Haske writers association💡
Bayan fitarta rumanah taja abun lullubewarta tana murmushi tace,
Nuratu kinfa karyawa mamani gwiwa daga kawai tana mana fatar samun jin dadi da 'yanci idan kika zama sarauniya....
Kallonta nuratu tayi cikin tsananin sanyin jiki tace,
Rumanah ke kinamin fatar nazama baiwarda za'a riqa kwana da ita tana haihuwa Ana karbe yayan idan nazama haka me naqaru dashi arayuwata bayandai ta tabbata naza baiwa tahar mutuwa...
Qarasowa da sauri rumanah tayi ta rungumeta ganin hawaye na zubo mata tace,
Nuratu bana miki fatar wannan rayuwar ko amafarki bare afili,
Keda mamani kune 'yan uwana kullum fatana da adduana musamu kubuta atare mukoma ga asalinmu domin kuwa saimun koma asalinmu zangano nawa asalin.Cikin sanyin murya nuratu tace,
Rumanah bawa baida ra'ayin kansa ko abinda yakeso sai Wanda uwayen gidansa suka yanke akansa,
Shin kina tunanin qaddara zata iya zuwa kaina aza6eni cikin masu zuwa shimfidar yarima?Girgiza mata kai rumanah tayi cikin son qarfafata tace,
Insha Allah bazamu ta6a wannan rayuwarba nuratu.
Rumanah ammy bazata ta6a bari kiyi wannan rayuwarba saidai ni banada tabbaci saidai Allah ya dubi rashin gatana.
Jiki sanyaye zuciya fal da tunani da zullumi suka kwanta har mamani tadawo cikin dare ta kwanta babu Wanda yayi bacci acikinsu sbd tunani.
Washe gari fuska 'daure mamani ta tashi babu Wanda ta amsa gaisuwarsa acikinsu qarshema kan rumanah taso sauke haushinta Dan har marinta tayi daga gaisuwa.
Cikin sanyin jiki ta share hawayenta tareda girgizawa nuratu data bude baki zataiwa mamani magana kai tareda sakin murmushin dole mai ciwo kafin ta kammala shirinta ta fice tana cewa,
Natafi'"""cikin sanyin murya.
Kodata isa sashen part ammy cikin sanyin jiki tafara aikinta har qarfe goma tabuga lokacin ammy ta tashi
Kanta qasa tagaida kafin tahau gyaran dakin cikin rashin walwala da rashin kuzari sbd duk lokacinda mamani tayi mata Abu abin na taba zuciyarta ganin batada wasu 'yan uwa kamarsu tunda sukadaine nata.Ammy sosai ta lurada rashin walwalarta ta danne tata damuwar cikin kulawa takira sunanta.
Amsawa tayi tareda barin gyaran gadon datakeyi tazo gabanta ta durqusa kanta na qasa.
Qare mata kallo tayi taga yanda jikinta ke 'Dan rawa tace,
Rumanah meya faru dake?
Mayarda hawayenta tayi cikin qarfafa muryarta tace,
Bakomai ammy.
Sam batason takurawa rumanah shiyasa ta kyaleta kawai.
Tundaga lokacin sabuwar tsangwana da muguwar tsana tashiga tsakaninta da mamani sbd gani takeyi itace take zugewa nuratu kunne akan tadaina wanka da tsafta sbd kar azabeta.
Duk yanda take daurewa kasawa takeyi saita kwana tana kuka sbd wani irin zagi da gori data sakota gaba dashi akan iyayenta dasuka rasu.
Tun tana boyewa tuni damuwa tabayyana ajikinta sbd ramar datayi.
Sultana duk datana cikin damuwar dawowar maheer dakuma hukuncin sultan Saida damuwar ganin halinda rumanah take ciki tadameta musamman ganin tana ramewa ta daina walwala kwata kwata ta mayarda kanta cikin bayi 'yan uwanta duk wani aikin wahala tanayi Wanda yaqara hargitsata.
Duk yanda sultana tayi da ita tafada meke damunta ta nuna mata ba komai sbd idan tafada tasan azabardasu mamani zasusha zai iya sanadin rayuwarsu kuma bazai tsaya akantaba harda nuratu.
Jakadiya itace ta bincikowa sultana tsaf abinda ke faruwa da rumanah sosai ranta ya 6aci hartayiwa sultan Aiken abinda ke faruwa da rayuwar 'yar amintaccen bawansa daya rasu saikuma ta dakatar sbd tasan hukuncinsa bazaiyi dadiba Dan rayuwarsuce ke lilo a sama kuma barinsu duniya tamkar barin asalin rumanah ne sbd mamani kadaice tasani.
*
Qarfe biyar na yamma jirginsu ya sauka a qasar
Kasancewar ansan bayason rawar jiki da yawa yasa motoci uku kawai sukazo daukarsa da iyalinsa sai khaleefa dasuka zo tare bayan yazo gurinsu daga zuwa weekend yabiyosu suka dawo tare.Tunda yafito ake zubewa ana gaishesa so daya kawai yadaga kai alamar amsawa hannunsa daya na aljihun wandonsa sai shades dinsa daya gyara.
Suhailat na gefensa ta saci kallonsa zuciyarta na nauyi sbd ganin tsantsar kyawu da kwarjininsa taji kishinsa na taso mata tayi saurin dauke kai tana gyara riqon handbag dinta.
Itada shine a mota 'daya 'dayar motar khaleefa dasu amah sai 'dayar ta guards.
Koda suka isa masarautar tuni duk wani guard da manyan masarautar suka fito tarbonsa.
Cikin girmamawa ake zubewa ana gaidasa harya isa gaban mahaifinsa a hankali yasaki murmushin da iyakacinsa fuskarsata ya gaidasa sultana cikeda girmamawa da kewarsa.
Lokacinda isawarsu maheer ta isowa sultana sakin murmushi tayi cikin tsananin farin ciki kafin tayiwa wanda ya isoda saqon babbar kyautar yana ficewa suhailat dasu amma suka shigo part 'din jakadiya na gaba.
Cikeda girmamawa suhailat taqaraso gaban sultana ta durqusa duk da cikinta daya fara girma ta gaidata.
Cikeda kulawa sultana ta amsa tana kallonsu amah dasuka zauna jikin mahaifiyarsu sbd rashin sabo dasu.
Tana kallon yaran tace,
Jakadiya aje asake dubowa part dinsu idan gyaran ya kammala sbd yaran sun gaji suna buqatar hutawa.
Washe baki Jakadiya tayi cikin girmamawa tace,
Allah yataimaki sarauniyar sarki kuma kakar sark ai tun asubar fari baiwa rumanah ta kammala duk wani gyara da'akasata a part 'din daga part 'din na yarima har part din gimbiya suhailat kuma kuyangi biyar nacan najiransu domin hidimarta data yara kuma anyi musu gargadin ko kallon part din yarima karsuyi bare tunanin shiga koda dasunan wanine ya aikesu.
Murmushi sultana tasaki tareda kallon suhailat tace,
Suhailat kuje kuhuta da yaran sun gaji sosai.
Miqewa tayi daidai fitowar rumanah daga bedroom din ammyn fuskokinsu suka sauka akan na juna daidai kuma shigowar yarima a palon na qurya Wanda qamshinsa yasasu juyawa qofar atare.
Saurin durqusawa rumanah tayi tareda sunkuyar dakanta ta gaidasu atare batareda ta bambamtaba.
Suhailat ce kawai ta amsa cikin wani mugun sanyin jiki daya saukar mata lokaci 'daya.
Ammynsa ya nufa da wani irin murmushi da duk duniya itakadai yakewashi
Cikeda farin ciki da murmushin daya kasa 6oye farin cikinta ta miqe tsaye yana zuwa ya rungumeta.Cikin rawar jiki rumanah ta fice sbd wani kallo da Jakadiya ta watso mata.
Itama jakadiyar ficewa tayi hakama suhailat sbd tasan qaidane idan zai gana da mahaifiyarsa kowa ficewa yakeyi sbd itakadaice takejin doguwar maganarsa bayan ita ko suhailat datake matarsa baya doguwar magana da ita,su bayi ma ko masu hidimarsa tun tashinsa bayajin yata6a yiwa bawa magana.
Bayan fitarsu Jakadiya takalli rumanah data nufi qofar fita babban palon farko tana qoqarin barin part din gabadaya takira sunanta.
Dawowa tayi tana sunkuyar dakai sbd ko iya dagowa takalli suhailat bata iyayi sbd faduwar gaban datake ji.
Ki kama yaran ki rakasu part dinsu ta huta akula da yaran kar abari su dameta sbd yanayinta.
Jinjina kai tayi cikeda ladabi ta miqe ta 'dauki fammah tareda riqe hannun amah kuma ta 'dauki handbag din suhailat din tabi bayanta.
#Mamuhgee