11

11.3K 967 48
                                    

Haske writers association💡

Suna isa part din na suhailat dake kallon na yarima itace tayi saurin matsawa ta bude mata qofar tashiga.

Babban parlour ne daya tsaru sosai da uwayen nairorin da aka zuba masa gurin tsarasa,
Royal cushions ne purple and golden komai na palon qyallin adon kalar golden din.

Duk haduwa da tsaruwar part din sultana saidataga wannan ma na suhailat yayi kyau sbd ita atunaninta baza'ataba samun part dinda yakai na sultana tsaruwa da kyauba saigashi na suhailat dinma ya tsaru kamarna sultana duk da tanajin labarin haduwa da tsaruwar part din adama kasancewarta itama 'yar adoce sosai.

Kuyanginda aka turowa suhailat 'din sukayi saurin shiga taitayinsu suna mata barka da shigowa.

Hannu kawai ta 'daga musu tareda kallon rumanah tana nuna mata 'dakinsu amah tace,

Kije kiyi musu wanka da ruwa marasa sanyi kuma bamasu zafi sosaiba ki shiryasu sai abarsu su huta kafin anjima suci abinci.

Tana gama fadar haka tamiqa mata hannu ta bata handbag dinta ta shige bedroom dinta.

Dakinsu ta nufa dasu tayi musu wanka ta shiryasu harzata fito suka maqale mata takaisu gurin mum dinsu.

Bata saba da yaraba batama ta6a zama da yaraba tun tasowarta
Daqyar tasamu ta lallabasu ta fito.

Tana fitowa part din tasaki ajiyar zuciya sbd gabadaya a takure take sbd tsoro da gudun aikata laifi.

Kodata koma part din sultana a palon farko ta ra6e sbd ganin alamun har lokacin yarima naciki.

Gab da magrib yafito tayi saurin zubewa amma ko lurada akwai mutum shibaiyiba ya wuce yabar part din da qamshinsa.

Sum sum ta nufi palon ciki ta tararda ammyn zaune har lokacin ta durqusa cikin girmamawa tace,

Ammy a table za'a jera abinci kokuwa anan?

Murmushi tayi cikeda farin ciki tace,

Ajera a table kuma ayiwa maheer honey pancakes da sugarless drink sbd bayacin abinci mai nauyi musamman yanxu da daddare
And kihada masa fruitsalad with less apple sai kikai masa part dinsa kisaka a fridge din Palo nasan idan yafito sallar magrib bazai komaba sai dare.

Wani irin yawu ta hadiye na muguwar faduwar data sameta jin inda aka aiketa itadai batason tayi laifi komai qanqantarsa.

Ficewa tayi tafara kawo abinci a second palo tana jerawa a dining jikinta amatuqar sanyaye.

Honey Pancakes din tayi tareda kawowa dining daidai lokacin aka shiga sallar isha takoma tahado fruit salad ta zuba a glassbowl ta 'daura a tray ta nufi part 'dinsa qafafuwanta har wani hardewa sukeyi sbd yanda jikinta ke rawa.

Tana isa kallo 'daya tayiwa guards din qofar ta juya tayi part din suhailat ta saka cikin fridge tareda sanarda kuyangin palon su sanarda suhailat ankawo fruit salad din yarima.

Kodata koma sallah taje tayo tareda komawa part din sultana tana saka kai da sallama dashi idanuwanta suka faracin karo yana cin pancakes din yana yiwa mahaifiyarsa murmushi.

Juyawa tayi da sauri sultana ta lurada ita amma sanin bayi basa zuwa idan yana guri musamman idan abinci yakeci kozaici yasa tabarta takomawarta.

Sai qarfe tara yabar part din sultana yanufi nasa
Yana zuwa ya tu6e yashiga bathroom dinsa da aka cika masa bathtub da ruwa masu matuqar qamshi da 'dumi ya lumshe fararen oily eyes dinsa tareda kwantawa yana sake jin nutsuwa.

Allah yayisa mutum mai tsananin son rayuwa musamman tajin dadi saidai suhailat bata cika son irin wannan rayuwarba itakuma sbd sunada abubuwan dasuka banbanta ra'ayoyinsu saidai suna qoqarin ganin hakan baitaba rayuwar aurensuba.

TARAYYAWhere stories live. Discover now