24

17.2K 1.3K 204
                                    

Haske writers association

Not edited.
Sheraton bamako hotel forth floor room 302 shine dakinsa da ako yaushe yake sauka idan yana qasar.

Babban suite ne dayaji tsari irin na rayuwar dayakeso akoda yaushe.

Zama tayi a darare kan sofa tareda aje handbag dinta tana kallon tsarin dakin.

Tun kafin ya isa yayi musu shopping kayan buqatarsu shiyasa yakalli agogon hannunsa yana 6ata fuska .

Knocking akayi ahankali sbd gudun kar ayi disturbing dinsu
Ga mamakinta ganin tayi ya miqe ya nufi qofar bayan tasan abaya budewa kowa qofa idan kagaji da knocking ne kashigo koka jira amma saigashi yatashi yaje yabude kuma hannu kawai yasa yakarba ya rufe qofar ya aje kan gado yafara 6alle ma6allan rigarsa.

Sauke kai tayi ganin murdadden jikinsa yafara bayyana
Yana gama tubewa ya nufi toilet.

Ya jima yana wanka kafin yafito yabude kayan ya dauki brush da toothpaste yakoma yayo brush yana dawowa ya fitarda turarrukansa da yayi shopping yayi shirin bacci bayan ya fitarda fararen kayan baccin daya siya yasaka ya fidda wayarsa yakira suhailat datun dazu take kiransa.

Miqewa tayi itama tashiga toilet tayo wanka ta fito daureda towel gashinta daure tsakiyar kai sbd karya jiqe gurin wanka.

Duk wani nauyi da kunyar duniya jitake kamar suna kanta sbd mayen kallon daya tsareta dashi tun fitowarta kuma lokacin waya yakeyi da suhailat.

Rigar bacci tagani kan kujerar gaban mirror tadan juyo takallesa ya dauke gira 'daya yana cigaba da wayarsa.

Da mamaki take kallon turaren Prada royal pink for women da shine turarenta,
Ya akayi yasan sunan turaren datake shafawa gashi tamazo da nata suna cikin handbag.

Wanda ya siyo din ta shafa ta dauki rigar tadaga batai mamakin ganin yanayin rigarba datafi kama da babu sbd tun a mineelik da ake sakata sakasu tasaba dasu.

Daga zaunen ya miqa mata hannu na musu tazo ya jawota ya ajeta kan cinyarsa ya zare ribbon 'dinda ke 'daureda gashinta gashin ya zuba yacigaba da wayarsa da suhailat yana cusa hannunsa cikin gashinta zuwa wuyan rigarta.

Cikin nutsuwa suhailat tace,

Zan kiraka gobe insha Allah gud night.

Aje wayar tayi tareda rintse ido da qarfi hawayen dasuka ciko mata suka gangaro kan fuskarta sbd yanayin yanda maganarsa ke fita qasa sosai ta tabbarda akwai abinda yakeyi da matarsa dan mum ta sanarda ita da rumanah yaje.

Share hawayenta tayi tareda miqewa ta nufi 'dakin yaranta takwanta kusada fammah tareda jawota jikinta a hankali tace,

Ya Allah kabani ikon juriya da adauke kai kan abinda bazai shiga haqqinaba nima kodan karna barwa 'yayana abin takaici da kunya.

Rumanah dake lafe jikinsa ta 'dago takalli fuskarta dake kallonta qasa qasa da murya yace,

Kinsa matata ta ajemin waya for the first time banine na aje mata ba.

Wani irin lumshe idanu tayi Wanda yasashi kafeta da ido kafin yakai bakinsa kunnenta qasa qasa yace,

Are you trying to seduce me da wannan idon?

Qanqamesa tayi qarfi ba shiri sbd tsananin kunyar da maganar ta bata ya lumshe ido yana sake shigar da ita jikinsa yace,

Karki damu suhailat is kind hearted ba duka zata hanaki mijintaba.

Miqewa tayi da sauri zata bar jikinsa yasake dawo da ita ta fado masa ya matseta suna kallon juna fuskarsu daf da juna har dogayen hancinsu na gogar juna.

TARAYYATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang