Haske writers association💡
Not edited.
Miqewa tayi tabar dining area din ta nufi dakinta tana dafe 'dan qaramin cikinta dataji yana murdawa.
bayanta yabi da kallo yanajin jikinsa na qara saki sbd wata irin kewarta dake cinsa.Zame suhailat yayi daga jikinsa ya nufi stairs ya haye dakinsa.
Yana shiga ko zama baiyiba yashiga wanka yafito yashirya ya kwanta tareda rufe idanuwansa sbd jin yanda zuciyarsa ke wani iri.
Koda suhailat ta shigo tagansa tayi tunanin yayi bacci tayi kissing lips dinsa ahankali kafin tafice takoma dakinta.
Kwance take iduwanta arufe saidai Sam bacci yakasa daukarta data rufe idanuwanta shi take gani lokacinda ya rungume suhailat
Takasa yakice abin aranta
Ta jinjinawa suhailat ranar data gansu a asibiti amma bata nuna jin zafintaba bayan tasan saita fita jin zafinma.Duk yanda taso dannewa ta yakice kasawa tayi saidata saki wani irin siririn kuka tana tura kanta cikin pillow taji 'dan sauqi aranta.
Qanqame pillow dinta tayi.
Taji kewarsa na sake shigarsa saidai tasan yanacan da matarsa
Wasu siriran hawaye suka sake gangaro mata ta rufe ido tana sakejin nauyin da zuciyarta ke mata.Acikin su uku suhailat ce kawai tasamu yin bacci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
Washe gari bai fita aiki da wuriba dan kawai yasan time dinda take fitowa daki
Koda yayi wanka ya shirya cikin kayan shan iska na zaman gida palon qasan yazo ya zauna yana karanta news paper yana shan black tea.Koda suhailat taga bazai fita aiki yau Ba itama fasa zuwa tayi sbd ganin bazata iya ficewa tabarsa ba sbd gaba daya kwanakin basu sakeba sbd baida time kullum sai dare yake dawowa.
Doguwar rigace mai shape sosai da budadden wuya ajikinta orange sai tayi mata kyau sosai ta qaraso inda yake zaune ta zauna kan jikinsa tana kallon fuskarsa daya 'dago idanuwansa ya zuba mata.
Murmushi tasaki tareda shafo fuskarsa tana cewa,
Na canzane?
Maida kallonsa ga karatun dayakeyi yayi yana cewa,
You're getting late for office.
Sake shafo fuskarsa tayi tana murmushi tareda matso da fuskarta ga tasa sosai tayi kissing lips dinsa tace,
I'm missing my husband so zan zauna tareda shi a gida yau""taqarasa fada tana hade bakinsu.
Kallonta yayi itama shi take kallo tana kissing 'dinsa
Sanin tunda yadawo babu abinda yashiga tsakaninsu yasa ya sake shigar da ita jikinsa yana cigaba da kissing 'dinta yana shafo wuyanta zuwa qirjinta.Jin shiru ya tabbatar mata da duk sun fice ta tashi kanta ko dankwali babu dan dama tayi wankanta,sanye takeda palazzo trouser brown da cowl neck top mara nauyi ko kadan ta fito palon tana tunanin yanda zata samu damar waya da ammy itadai gida takeso sbd zuciyarta zata iya tarwatsewa anan.
Bata lura dasuba saida takusa isa daf dasu idanuwanta suka sauka kansu
Gabanta yayi wata irin mummunan faduwa jiri ya 'dibeta saura kadan ta fadi yasaki suhailat dake jikinsa cikin zafin nama ya tareta ta fado jikinsa
Atake ya lumshe ido tareda sakin wani muguwar 6oyayyar ajiyar zuciya.Kallonsa suhailat tayi idanuwanta nacikowa da hawaye kafin takalli rumanah din wadda tuni nata hawayen suka 6alle mata ta zame jikinta ta juya dakinta tana 'danne kukan dake taso mata
Wlh batason nan tafison gurin ammy,
Nan zuciyarta bugawa zatayi gwara ta tafiyarta inda bazata riqa ganinsa da matarsaba.
