0️⃣1️⃣

6.4K 316 3
                                    

AMANA WRITERS ASSOCIATION 👨‍👨‍👧‍👦

ABINDA KA SHUKA🌾

"Maryam! Maryam!"

Juyowa nayi Ina kallonta,Kallona takeyi itama tareda fadin Maryam yakamata ki natsu kicire damuwa aranki,kinga burinki bewuce kisamu aikinnan bah,so tunda har sunkiraki interview kidaure kitattaro natsuwa kidawo da ita jikinki

To shine abinda nafada tareda fitowa daga cikin motar
Kallon building dinda ke gabana nayi,se naji duk jikina yai sanyi,

Juyowa nai na kalleta tareda fadin "Anya mints xasu daukeni kuwa kalle Kayan jikina fa,kuma ki kalli yanda yanmata masu ji da kansu suke shiga gurinnan.....

Kidaure kije Allah xebaki saa "shine abinda mints tafadi tareda shiga motarta tatafi

Tafiya tafarayi a hankali har tashiga
Tsayawa tai Tana kallon haduwar gurin,lallai kudi na inda suke,komawa tai kamar bakyauya tana tafiya tana kalle kalle,bata ankarabah taji tabuge wata mata,juyowa tai tace dan Allah baiwar Allah kiyi hakuri,budurwar tai murmurshi tareda cewa karki damu bakomi...

Kema interview kikaxo?ey budurwar tafadi tareda kallon maryam

Maryam ta kalleta ,budurwar tayi kyau,tayi shigarta me kyau,aranta tace indai wainnan suna gurin ae bayanda xaae musamu

Sukafara tafiya suka tunkari receptionists din
Gaisheta sukai tareda cewa tai directing dinsu xuwa office dinda ake interview

Kwatance tamusu sukatafi,suna xua sukaga mutane dayawa na bin layi kowa yayi gayu daidai gwargwado,kallon kanta tai taredajin wata kunya ta lullubeta

Guri suka samu suka xauna akafara kiran sunaye,kowa yafito setaga yafito da murmushi a fuskarsa,har akaxo kanta

Mikewa tai tashiga office din taredayin sallama

Wani kamshine tareda sanyi me dadi ya riski hancinta,wata hadaddiyar mace tagani wacce vacatawuce shekara 23 a duniya bah

Gaisheta maryam tai tareda fadin nadauka ance namiji ne me company dinnan
Matar tai murmushi tace ey miji na ne ,bayanan yatafi wani business trip 😊ko bakiso mace tamaki interview ne?Aa ae duk dayane tafadi tareda maidamata murmushi itama

Sooooo ya sunanki?
Sunana maryam usman

Sunanki nada dadi,Thank you maaa
Sooo 0 levels dinki sunyi kyau me yasa bakicigaba da karatu bah?kallon kasa maryam tai tayi shiru,tambayar tasake maimaitamata,dagowa tai ta kalleta sanann tace family issues ne bansamu damar xuwa jami'a bah

Matar tai murmushi shikenan malama maryam ynxu keda bakida crtificate na degree ma wani aiki kikeso mubaki?maryam tace anty ko secretary haka kuma Na iya yin snacks sosae koyaushe kuka bukata xan iya muku

Murmushi tai sega abokin aikinta yashigo kallonta yai tareda fadin Aisha ke kadai akejira gurin meeting,tace ohh namanta kaga har time yatafi...pls kataimakamin ka karasamasu interview din,okay ina xuwa fita yai itama tatashi tanafadin se anjima maryam

Zama maryam tai a kujerar da ke gabanta tana duba nokia din hannunta,sallama yai tareda shigowa,his voice sounds familiar shine abnda tafadi cikin ranta

Zama yai tareda juya da kujerar gareta

Kirjintane ya buga
Innalillahi wainna ilaihirrajun
Shine abinda taketa maimaitawa

Kallonta yake shima cikin mamakin ganinta


Arabiya 😉

ABINDA KA SHUKA(COMPLETED)Where stories live. Discover now