3️⃣0️⃣

1.4K 122 8
                                    


Zan karasa sabida wasu dalilai,amma kusani comments dinku suke karfafa min gwiwa,nagode sosae❤️Ina kaunarku gabadayanku🌸


Oga nagani saman kaina yana wani huci kamar zaki,yace tashi,tashi maxa kinmanta rules and regulation dinako,ke mahaukaciyar inace,kallonsa nikeyi da maaikatan da sukayi layi kusa dashi na kalla time naga 7am but how comes,se 8 yake zuwa nasan dole fadamasa akayi,yace tashi mana,nayi sauri natashi yace uban meyasa kike kwanan min a restaurant?nace pls kayi hakuri banida inda xan xaunane,yace wanann matsalarkice,kudina ya watsomin yace ki tattara kibarmin gurinnan ynxunnan,tsugunnawa nai nace dan darajar manxan Allah oga karufamin asiri,banda kowa wlhy,banda gurin zama,aikinnan shine rufin asiri na,kuma wlhy ciki gareni karufamin asiri....

Shiru yayi yashiga ciki,segashi yafito da wani kudi ya mikamin yace gashi wannan xe isheki har month dinnan yakare,amma gskia baxan iya barinki anan ba,kije kinemi wani aikin,gskia baxan iya ba dukda inajin dadin aiki dake amma nasan Allah xehadani da wasu sooo kitafi kawae,kuka nafara natashi natafi nahada kayana dake gurin,na masu sallama nafita se ga ummi tabiyoni tana kirana,tsayawa nayi tace dan Allah kiyi hakuri bansan korarki xeyiba,shiru nayi natsaya kallanta nace meyasa xakimin haka,na yarda dake,nafadamaki komi a kaina kinci amanata,korata xeyi sbda budget shyasa nafadamasa halinda kike ciki sbda ya kyaleni,murmushi nayi nace kefa ko yakoreki,kina tareda iyayenki da mijinki,nifa banda kowa lallai mutanen duniya bakuda amana......

Tafiya nayi na batta a gurin,natafi masallacinda na kwana rannan,na siya abinci naci,na zauna tacan baya,bansan yaakai liman yaganni ba,kawae ganinshi nayi a gabana,yai min sallama yace baiwar Allah iyayenkifa nace sun rasu,yace bakida yan uwane,nace kawuna yace baxerikeniba,yace taso muje gidana,wani sanyinaji a raina na mike nabishi,muna shiga gidan ya barni a wje yashiga yama matarsa bayani,mukashiga tare faran faran ta karbeni tana tausayamin,takawomin tuwo naci sosae kam,sannan ta kaimin ruwan wanka tace naje nayi,takaini dakin yaranta yanmata guda biyu,haka nacigaba da zama a gidan har suka sani islamiya nima,kullum muke zuwa muke dawowa da yaran,kwanakinnan Ina yawan yin amai,amma basutaba luraba,ranan muna zaune sega kawar ta taxo muka gaisheta tanata kallona,mukashiga dakinmu,tace kawata wannan budurwarfa diyar waye?tace wlh malam ya tsinceta,infadamaki batada kowa,marainiya shine fa muka kawotanan,nike riketa,tace lallai amma bakida hnkali wanan santaleliyar budurwa kawae ta kwace maki miji,ke kina kallon idon yrinyarnan ai kinsan yar barikice,gaskiya kinaso ki tafka babban kuskure,dariya tayi tace ke nayarda da mijina sannan na yarda da nutsuwar yarinyarnan ba abunda xefaru se Alkhairi inshaaallah......

Tashi tayi tashiga kitchen tafara soya mai,ji nayi zuciyata na tashi ga kamshin man,cikina ya murda da gudu nashiga toilet nafara amai,hnkali amina yatashi tafita da gudu ta kira maman,segasu da kawar taimakamin sukai,natashi kawar tace ke kalleni,nako kalleta tace kawatah diyarnan takifa cikine da ita,ko dama tataba aure,gabanane yafadi,mamansu amina tace wani irin ciki kuma ana zaune lafiya?ko kintaba aurene maryam nayi sauri na girgiza kai tace batada komifa,kallonta tayi tace naga alama kina wasa amma Allah ya taimaka,tadauki jakarta tatafi,jikin maman aminane yai sanyi tace maryam fadamin gskia ciki gareki?dagakai maryam tayi aiko tasa salati tace amina tashi maxa kiramin babnku,amina tace to tatafi,se gasu sunshigo tare yace yanaganku haka,wani abunne yafaru,tace maryam cikine da ita malam,nikam wlhy kanemo yan uwanta,baxaka daukomana tawhin hnkaliba,yai ahiru yana kallon maryam yace dagaske?maryam tafara hawaye tace ey,yace wayamaki?tayi shiru se kuka,yace kinga yaya mata gareni bansan boyayyar halayyarkiba,baxanso ki batamin su ba,kar kibatamin tarbiyyarsu,muje gurin kawunki inbashi hakuri kikoma gurinsa,tace Aaaah Aaah yace shknan kiyi hakuri kibar gidannan wlhy banson matsala.....

Daki nakoma nahada kayana nabar gidan,Ina kuka su amina na kuka,maman amina taban kudi tace nariqe a hannuna na musu godiya da karamcinda sukamin nafito gidan,nafara tafiya Ina tunanin inda rayuwa xata kara kaini.....

#vote
#comment
#share
    

                Your's arabiya🦋

ABINDA KA SHUKA(COMPLETED)Where stories live. Discover now