38

14.9K 1.3K 207
                                    

Haske writers association.

A gaggauce
Not edited.
Zaune suke dukkaninsu gaban boka aqoob dayayi shiru cikin jinjina mataki na qarshe dazai fada musu sbd aljanun dayake aiki dasu sune suke fada masa komai gameda sarauniya mineelik sbd suna cikin maqiyan farko na sarki penya.

Kallonsu yayi 'daya bayan daya
Dukkaninsu kowanne ashirye yakeda karbar matakin qarshe 'din sbd yanxu sunkai iya maqurar ganin cikar burin sbd Jamal dasukaga yafara shiga hanyarda bazata bulleuba su duka.

Wasu irin qananan wuqaqe farare tas guda shida masu kamar azurfa ya fitar daga wani irin rami ya ajiye agabansu tareda kallonsu yace,

Wannan wuqar dafin jinin penya ce wadda duk duniya ita kadaice zata kashe sarauniya mineelik,
Kowannenku zai soketa da wannan wuqal agurare daban daban saidai kuma dafin zai illatatane bazai kashetaba matuqar ba masoyintane ya soketa da ita kuma ya zamto shine zaiyi mata suka ta qarshe da wannan wuqar to tabbas wannan ne kawai zai kasheta...idan Wanda takeso fiyeda komai bai soketaba to tabbas kusani sukarku zata illatane amma bazat mutuba Wanda kunsan rashin mutuwarta na nufin rayuwarmu mu duka dan haka wannan matakin na qarshe yafi kowanne hadari.

Cikin zalama da qosawa kojo yace,

Jamal bazai taba qi hakan ba koya gardama zamuyi amfani da qarfinmu mu sakasa.

To bayan wannan kuma idan ta mutu to masautarta zata bace daga duniya babu Wanda zai sake ganinta saidai idan Wanda take tsananin so ya sadu da ita to tabbas idan ta mutu masarautarta tariga ta bayyana har abada tazama ta bil adama ta tashi daga duniyarsu.

'Daure fuska amari yayi zaiyi magana da sauri kojo ya dakatar dashi yana cewa,

Munriga munkawo yanzu babu abinda zai gagara yamaida mu baya ga wannan tafiyar Jamal dole zai sadu da sarauniya mineelik.

Wasu sabbin madaurin damtse na wani tsarin boka yabasu kowannensu ya daura tareda 'daukar wuqa 'daya na Jamal kuwa cikin fata amari ya nade masa ya soka qugunsa suka miqe.

Yonas dake qoqarin soka tasa cikin takalmin fatar damisarsa yaji hannunsa na wani irin qaiqayi yayi saurin dubawa zai sosa saiyaga rubutu na bayyan a hannun nasa yayi saurin kallon mahaifinsa yaga idanuwansa rufe alamar saqone yake ruboto masa dan sanar dashi wani abin.

Da sauri ya maida kallonsa ga tafin hannunsa yafara karanta saqon.

"" idan buri ya kammala kawai da datti ake ashare komai da komai""""

Jinjina kai yayi cikin rashin tausayi yakalli bayansu kojo dasuka gabansa dan yafahimci saqon meyake nufi yana nufin idan ankammala su kashesu nan take.

Suna fitowa qofar gidan boka aqoob sukaga wani irin gini mai matuqar tsawo da kyawu tareda girman dabasu taba ganiba mutanen gari sai fitowa kallo akeyi ana nufar hanyar da ake hango masarautar
Atake cikin gaggawa suka hau raqumansu suka nufi hanya sai tun daga nesa suke hango babu daji sai masarautar kawai da girmanta yasa ta zamto kamar tana cikin ganin ne.

Suna isa bakin qatuwar qofa mai girman gaske suka taru su biyar suka tura qofar tabude suka shige cikin wani irin mamaki mai rikita tunani da nustuwa sbd girma da kyawun masarautar babu kowa koina tsit saidai komai fes tamkar yaune aka ginata.

Harabar gurin suketa rarraba idanu suna kallo cikeda far in ciki mara misaltuwa sbd burinsu yacika saura qiris su mallaki sauran duniyar.

Wasu furanni masu qamshi yonas ya tsinka ya shinshina ya lumshe ido cikin farin ciki ya daka wani tsalle tareda sakin ihun farin ciki.

Kojo kuwa mahaukaciyar qofar daya tabbatar ta fadar da karagar ke cikine ya nufa ya saka hannu biyu yatura qofar ta wangale atake dukkaninsu sukai mutuwar tsaye ganin karagar dake wani irin daukar ido duk da kasancewarta kalar baqa mai adon zan zinari.
Girman fadar suka kallon cikin wani irin farin ciki madaukaki da sauri suka nufi kujerar kusan atare kowanne na burin kaiwa ya hau Jamal yasha gabansu cikin wani irin yanayi na damuwa da bacin rai.

TARAYYAWhere stories live. Discover now