42

12.8K 1.2K 114
                                    

Haske writers association

Not edited.
Kasa motsi tayi tabi bayanta da kallo harta fice ta jima tana kallon qofar kafin ta maido kallonta kan abeel daya farka yana kallon fuskarta ta rintse ido tareda rungumesa tana jin wata sabuwar damuwar sbd rashin sanin abinda yafaru yanxun.

Ahankali ta lumshe idanuwanta mafarkin abbanta datai yau yana dawo mata.

"Ummu-rumanah kibi mijinki a dukkanin umarninsa matuqar basu saba addininki ba sbd shine gatanki kadai yanxu aduniya,
Ki gujewa mulki sbd haqqoqin dubban mutane da bazaki iya daukaba sbd rauninki na zamowa 'ya mace kibarwa Allah komai ki gyara aljannarki."""

Kalaman da mahaifinta ya sanarda ita a mafarki kenan saidai abinda takasa ganewa shine ta yaya zata sauka mulkin batareda ta kawo sauyi da zaman lafiya a qasar ba.

Bude ido tayi tareda jinjina shawararda zuciyarta ke bata dan kawo qarshen komai saidai hakan wani abune mai girma dayakeda matuqar hadari saidai dole zata aikata hakan koda hakan shine ajalinta zatayi dan kawo qarshen rayuwar da alummar qasar suka samu kansu.

Tabbas qaddararta itace ta koro iyayenta daga gida ta kawosu nan sbd gashi abinda yafaru tun qarnikanda ko kakanninta ba'a haifa Ashe tana cikin qaddarar gashi itace zata kawo qarshen abin.

Hawayen tausayin mijinta da 'danta tareda ammy ne suka gangaro mata ta sauke kanta tareda sakin kuka ahankali sbd tasan sune zasufi kowa kukan rashinta arayuwa sbd sune wainda takeda matuqar mahimmanci arayuwarsa ta yanda rashinta zai matuqar ta6a rayuwarsu.

Sunansa ta furta ahankali cikin zuciyarta sbd tasan mutuwarta zata tarwatsa zuciyarsa zatabarsa cikin mawuyacin hali saidai tasan suhailat na nan zata kula dashi.

Miqewa tayi ta nufi dakinta ta kwantarda abeel ta zauna gabansa ta qura masa ido tana fidda sautin kuka ahankali sbd kukane takeyi sosai.

Tana fitowa sashen rumanah kai tsaye shashen ammy ta nufa bata nuna mata komaiba tasanarda ita zataje Mali.

Ammy dake fama da ciwon kai mai tsanani takalleta da idanuwanta ahankali tace,

Allah ya kiyayeki ya hadaki da alkairin dake cikin tafiyar.

Amin ta furta ahankali tareda juyawa ta fice dan dama su amah suna Mali tuntuni da aka fara wainan rudanin.

Motocin dazasu kaita airport na fitowa daga masarautar tasaki wani irin kuka ahankali tareda rintse idanuwanta tana furta Allah yabani juriya da danganar rabuwa dakai maheer.

Suna isa airport basuyi minti ashirin ba suka tashi daga qasar Ethiopia zuwa mali.

Lokacinda ta wuce tabarsa daqyar ya iya fita yabar dakin ya nufi part dinsa yana qoqarin danne halinda zuciyarsa ke ciki amma yakasa saida jiri ya zaunar dashi kan kujera da qarfi ya rintse ido ga mamakinsa saiyaji kamar hawaye na neman zubo masa yayi saurin dafe kansa da hannu bibbiyu jin kamar zai rabe masa sbd yasan bazai ta6a iya cireta aransa ba.

Ahankali ta qaraso bayansa ta tsaya tareda zuba masa ido tana sake danne hawayenta..

Bude idanuwa yayi ahankali sbd he can feel her presence.

Juyowa yayi suka hada ido atake takasa riqe kukanta tafara girgiza kai tareda sakin kukan
Ya ware hannunsa 'daya alamar tahowa garesa da gudu ta qarasa ta fada jikinsa ya rungumeta sbd shikansa yana buqatarta kusa ayanxu.

Kukan datakene yafara bashi mamaki ya 'dago fuskarta ya kalleta atake yaji kwanyarsa ta qarasa hargitsewa ya bude baki zaiyi magana tayi saurin 'dora bakinta cikin nasa tana tsiyar hawaye.

Ahankali tasaki bakinsa tana kallon fuskarsa dake bayyane da damuwa cikin tsananin sanyin muryar kuka tace,

Ina sonka yarima maheer abdulshams,

TARAYYAWhere stories live. Discover now