36

15.4K 1.3K 133
                                    

Haske writers association

Not edited.
A gaggauce.
Mineelik nada kwarjini da wani irin haske na tsananin kyawu Wanda yasaka Sam babu mai ganinta daga mahaifinta sai mai kulada ita shiyasa bakowane yasantaba musamman daya zamto itace kujerar mulkin mineelik ayanda abin yake mahaifinta yariga yayi amfani da wani irin sihiri akan karagar da sunan mineelik yanda ko bayan mutuwarsa babu Wanda zai iya raba mineelik da karagarta kuma barinta a nahiyar na nufin mutuwar duk Wanda ke nahiyar kuma babu Wanda yasan da hakan sai ita mineelik din da mahaifinta sbd ganin bai haifi namiji ba yasa aka fara farautar karagar mulkin.

Mineelik na zama cikakkiyar budurwa qannan mahaifinta su hudu suka hada kai suka kashe mahaifinta mutuwar wulaqanci sbd wani irin zalamar son hayewa karagar saidai bayan kashesa suka kashe junansu agurin sbd kowa nason shine zai hau.
Lokacinda mahaifin mineelik zai mutu saida ya shafawa karagar jininsa dake zuba na suka hudu dasukai masa cikin tsananin azaba da taurin zuciya tareda fushi mai tsanani ya daf karagar yace,

Ni penya maqagin wannan karagar ayau jinina ya zuba sbd wannan dazata zamewa duk wani makusanci agareta masifa  ayau ina mata baki mai hadeda tsinuwa duk Wanda zai hauta tazamo ajali mai masifa agaresa matuqar ba MINEELIK-ASSULTANAH bace take kanta har ranar dazata na'da wani akai da kanta sbd jinina da aka zubar akanta daga wannan qarni nawa ta haramta ga dukkanin qarni masu zuwa.

Lokacinda mineelik ta fito bayan mutuwar mahaifinta aranar duk Wanda ke bousk yaganta sukaga zallar kyawun halittar dabasu taba ganiba saidai cikin rashin sa'a fitowarta tasaka rayuka da dama mutuwa dan kuwa wani irin haskene da maganadisu atareda ita dake jan mutane zuwa gareta Wanda wannan abin shine atareda karagar mai janyo mutane da rufewar zuci da ido akan hawanta.

Ranarda mineelik tahau karagarta amatsayin assultana aranar akayi wani irin tashin daya faru aranar shine koda gari ya waye duk Wanda ke nahiyar babusa.
Tashin hankali data shiga shine tabarwa datayi alamun mulkintane bazaiyi kyawuba sbd karagar tayiwa jininta qarfi kasancewarta mace.

Ita kadai tayi rayuwa mai tsayi,shekaru masu tsayi batareda kowaba,
Kadaici,qunci,baqin ciki da kewa sune abokanan rayuwarta sai karagar wadda ahankali take zuqe mata tausayinta sbd babu wani Wanda za'a yankewa hukunci a zubarda jininsa shiyasa abin yake cinta itakadai makari 'dayane mahaifinta yasanarda ita na wannan karaga shine soyayya mafi qarfi amma idan idan sadaukarwar abu mafi soyuwa tashigo.
Sanin kaf acikin duniyarta babu Wanda zai iya ko 'dago kai yakalleta sbd kwarjininta bare ya iya samun soyayyarta saidai ta tabbatarda wannan azarbabin da  gaggawar tareda rashin tsoro da kwadayin sai bil adama.
Wannan shine burin
Hakan yasa ta rufe daularta babu  wanda yake ganinta sai ita tafara fitowa duniyar bil adama domin kuwa babu abinda take buqata da tsananin buri kamar soyayyar da babu irinta a qarnin.

Aduk shekara da kalar suffan datake fitowa saidai bata taba dacewaba amma alqawarine bazata daina neman soyayyaba harsai ta mutu. 

     Shiru sukayi dukkansu kowanne najin zuciyarsa a bushe babu wani tsoro ko fargaba sbd dama nema suka fita duniya dan haka su sunga zinari kuma bazasu danganaba harsaisun mallaki wannan karaga Ajani ne ya gyara zama yayi gyaran murya yace,

"Toh shi zinarin yana tare da ita kenan?

        Gyara zama aqoob yayi cikin muryan da ta manyanta da tabbarda abinda zai fada yace,

"Ita da kanta itace zinarin sbd itace kujerar mulkinta,sunanta sunan karagarta daularta itace arziki da kowa ke fatar samu saidai hadarin dayayi Katanga wa arzikin shine soyayyarta wadda itakaice mukulli ga wannan taskar arzikin.

              Kallon kallo suka shiga yiwa junansu saidai babu Wanda alamar tsoro ko fargaba yake ataredashi Jamal ya kalli cikin idon aqoob yace,

TARAYYAWhere stories live. Discover now