4️⃣7️⃣:M & A

1.4K 139 9
                                    


And to those sharing this novel to their family and Friends nagode sosae,Allah yabar kauna,Allah yahada fuskokinmu Aljannah,waenda basa sharing suma Ina godia da karatu,Allah yasaka da Alkhairi,its a great honor😇

Se after 10 suka raka aryana gida,sannan mubarak yai sallama da muhsin yawuce,komawa cikin gida yai yaga bilaaal a parlor da baba,ya gaida baba yashiga ciki,wayarsa yadauka yakira maryam,sundade suna magana kafin suyi sallama,bayan 2 days baba tsoho yakira muhsin ya shaidamasa yaturo magabatansa,haka kuwa akayi,baba da brothernshi,da wani aminin baban ne suka tafi kasar,an karbesu hannu biyu biyu,sannan anbasu maryam,suka mika sadaki,akasa rana 1 month,washegari suka dawo suna basa labarin karamci irinna mutanen Cameroon......

Shirye shiryen bikin arryyy kawai su muhsin keyi,don shine aminin amarya kuma abokin ango,ta kowani bangare wujijjiga yakesha,yau suna nan gobe can,gajiya yai yahada mintss da aryyy,tuni kam kawancen nasu yafara nisa,don duk sunsaki jiki da juna,kasancewar aryyy bawasu kawaye gareta ba,haka mintss maryam ce kawai,kullum cikin video call suke da maryam,itakam harga Allah bataso tayi missing bikin aryana,ranar da suna waya da muhsin harda kukanta akan yakira mummy yaroketa abarta tadawo naija biki amma sam yace baxaae haka dashiba kam,baxe iya ba,shi dai sedai kullum yaita azalzalata shidai tadawo,yanason yaganta a kusa,ynxu kam sunsaba sosae da juna,soyayya suke mai cike da tsafta.......

Bilaal kam ba ynda beyiba,sa ranarnan da akama muhsin da maryam yatabashi sosae,son maryam yakeji ynxu dagaske,so yake yasameta a karo na biyu,amma besan ta Ina xefara ba,don yasan ko yaje Cameroon din besan ta Ina xefara nemanta ba,duk wata hanyar da xebi yasamu numberntama besamuba......

Shirye shiryen biki siketayi suma bangaren maryam,hakan yasa su mummy suka roki abari tadawo saboda shirye shiryen,ranar da tadawo kusan kwana sukai basui bacci ba anata fira,washegari tasamu mamana akan tanaso taje bikin aryyy,mamanaa tace baxeyuwu ba,sbda lkcin bikin itama bikinta saura sati biyu kuma baason amarya da yawo so tayi hakuri kawai,bayan auren ta taje taga gdan amarya,bayanda ta iya hakannnan ta hakura,a ranar kam sega mummy da Anty Aisha sunxo,shirye shiryen bikin suketayi,su siyama kam sunata lissafa shagulgulanda xaae,maryam ce ta kalleta tace sis nikam banson big wedding,a daura kawai ayi walima,se Allah yasama Albarka a ciki,kabbaran da siyama tayi shi yasa su mummy kallonsu,sannan tace sannu sheikhiya maryam,sannu kinji to wlhy baxeyuwu ba,inma fadi maki,biki daya dai,rana daya kawai,wlhy semun raqwashe,in bacekije ba inje a matsayinki,duka maryam ta kaimata tayi sauri ta kauce,mamana tace ae maryam kiyi shiru kawai amma event dole ne sedai kiyi hakuri.......

Duk ynda sukai haka tafadawa mintss,mintss tace lallai bakida hnkali,da kina nufin haka xamuyi buki,ae baki isaba dan ubanki,yooo ubanwa yabaki wannan shawara kuma asanina dai muhsin ba ustaz bane,to akan me kikeson cutarmu?ko rawa a kwancenne bakiso muyi?aekam dole mu cashe Tab,kyanshi ma muyi week ana cashewa,maryam ta kwashe da dariya tace lallai mint,to wlh ba a bikina ba,siyama tace ae anty mintss kin kawo shawara,a week ana cashewa kawai ,mintss tace siyama Allah maki Albarka kinjiii,gwara kiriqa daurata kan hanya,maganganunsu suka cigaba dayi akan event biyu xasuyi,se suka fara tunanin outfit dinda xasusa da wanda amarya xatasa,makeup artist da mai lalle,duk dai sunata lissafawa,maryam tace amma fa karyai yawa?mintss tace na tabbata kudi ba matsalan muhsin bane wlhy,so ki kyalemu kawai muqawata bikinmu abegggg.........

Shiru tayi takoma gefe,siyama ta amsa wayar sukacigaba da lissafa,muhsin keta kira a dole sukayi sallama ba don sungama ba,maryam ta amsa wayar,yace mintss tana shiga hakkina fa,maryam tayi murmushi tace yaakai kasan itace?yace nasan itakadaice xakidade kina magana da ita haka,tace wai fa shirye shiryen biki suketayi da siyama,nan ta basa labarin ynda sukai,yace ta mikama siyama wayar,mikamata tayi yace tafadi kudinda xe isa yai transfer,tace inshaaallah xatamasa text,tana mass text kuwa taji alert,tsalle tayi taje tafadawa mamana sannnn takira mintss tace yaturo mintss tace ba matsala sufara siyayyan abunda yakamata itama ana gama bikin aryana xatataho itada mama.....

Washegari muhsin abuja yatafi gurin kanwar mamansa,sukai lissafin abunuwanda yakamata yahada a lefe yabata kudin,tahada komi tataho dasu,tace nidai kawai don ba ynda xanyi dakai ne muhsin amma wlhy da ka hakura da yarinyarnan,yrnyar da tagudu ranar aurenku,katseta yai yace amma Anty da wa ta gudun tace kaninka bilal,yace kinga bilaal ne,inda wanine da na hakura da ita koda kuwa sonta xe kasheni amma bilaal ne,baxan iya hakura da itaba wlhy,son da nike mata ba kadan bane,kumana fatan Alkhairi kawai,tace dama ae ba ynda xamuyi,Allah sa Alkhairi,Allah baku xmn lafiya yace Ameeen,sallama yamata tarakashi har mota don a ranar xe juya,salllama yama mai gadinta sannan yafita yai parking waje,maryam yakira a waya,sunfi 30 mint suna magana,sannnn sukai sallmaa yakama hanya,shi kanshi yana mamakin irin sonda yakemata.......amma yaxeyi?so wani abu ne wanda zuciya bata shawara kafin tafada tarkonsa......

Ranar saturday ne daurin auren mintss,dama ita tace ba abunda takeso,dinner ce kawai xasuyi da muhsin yahada masu,aryana tasha gyaran jiki tayi kyau da ita,se qyalli takeyi,tafito amarya sak,lalle akaetamasu da yake yau jumaa,mintss takira maryam vidcall,tana nunamata aryyy,maryam tace OMG,aryyyy in a wani gurine ae baxan ganekiba,irin wanga qyalli sekihana mubarak motsi,aryyyy ta kwashe da dariya tace ae sekin tabani ma kinji,kiji wani laushi,jiki yaxama na jarirai ,mintss tace sema kinmatso kusa,kiji wani shegen kamshi natashi,ae inda akasiyo kayan kamshinta Anan zamu saya naki,maryam tace inane hala?mintss tace kiduba page dinsu a instagram @scentparadise,maryam tace toh kinsan ni rabona da IG 6 years kenan,amma barinyi installing app din,Allah sa na iya tuna komi nawa,mintss tace Ameen,sallama sukai ta kashe wayar.......

Washegari aka daura aure misalin karfe 2,amarya tasha kwalliyanta,don professional makeup artists tadauko wato @arabsglam,akamata makeup itada frnds dinta kuma cikin sauki,da iyayenta,sannan da yamma sukasha walima,se after magrib akaxo kai amarya inda baba yace se anfara kaita gurin baban muhsin yamata nasiha sannan,haka ko akayi aka kaita yamata nasiha,akakawota babanta yace shikam beda abun cewa Allah mata Albarka,aryyy kam in Banda kuka ba abunda take,dakyr aka banbareta jikin su mama Hauwa,muhsin yadaukesu itada mintss da wasu tsofaffi biyu,shikam kamar yai kuka,kukan aryana yasa duk jikinshi yai sanyi,haka yaita lallashinta a mota har suka karasa gidan.......

Ana kaita kuma akafara shirye shiryen dinner,kaya ta canxa akafara tsantsara mata kwalliya,tasa gown dinta royal blue wanda ya Amshi farin fatarta,ita kanta kallon mirror take tana kara godewa Allah,aryy ma sunsha ankonsu peach,anmasu makeup suma,pictures sukai snapping taturama maryam......

Motoci ne sukaxo akatafi da frnds din amarya muhsin kuma yadauki amarya da angonta,hugging aryana mubarak yayi,muhsin yai tsaki yace wlhy xan saukeku a titinnan na rantse,sekace xata gudu,kabari kukoma gida mana,mubarak yace kadai baxakaganeba wlh,yaba kwalliyannanta da kyawunta yaketayi har suka karasa hall din,inda abakin hall din akai zane da M & A........

Keep voting
Keep sharing it to your family and friends
Love you all❤️
    

                Your's arabiya🦋

ABINDA KA SHUKA(COMPLETED)Where stories live. Discover now