu cikeda tsoro da tashin hankalin rashin ganin mamani dasu bulama.
Dakatarda sauran yayi ya ringa bin cikin hakukuwa batareda yana dogon motsiba yaje ya leqo qauyen.
Tsit sai koke koken dake tashi gawarwaki kuwa gasunan kwance
Jini kuwa tuni yake gudana a qauyen dabbobinsuma ba'a bariba shiyasa gawarwakin bana mutumba bana dabba ba.

Saki jikinsa yayi sosai zuciyarsa tayi nauyi yasan tunda su bulama basa taredasu to kuwa sun mutu ko antafi dasu tafiyarda bar abada ba dawowa,
Tafiyarda gwara mutuwa da ita sbd a qasqantaccen bawa zaka qare wasuma kafin akai wahala da azaba tareda yunwa takashesu.

Komawa yayi yana daga qafa da qyar jiri na dibarsa yakirawo sauran suka shigo qauyen babu Mai nutsuwa nansuka fara tsallake gawarwaki suna birkito wainda ke kife suna duba sauran iyalan gidan dabaa ganiba.

Tuni suma wasu daga cikinsu suka fara ihun kuka sbd ganin mazansu wasu kuwa sauran matansu Dan duka iyalan gidan baabah din mazansu da matansu tareda 'yayansu su talatin da takwas ne amma su ashirin da 'daya suka tsira ankashe sha hudu antafi da uku.

Lokacinda suka arba da gawar baabah nan suka qara saddaqarwa nandai akayi kukan daza'ayi aka dangana
Mazan dasuka saura haka aka hada gawarwakin sukaje nesa da qauyen suka rufesu suka dawo kowa yacigaba da rayuwarsa amma kullum cikin fargaba duk da sunsan mutanen bazasu dawo yanxuba sai zuwa nanda shekaru masu Dan tsawo sun kwatanci qauyen yasake cika sosai an hayayyafa yara sungirma sunxama samari da yanmata saisu sake dawowa su kwashe.

Tunda dai suna tsoro haka suka sake sakewa suka cigaba da rayuwa aka nada kutti amatsayin sabon shigaba Wanda wannan karon shi akan hada mugayen makamai na itace da dafin macizai da kunamu yamaida hankali sbd yadauki alqawarin angama satarsu ana siyardasu amatsayin bayi yaqi zasu shirya daga yanxu har ranarda mutanen zasu dawo.

*
Abincin dake cikin jirgin nasu ne iya sukadai suci su qoshi su kama wainda suka kamo suyita duka ba ruwansu da namiji ba ruwansu da mace ga yunwa sunbarsu da ita ga qishirwa tuni wasu daga cikinsu suka fara macewa sbd muguwar tafiyace mai nisa dazata kaisu nahiyar da
MENEELIK PALACE take
Duk Wanda ya mutu ruwa kawai suke jefasa ahaka mutanen suka rage da damansu.

Kwanansu goma sha bakwai ajirgin ruwar kafin suka isa da sassafe.
Cikin mutane sittin da 'yan kai dasuka kamo mutane arba'in kawai suka iso dasu daga qauyensu bulama sauran duk sun mutu ahanya.
Bayan 'yan qauyensu bulama dama sunsato wasu daga gurare da dama.

Kamar kayan wanki haka aka gargadosu dukkaninsu hannuwansu a 'daure kusan da igiya 'daya sbd ajere suke.

Babu Wanda zaka kalla kaga kamar baikusa mutuwaba sbd babu Wanda yake iya tsayuwa daidai sbd wahala da yunwa ga dau'da data canza musu kamanni mamani tuni kuka ya qare zuciya ta qafe banda tsanarsu asma'u ba abinda takeji sbd ganin sune sanadin zuwanta nan ga cikin jikinta haryafi na asma'u fitowa.

Bulama duk wuya da azaba asma'u yakeji itada mamani sbd ganin dukkaninsu juna biyune dasu gasu mata.
Kukansa da fargabarsa karsu mutu kafin a iso
Basu mutuba amma dai suna kusa sbd babu mai iya jan qwaqwaran numfashi acikinsu.

A inda suke baza hajar siyarda bayinsu suka xubesu nansuka rarrabu cikin mutanen dake cikeda kasuwar Dan kar agansu da yawa dakuma kalar marasa imani agane satosu sukayi ba bayi bane babbansu  tareda manyan yaransa uku suka isa gurin wani mai siyarda 'yayan itatuwa suka zauna sunacin abinci cikin farin ciki da nutsuwa.

Asma'u ce ta yanke jiki ta fadi da 'dayansu ya lura yamiqe da sauri tareda yiwa ogan nuni da sauri shima ya miqe suka isa gurinta

Bulama tuni yafashe da wani irin kuka sbd yasan mutuwa tayi.

TARAYYAWhere stories live. Discover now